Lukman Tambuwal

Lukman Tambuwal

Share

25/06/2026

Ga wata tambaya akan reciprocal expressions

25/06/2026

Profit Function Challenge

24/06/2026

Da mu yarda da kada mu yarda, Arewa tafi ko wane yanki lalacewa a Nigeria.

Kuma wannan ya samo asali ne daga bad governance, da bakin cikin attajira da hassada daga wurin talakawa. Wannan a haɗe sai ya kawo tsabagen talauci da jahilci a yankin mu.

Gwamnati tana da dimbin dukiya da zata iya ƙirƙirar kamfunna da zasu samarwa yan kasa aikinyi da zai rage aikatan wasu abubuwa da ba daidai ba daga wurin matasa, amma tafi gwammace wa tayi abunda ba zai amfani mafi yawan talakawa ba, domin idan matasa sunada aikin yi, kuma suna iya riƙa kawunan su, toh wannan zai rage loyalty, kuma ba abu ne da yan siyasa suke so ba.

Shi talauci yana da kalu bale kala kala, daya daga ciki shine: zai iya sa a saka ka yin abu koda ranka bai so ba. Idan kunyi musu, ina so ku gayamin area boy daya a Sokoto wanda ya fito daga gidajen yan siyasa masu rike da mulki ko kuma wanda baban sa babban attajiri ne.
Idan an kasa kawowa, toh a gaya min kuma su waye suke goyon bayan area boys.
Duk yan bandits dinda ke arewa daga gidan talakawa s**a fito kuma daga gidan da babu ilimin addini dana zamani, dan haka sumfi saukin a sauya masu ra'ayi da tunani.

A lokacin da ilimin addini da na boko s**a yawaita, mutane zasu fara fahimtar yancin su, dan haka sai shuwagabanni s**a bari ilimi ya tabarbare a arewa. A yau da nike wannan rubutu, duk wata primary ta gwamnati dake Sokoto ba zaka tarar da yayan shuwagabanni ko attajira a cikin su ba, an barwa yayan talakawa suje suyi wasa su koma gida idan lokacin tashi yayi, saboda ko karatu ba'a yi cikin su, malaman da ake dauka su karantar, da yawan su basu san me suke yi ba, kuma gwamnati tana yin hakan ne da gangan domin kada a samu nagartaccen ilimi.

Duk da cewa mune ke da yawan musulmai, amma mumfi kowa yawan mabarata, saboda anyi corrupting malamai, basu gaya wa mutane sakon Allah da Manzon Allah yanda ya dace, kalilan ne ke fadan gaskiya. Yau idan malami yana isar da sakon Allah yanda ya dace, gwamnati na jawo shi ga jiki zaku ji yanayin karatukan sa sun sauya.

An dena koyar da tahiri, da yawan matasa a yanzu basu da labarin lokacin da mai kuɗi a anguwa zai tara yaran anguwar yayi masu kaciya gaba ɗaya, basu da labarin lokacin da babu makwancin dake kwana da yunwa saboda bai zama dole mutum yaci abincin gidansa ba. Basu da labarin lokacin da makwanci shike hukunci ga yayan makwabtan sa, har bada aure shi zai yi. Dadai sauran su.

Yau talaka a arewa ya koma tarkar danshi aka kirkiro hassada, ba'a so kowa yaci gaba, idan arzikin mutum ya karye, har zama majalisa za'a yi ana labari ba tare da nuna tausayi ba.

Kuma ina tabbatar muku duk wannan ya samo asali ne daga shuwagabanci marar inganci. Da wayo na nasan lokacin da mai anguwa zai iya aika wa a kira koma wanda yafi kowa kuɗi a anguwa kuma dolen sa yaje, amma yanzu mai anguwa saidai ka gansa bakin gidan mai kuɗin yana jiran sa ya farka daga bacci.

Yau a arewa kawai zaku ga mutum yana cikin talaucin gaske, amma k**a bashi 500k zai iya zuwa ya karo aure. Saboda baida mu da future dinsa ba, bai damu da ya ya'yan sa zasu tashi ba. Shi yasa duk yayan da ake saki kan t**i suna yawo babu kula zaku tarar yayan talakawa ne, idan aka yi magana sai kuji suna fadan cewa Allah ke lalura, saboda abunda malamai s**a gaya masu kenan. Alhamdulillah mu ba jahilai bane, munsan tafsirin da karya aka yi shi, domin Allah baiyi alkawarin taimakon kowa ba sai wanda ya fara tashi ya taimaki kansa sannan Allah ya k**a masa.
اللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُوا مَا بِأَنْفُسِهِمْ

"Lalle Allah ba Ya canja halin da ke ga wasu mutane har sai sun canja abin da ke cikin zukatansu (ko halayensu)."

احْرِصْ عَلَى مَا يَنْفَعُكَ، وَاسْتَعِنْ بِاللَّهِ، وَلَا تَعْجِزْ

"Ka yi ƙwazo a kan abin da zai amfane ka, ka nemi taimakon Allah, kuma kada ka zama mai kasala ko raunana."

أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَعْقِلُهَا وَأَتَوَكَّلُ أَمْ أُطْلِقُهَا وَأَتَوَكَّلُ؟ قَالَ: اعْقِلْهَا وَتَوَكَّلْ.

"Daga Anas bn Malik (RA), wani mutum ya ce: 'Ya Rasulullah, in ɗaure ta (raƙumina) sannan in dogara ga Allah, ko kuwa in sake ta kawai sannan in dogara ga Allah?' Sai Annabi ﷺ ya ce: 'Ka ɗaure ta sannan ka dogara ga Allah.'"

23/06/2026

Circle geometry

Telephone