TAJ Network
30/06/2026
Majalisar dattawan jam'iyyar APC wato Progressive Elders Council a jihar Adamawa, ƙarƙashin jagorancin Janar Muhammadu Buba Marwa (mai ritaya), ta gudanar da wani muhimmin taro a Fadar Gwamnatin Jihar Adamawa.
Taron ya mayar da hankali ne kan lalubo hanyoyin warware matsalolin da ke addabar jam'iyyar gabanin zaɓen shekarar 2027, tare da nazartar matakan kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamna domin tunkarar zaɓen.
30/06/2026
Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Amince da Ayyukan Manyan Hanyoyi Hudu a Yankuna Uku a jihar Adamawa
Ga jerin ayyukan da aka amince da su:
1. Za a kashe Naira biliyan 83 domin gina hanyar Ngurore – Jimeta – Mayo Belwa a Jihar Adamawa.
2. An ware Naira biliyan 58 domin ci gaba da aikin gyaran hanyar Yola – Hong – Mubi, mataki na biyu.
3. An amince da Naira biliyan 15.246 domin mataki na biyu na aikin hanyar Yola – Fufore – Gurin, wanda zai ƙunshi gina kilomita 20 bayan kammala kilomita 17 na mataki na farko.
4. Haka kuma, an amince da Naira biliyan 62.99 domin gina hanyar Toungo – Karamti, tare da gina manyan gadoji guda biyar da za su haɗa Jihohin Adamawa da Taraba.
25/06/2026
Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Yusuf Sulaiman Sak, Auwal Mohammed Magaji Girei
Gov. Fintiri ya sha alwashin kawo karshen 'yan luwadi a karamar hukumar Mubi.
Yana mai cewa idan s**a shiga hannu baza'a sake ganinsu ba
20/06/2026
Dan takarar APC ya lashe zaɓen cike gurbi a Jihar Kebbi
Dan takarar jam'iyyar APC, Rabiu Garba Aiki, ya yi nasara a zaɓen cike gurbi na mazabar Zuru ta Jiha a Jihar Kebbi, inda ya samu gagarumar nasara.
20/06/2026
🚨 Attention: Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta bayyana damuwa kan wasu bidiyoyi da ke yawo a kafafen sada zumunta dauke da kalaman da ka iya tayar da rikici tsakanin al’ummomin Bachama da Chobo a Karamar Hukumar Lamurde. Rundunar ta ce ta dauki matakan tsaro na musamman domin tabbatar da zaman lafiya, inda ta kara yawan jami’an tsaro a muhimman wurare tare da karfafa tattara bayanan sirri domin dakile duk wata barazana ga zaman lafiya da tsaro.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Kabiru Umar Hassan, ya umarci Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da ayyuka ya kara inganta tsaro a yankunan da abin ya shafa tare da hada kai da shugabannin al’umma, matasa da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya. Rundunar ta kuma bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, su guji yada jita-jita, sakonnin kiyayya ko duk wani bayani da ka iya haddasa tashin hankali, tare da gaggauta kai rahoton duk wani abin da ya shafi tsaro ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.
Sanarwa: SP Suleiman Yahaya Nguroje
A madadin kwamishinan yan sanda
Fintiri ya yabawa AB Kwacham da gudumowar da ya bashi
🚨🚨Video:
Karo na farko Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri cikin fara'a ya ambaci magajinsa a bainar jama'a 🫴🏻
'Yan Sandan Adamawa Sun Cafke Wanda Ake Zargi da Hannu a Garkuwa da Mutane a Hullere
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta samu gagarumar nasara a yaki da masu garkuwa da mutane, bayan da ta k**a wani mutum da ake zargi da hannu a sace mutane uku a yankin Hullere Gwalamba da ke Karamar Hukumar Yola ta Arewa.
Rundunar ta bayyana cewa an k**a wanda ake zargin, mai suna Alhaji Adamu Yahaya daga Hosere Jambutu a Karamar Hukumar Yola ta Arewa, bayan wani samame na musamman da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce an kai rahoton lamarin ga Sashen Binciken Sirri na Jiha (SID) a ranar 16 ga Yuni, 2026, inda wani mutum mai suna Samaila Musa ya sanar da cewa an yi garkuwa da wasu ’yan uwansa uku tun ranar 12 ga Yuni, kuma an kai su wani wurin da ba a sani ba.
Wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da Adamu Samaila Sultan mai shekaru 24, Bilal Abdurrahman mai shekaru 8, da kuma Ya’u Sani Baba Iyali mai shekaru 10.
Rahoton ya nuna cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalan wadanda aka sace tare da neman kudin fansa kafin su sake su.
Bayan samun rahoton, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamawa ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da amfani da kayan aikin sirri da fasahar zamani domin gano tare da kamo duk wadanda ke da hannu a wannan aika-aika.
Rundunar ta ce binciken ya kai ga cafke mutum guda da ake zargi, wanda a halin yanzu yake taimakawa jami’an bincike da muhimman bayanai da za su kai ga k**a sauran membobin kungiyar.
’Yan sandan sun tabbatar wa al’umma cewa za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Ana sa ran za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Yola