Arewa Web3 Labs
17/04/2026
A gaskiya wannan muhawara ta fara wuce iyaka.
Idan muka kalli yadda ake tafiyar da ita yanzu, ta koma hayaniya da kai-kawo maimakon anfanuwa ga al’umma. ya kamata ku tuna cewa mutane da yawa na kallonku a matsayin masu ilimi kuma shugabanni a wannan fanni namu na crypto musamman DEX.
Idan kun girma, ku nuna hakan a aikace ba sai komai ya zama abin gardama ba. Akwai bambancin ra’ayi, amma ba lallai bane ya zama hanyar rikici ko cin mutunci juna.
Mu daina mayar da hankali kan wanda ya yi daidai ko wanda ya yi kuskure, mu koma kan abin da zai amfani mutane: ilimi, gaskiya, da fahimta mai zurfi.
A irin wannan lokaci, mafi kyawun mataki shi ne a dakatar da wannan case cikin mutunci, abar hayaniyar haka.
Wani Malamina yace min✍️
Shiru da hikima sun fi hayaniya da gardama amfani.
Bissalam.
The_easiest_way_to_get_a_web3_jobs_20263_
13/02/2026
Shawarwari Goma Ga Ƙaramin Crypto Trader
1. Ka ririta capital ɗinka kamar jariri ko kwai✍️
Capital a trading tamkar jariri ne. Ana rainonsa a hankali a hankali da risk management, discipline, da haƙuri. Idan capital dinka ya ƙone, trading ɗinka dole ya tsaya. Don haka ka girmama shi kamar rayuwarka.
2. Ka guji overtrading da shiga kasuwa ba tsari✍️
Shiga trade ba tare da setup ba, ko bin motsin zuciya (FOMO), hanya ce mai saurin ƙona account. Ka san lokacin shiga trade, lokacin fita, da adadin risk din da zaka dauka kafin ka taɓa buy ko sell.
3. Ka san yadda za ka rarraba profit✍️
Idan ka samu riba:
Ka fitar da wani ɓangare (withdraw).
Ka ware na alheri da na bukatunka.
Ka bar mafi yawa a account domin ya girma. Wannan shi ne sirrin compounding a crypto.
4. Ka tsaya da ƙafarka kafin ka riƙa copying ko koyarwa✍️
Idan kai ba ka da consistency, kada ka ɗauki nauyin bada signal a groups ko koyar da mutane. Idan ka fadi, za ka ja mutane da yawa su fadi tare da kai. Ka fara gyara kanka tukuna.
5. Ka daidaita rayuwarka da yanayin kasuwa✍️
Idan kasuwa tana sideways ko drawdown, rayuwarka ma ta kasance a hankali. Kada ka gina rayuwa akan bull market kawai. Bear market shi ne lokacin gane trader na gaskiya.
6. Ka mayar da loss darasi, ba dalilin daina trading ba✍️
Loosing a crypto ba rashin basira ba ne (indai kana da ilimi a tafiyar). Yana nuna maka inda ka karya doka ne. Ka duba journal ɗinka, ka gyara kuskurenka, ka koma kasuwa da hankali.
7. Kada ka cinye profit gaba ɗaya✍️
Ka raba profit gida uku:
Reinvestment a account.
Personal use & helping others.
Reserve (stablecoins / cash). Lokacin da kasuwa ta yi muni, reserve ne ke kare ka daga liquidation da panic.
8. Ka guji gasa da whales✍️😂
Whales suna da capital masu nauyi. Idan ka shiga kasuwa kana so ka yi sauri kamar su, za ka ƙone yan dalolinka ne. Ka yi trading kamar ƙaramin yaro mai hankali, ba kamar babba marar tsoron loss ba.
9. Ka tafiyar da trading ɗinka da zamani✍️
Ka yi amfani da:
On-chain data
Market structure
Risk tools
Journal & review
Trader da bai sabunta iliminsa ba, kasuwa tana cin shi a hankali.
10. Ka gina kanka kafin ka shagaltu da hype da soyayya✍️
A farkon tafiyarka, ka rage:
Shiga hype coins
Bin influencers makafi
Damuwa da abin da wasu ke samu
Ka gina system, discipline, da patience. Idan ka tsaya da ƙafarka, kuɗi da nutsuwa za su zo da kansu.
✍️ Arewa Web3 Labs
Takuce
Code120226
With Sunusi Danjuma Ali – I'm on a streak! I've been a top fan for 9 months in a row. 🎉
Click here to claim your Sponsored Listing.