Murya daya TV
29/06/2026
Masha Allah Happy Marriage life ❤️
28/06/2026
Tambayoyi 4 Da Wasu 'Yan Najeriya Ke Neman Amsa Daga Sufeto Janar na 'Yan Sanda (IGP)
Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta ce bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta mai nuna wasu dauke da makamai a kan babura an fassara shi ba daidai ba. A cewarta, mutanen da aka gani a bidiyon mambobin kungiyar tsaro ta sa-kai ne da kuma mafarauta masu rijista.
Sai dai wasu na tambaya:
1. Ta yaya aka ba wa kungiyar tsaro ta sa-kai damar sanya kayan sojoji?
2. Me ya sa suke dauke da manyan makamai masu karfi?
3. Me ya sa wasu daga cikinsu s**a rufe fuskokinsu kuma ba su sanye da kayan aiki na hukuma kamar yadda aka saba gani a kungiyoyin sa-kai?
4. Me ya sa aka ga suna hayaniya tare da yawo da makamai a kan hanya, abin da wasu ke kallon barazana ga jama'a?
Haka kuma, idan mafarauta ne kamar yadda aka bayyana, ta yaya suke mallakar irin wadannan manyan makamai da ba a amince wa fararen hula su rike ba?
Majiyar labari: Igbere TV
Ra'ayi: Har sai an gano ainihin tushen matsalar tsaro tare da samun amsoshi masu gamsarwa kan irin wadannan tambayoyi, zai yi wahala a samu mafita mai dorewa. Na kuma sha tambaya kan rawar da dakarun Amurka da aka ce suna taimakawa rundunar sojin Najeriya tun daga watan Janairu suke takawa a kasar. Nan ba da jimawa ba zan gabatar da nazari kan wannan batu.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Address
Kaduna
A.S.KD