At-tasfiyah24

At-tasfiyah24

Share

04/02/2026

ABOKIN FIRA

23. Wani Hani ga Allah Baiwa

Wasu fatake ne s**a yi tafiya a cikin jirgin ruwa wanda yake maƙare da hajarsu ta kasuwanci. A yayin da suke cikin tafiya suna raha suna nishaɗk suna tattauna al’amurransu na ‘yan kasuwa, sai kawai aka ji igiyar ruwa ta yunƙura k**ar za ta kifar da jirgin. Nan take s**a shiga taitayin su.

Wani ya ba da shawarar a rage ma jirgin lodi domin kayan da ya ɗauko sun yi masa nauyi sosai. Ba tare da tsayawa yin shawara ba aka yanke hukuncin a zubar da kayan Alhaji Jatau saboda su s**a fi zama kusa da gaɓar teku, kuma daman babu cikakken shiri tsakanin sa da manyan ƴan kasuwa.

Da Alhaji Jatau ya yi gardama sai s**a ga ba su da lokacin jayayya da shi a wannan yanayi da ake ciki.
Don haka, sai aka sa ƙarti s**a wurga shi tare da kayansa cikin teku, s**a ci gaba da tafiya abin su.

Alhaji Jatau ya ji kawai kunfan teku yana yawo da shi ba abin da yake yi sai Hailala yana neman agajin Mai-sama. Can sai ya ji an jefa shi a wani ɗan tsibiri taƙaitacce da babu mutum ballai aljani a cikin sa.

Da ya farfaɗo ya dawo hayyacinsa sai ya lura da wasu ƴan ganyayyaki waɗanda ya riƙa cin su k**ar yadda akuya take cin ciyawa. Idan ya ƙoshi sai ya sha ruwan da ke kwarara mai daɗi daga tsakiyar wannan
tsibiri.

A rana ta biyu ya saki jiki ya fara sabawa da wurin har ya ciro wasu rassan itatuwa ya gina ma kansa ƴar bukka wacce ya tsuguna a cikin ta.

A rana ta uku sai ya samu wata dabara ya dantse wata ƴar makwarara inda ƴan ƙananan kifaye suke wucewa. Sai ya fara farautar su yana gasawa yana yin kalaci.

Ranar da Alhaji Jatau ya cika kwana bakwai a cikin wannan tsibiri, da daddare ya hura wuta k**ar yadda ya saba don gasa kifayensa
sannan ya je wurin tarkonsa don k**a wasu. Daga can sai ya hango wuta ta k**a ƴar bukkar tasa.

Da yake abin ba mai yawa ne ba ko da ya iso bukkar ta ƙone ƙurmus. Alhaji Jatau ya damu matuƙa da wannan ci baya da ya samu. Amma ya yi haƙuri ya mayar da lamarinsa ga Allah Gwanin Sarki.

A daidai lokacin da alfijir yake ketowa sai wani ɗan ƙaramin jirgi ya dunfaro tsibirin da Alhaji Jatau yake cikin sa. Da jirgin ya iso sai ya ga wasu mutane baƙi da bai san su ba.

S**a nemi ya shigo jirginsu domin su tsallakar da shi. Ya tambaye su, ya aka yi s**a san da zaman sa a wurin? Sai s**a ce, ai mun hangi wuta ne tana ci a wannan yankin jiya da daddare, shi ya sa muka gane akwai mai neman taimako.

Da ya ba su labarin abin da ya faru da shi da ƴan kasuwar da s**a wurga shi a cikin teku sai s**a sanar da shi cewa, wannan jirgi tun a wannan ranar da s**a jefar da shi ya haɗu da ƴan fashi kuma duk sun kashe waɗanda ke cikin sa sun yi awon gaba da kayansu.

Darussa:
- Shirin Allah gare ka ya fi naka ga kanka.
- Kada ka cuci kowa. Idan an cuce ka ka nemi haƙƙinka wurin Allah
- Wani hani ga Allah baiwa ne

✍️ Prof. Mansur Sokoto

01/02/2026

ABOKIN FIRA

22. Uba Mai Hikima

Wani matashi ne ya ji wa’azi a kan haƙƙin mahaifa. Ya tsima sosai, yana son ya biya mahaifinsa haƙƙin haifuwar sa da rainon sa da ya yi.

Sai ya zo ya sami mahaifin nasa, ya ce masa: “Baba, yau ina son duk abin da kake so a duniyar nan ka gaya min shi. Zan yi maka ɗa''a. ba tare da gajiyawa ba”.

Mahaifin nasa ya yi farin ciki da jin wannan magana matuƙa. A nan kuma ya so ya koya ma ɗansa wani darasi mai girma. Sai ya ce masa, babu abin da nake sha’awa k**ar lemun zaƙi.

Amma ina son k**ar guda goma. Nan take yaron ya tashi ya zabura cikin kuzari da karsashi ya je kasuwa ya ciko kwando da lemun zaƙi.

Da mahaifinsa ya ga haka sai ya sa masa albarka. Ya ce, ciro min guda goma kawai. Ya sa hannu ya zaɓa masa nunannu guda goma.

Daga nan kuma sai mahaifin ya ce masa, ni ina sha’awar in sha lemun nan ne a saman bene. In da ma za ka goya ni ka kai ni can. Yaro ya ce, ai ba damuwa. Bismillah. Ya goya shi ya kai shi saman bene.

Sannan mahaifin ya ɗauki lemu guda ɗaya ya kwalɗe. A maimakon ya jefa a bakinsa sai ya wurga shi ƙasa. Ya ce ma yaron ɗauko mani shi.

Yaro ya sauka ya ɗauko lemu a cikin mamaki da ta’ajjubi. Isowar sa ke da wuya sai ya tarar da mahaifinsa ya sake kwalɗe wani, kuma a gaban
idonsa ya sake wurga shi ƙasa. Abu dai k**ar wasa sai ga shi duk� lokacin da ya hawo sai ya sake sauka don ya ɗauko lemun da mahaifinsa ya jefa ƙasa.

Nan take fuskar yaron ta fara canjawa. Kafin a kai lemu na bakwai yaron ya yi gajiyar haƙuri ya ce ma babansa, mene ne haka kuma Baba? Sai mahaifin nasa ya ce, na san kana son ka rama abin da na yi maka ne na alheri da kyautatawa. Ko ba haka ba?

Ya ce, haka ne Baba. Ya ce, to, a lokacin kana ƙarami sosai akwai watarana,
ina zama na a ƙasa ka sa ni na je kasuwa in sayo maka ƙwallo. Da na kawo maka ƙwallon sai ka ce a saman bene kake son ka yi wasa da ita. Kuma ka ce dole ne sai na goya ka. Da na hawo da kai sama sai ka riƙa jefa ƙwallon a ƙasa kana yi min kuka sai na ɗauko maka ita.

Haka na yi ta zirga zirga yadda ka yi a yau tun bayan sallar azahar har aka kira
la’asar ban ce maka na gaji ba ko na nuna maka damuwa ko ƙosawa.

Darussa:
- Sanin girman haqqin iyaye
- Kada ka gwale mutum idan bai yi daidai ba. Ka sa hikima a wajen lurar da shi da yi masa gyara.�

✍️ Prof. Mansur Sokoto

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Culinary Team

Attire

Website

Address


Kano