APM Youth and Women Alliance, Bauchi State Chapter

APM Youth and Women Alliance, Bauchi State Chapter

Share

18/05/2026

APM Nasara
APM sak
APM adalci
APM haɗin kai
APM ci gaba

Hon. Faruk Mustapha ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamnan jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar APM ya bayyana godiyarsa ga dukkan waɗanda s**a mara masa baya da goyon baya tun daga farkon burinsa na neman kujerar gwamna har zuwa ƙarshen tsarin zaɓen fidda gwani.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ɗan takarar ya ce duk da cewa matsayar maslaha da jam’iyyar ta cimma bai zo daidai da burinsa ba, ya amince da sakamakon cikin zuciya ɗaya tare da miƙa lamuransa ga ikon Allah Maɗaukakin Sarki.

Ya bayyana cewa a matsayinsu na Musulmi, sun yi imani da cewa duk abin da Allah Ya ƙaddara shi ne mafi alheri, kuma babu wani ɗan Adam da zai iya sauya hukuncinSa.

Ya ƙara da cewa siyasa bai kamata ta zama sanadin rarrabuwar kawuna tsakanin juna ba, yana mai jaddada cewa ci gaban jam’iyya da kuma bunƙasar jihar Bauchi su ne babban buri da ya kamata kowa ya sanya a gaba.

Haka kuma, ya yi kira ga dukkan magoya bayansa, abokan siyasa da masu masa fatan alheri da su mara wa dukkan waɗanda s**a samu tikitin jam’iyyar APM baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a dukkan matakai.

Ya ce wannan ba shi ne ƙarshen tafiyar siyasarsa ba, domin shugabanci na buƙatar haƙuri, sadaukarwa da jajircewa wajen hidimtawa al’umma.

17/05/2026

Manufarmu gina siyasa mai tsafta, ci gaba ga al'uma da kuma nasarar jam'iyar APM sak 2027

17/05/2026

Wannan hadi zayyi matukar bada ma'ana 👌🏻

16/05/2026

APM YOUTH AND WOMEN ALLIANCE: Taƙaitacciyar Manufa

“Haɗa matasa da mata domin gina siyasa mai tsafta, ci gaban al’umma, da nasarar jam’iyyar APM a jihar Bauchi.”

Want your organization to be the top-listed Government Service in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Bauch State Yan Doka Road
Bauchi