DNN Hausa
23/06/2026
Gwamnatocin Najeriya da Burtaniya sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa hadin gwiwa wajen yaki da daukar nauyin ta’addanci, laifukan intanet, yada bayanan karya da sauran barazanar tsaro da ke tasowa a duniya.
An bayyana hakan ne yayin taron tattaunawar hadin gwiwar tsaro da kariya tsakanin kasashen biyu karo na hudu da aka gudanar a Abuja.
Mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce hadin gwiwar ya fadada daga yaki da ta’addanci zuwa fannoni da s**a hada da tsaron intanet, tsaron teku, musayar bayanan sirri, magance rikice-rikice da tabbatar da zaman lafiya a yanki.
A nasa jawabin, mai bai wa gwamnatin Birtaniya shawara kan harkokin tsaro, Jonathan Powell, ya bayyana Najeriya a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwar Birtaniya a Afirka kuma ginshiki wajen tabbatar da tsaron yankin.
23/06/2026
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aika wa Majalisar Dattawa kudirin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya domin samar da tsarin kafa ‘yan sandan jihohi.
Kudirin na neman yin gyara ga wasu tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin shekarar 1999 domin samar da cikakken tsarin doka da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin ‘yan sanda nasu na kan su.
Matakin na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da aka dade ana yi kan bukatar bai wa jihohi karin iko wajen tafiyar da harkokin tsaro domin magance matsalolin ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka da s**a addabi sassan kasar nan.
Tun a watan Fabrairu, Shugaba Tinubu ya bukaci Majalisar Tarayya ta yi gyaran kundin tsarin mulki domin samar da damar kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai bayyana cewa hakan zai taimaka wajen inganta yaki da matsalolin tsaro a fadin kasar.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano