Umar F Abdul

Umar F Abdul

Share

04/10/2023

Zancen gaskiya idan ba tashi matasan Sokoto, Zamfara, katsina da Sauran su s**ayi s**a bada nasu gudumawar ba za'a dade ba'a shawo kan matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin su( Ba fata nake ba).

Eh, hakkin gwamnati ne tsaron lafiya dukiya, da kuma rayukan al'ummar da suke shugabanta, amma idan s**a kasa tsinana abin kiriki bai k**ata ace mu zuba ido a cigaba da k@she mu irin kisan da ko dabbobi basu chanchanta da ayi musu ba.

Bai k**ata ace sabida gwamnati ta gaza ku zuba ido a cigaba da bautar da iyaye, yayye da kannen mu ba.

Ni Dan jahar Borno ne mazaunin Maiduguri I'm talking from experience, Lokacin da matsalar bōko haram ya tsananta al'umma s**a cire tsammanin cewa gwamnatin wancan lokacin zata magance musu matsalar rashin tsaro ga Kuma irin cin kashi da su Yan Bōko haram din suke yi musu a wancan lokacin sai s**a tashi tsaye Dan nema wa kansu mafita.

A Maiduguri akwai Lokacin da ko sunan bōko haram mutum bazai iya ambata ba Koda a cikin gidan sa yake.

Anyi Lokacin da ake shiga gida karfe 4, 5, 6 na yamma Kuma baza a fito ba sai washe gari, ba maganar Sallar Magrib, ko Isha a masallaci.

Anyi Lokacin da normal ne ganin bìndiga a cikin gari..

Anyi Lokacin da Kuna zaune za'a zo a k@she dan uwan ku a tafi salin alin ba abinda zai faru.

Anyi Lokacin da rashin tsaro yasa aka rufe makarantu anan Maiduguri, Kai hatta University of Maiduguri sai da aka rufe...

Anyi Lokacin da tsoron shiga cikin jama'a ake yi a cikin Maiduguri sabida tsoron tashin bōmb...

Anyi Lokacin da Maiduguri ya watse aka yi gudun hijira zuwa inda mutum zai samu aminci...

Anyi Lokacin da akayi wata tara ba mobile network a Maiduguri, idan mutum Yana so yayi waya sai ya biya kudin mota yaje Damaturu..

Anyi Lokacin da duk wani Jami'in tsaro boye kan shi yake...

Har Mai Girma Shehun Borno an kawai hari Allah madaukin sarki ya Kare shi.

Rashin tsaro yasa rana tsaka kawai aka haramta Mana hawa machine Wanda har yanzu ba'a hawa.

An k@she talaka.

An kas@he jami'an tsaro

An k@she Mai kudi.

An k@she sarakuna.

An k@she Malamai

An k@she Yan siyasa

An k@she Mana Dan takaran gwamna.

An tada Bōmb a kasuwa

An tada Bōmb a masallaci

An tada Bōmb a makarantu.

Da matasa s**a gaji da irin cin kashin da ake yi musu, sai s**a tashi nemar wa kansu mafita.

S**a cire tsoro a zuciyar su, s**a fara k**a yan ta'addan, zaka ga mutum me bìndiga Yana gudun Wanda take da sanda.

Dan Bōko haram din da ake tsoro yanzu Kuma shike tsoron Yan gari, Yana gudu don tseratar da rayuwa sa..

kowa ya zama Dan kato da gora a cikin gari, matasa s**a fara aikin da Jami'an tsaro s**a kasa Yi.

Da ikon Allah cikin kankanin Lokaci matasa s**a tsaftace cikin garin Maiduguri, aka kori yan ta'adda zaman lafiya yazo.

Ku tashi ku nema wa kanku mafita in Sha Allahu Allah zai taimake ku.

Ubangiji Allah ka zaunar ka kasar mu lafiya.

✍️ Mohammed Isa Hassan

09/05/2023

Kuyi following na sabon page namu domin samun ingantatun labaru.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Maiduguri?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Maiduguri