OneZamfara

OneZamfara

Share

Photos from OneZamfara's post 03/07/2024

03 July 2024


YOUTH ALLIANCE MOVEMENT💪🏻

Yau Cikin Ikon Allah (SWA) Da Yardarsa Da Amincewarsa Wannan Kungiya Mai Suna Asama Ta Samu Nasarar Kaddamar Da Ayukkanta Na Alheri Zuwa Ga Mabukata Domin Ragewa Al’umma Halin Da Ake Ciki Na Kuncin Rayuwa Da Talauci Da Yunwa Da Sauran Abubuwan Da Rayuwa Ke Bukata Karkashin Jagorancin Shugabanta Malan Junaidu Muhammad Majidadi.

Inda Wannan Kungiya Mai Tarin Al’barka Ta Rabawa ‘Yan Gudun Hijira Abinci Da Kuddi Kyauta A Unguwar Saminaka Dake Nan Cikin Garin Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara, Wannan Shine Program Dinmu Na Farko Program Dinmu Na Biyu Zamuje Gidan Yari Domin Biyawa Mutanen Da Aka Kargame Domin Bashi Ko Tara, Gwargwadon Halinmu In sha Allah.

Daga Karshe K**ar Yanda Kuka Sani Cewa Wannan Kungiya Ba Kungiya Bace Ta Siyasa Kota Wani Mutun Wanda Shine Yake Dauke Da Ita Domin Gudanar Da Ayukkanta, Wannan Kungiya Bude Take Ga Duk Wanda Yake Da Niyyar Taimakawa Mabukata K**a Da Marayu, Marassa Lafiya, ‘Yan Gudun Hijira, Musakai, Al’majirai, Makabartu, ‘Yan Gidan Yari, Da Sauran Mabukata Daya Shigo Ciki Muhada Hannu Da Karfe Domin Taimakawa Bayin Allah.

Muna Rokon Allah Ubangiji Daya Bamu Ikon Yin Wannan Akin Dominshi, Allah (SWA) Ya Bamu Zaman Lafiya Maidorewa A Jiharmu Ta Zamfara Dama Kasa Baki Daya Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.🤲

⁦✍️⁩
حسين كشب

Want your business to be the top-listed Computer & Electronics Service in Zamfara?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

ZAMFARA
Zamfara