SURAJ JOURNALISt
14/06/2026
•SHEIKH ISMA'ILA IDRIS BIN ZAKARIYYA: JAGORAN DA YA TSAYA TSAYIN DAKA WA TAUHIDI DA SUNNAH
•Lokacin da Sheikh Isma'ila Idris bin Zakariyya ya fara da'awarsa, kira zuwa ga Tauhidi da Sunnah bai samu yaɗuwa da karɓuwa sosai ba a sassa da dama na Arewacin Najeriya. A irin wannan yanayi ne ya fito da ƙarfinsa da jajircewa, yana koyar da Alƙur'ani da Sunnah tare da kira zuwa ga tsarkake addini daga abin da yake ganin ya saɓa wa koyarwar Musulunci.
•Bai kasance cikin waɗanda s**a zaɓi yin shiru saboda tsoron s**a ko adawa ba. Ya sadaukar da rayuwarsa, lokacinsa da iliminsa wajen yaɗa abin da ya yi imani shi ne gaskiya. Duk da ƙalubale da ƙin amincewa da ya fuskanta a wasu lokuta, bai gushe ba yana kira zuwa ga abin da ya yi imani shi ne tafarkin Alƙur'ani da Sunnah.
•Ta dalilin irin wannan ƙoƙari dubban matasa s**a karkata zuwa neman ilimin addini, aka samu malamai da masu da'awa da dama, sannan aka bunƙasa harkar ilimi da wa'azi a wurare masu yawa.
•Ko mutum ya yarda da shi a kowane irin ra'ayi na fahimta ko bai yarda ba, tarihi ba zai taɓa mantawa da gudunmuwar da Sheikh Isma'ila Idris bin Zakariyya ya bayar wajen bunƙasa da'awar Musulunci da yaɗa ilimin addini a Najeriya ba.
SURAJ JOURNALISt ✍️
14/06/2026
•A tarihin Izala, akwai abubuwan da za a iya saɓani a kansu, amma abu ɗaya da yake da wahala a musanta shi ne gudunmuwa da Sheikh Isma'ila Idris bin Zakariyya (Rahimahullah) ya bada wajen kafuwa da bunƙasar wannan tafiya.
•Mutane da yawa sun taimaka, wasu sun ba da kuɗi, wasu sun bayar da goyon baya, wasu kuma sun tsaya tsayin daka tare da Malam har aka yi nasarar kafa Kungiyar. Amma idan za a ambaci mutumin da ya zama fuskar kiran mutane, Wa'azi, Muqabala, tsara yadda Kungiyar zata dinga fita Wa'azi kuma jagoran tafiyar, sannan muryar da ta ɗaga tutar "Izalatil Bid'ah Wa'Iqamatis Sunnah" har ta zama abin da duniya ta sani a yau, to tarihi yana nuna Sheikh Isma'ila Idris bin Zakariyya ne.
•Duk wanda yake son ya fahimci tarihin Izala da gaske, ba zai iya cire sunan Sheikh Isma'ila Idris daga sahun farko na assasawa da gina wannan tafiya ba. Tarihi ba ya canzawa da son rai, kuma girman gudummawa ba ya gushewa saboda saɓanin ra'ayi.
•Allah Ya jiƙan Sheikh Isma'ila Idris bin Zakariyya, Ya saka masa da alkhairi bisa abin da ya bayar ga da'awar Sunnah.
SURAJ JOURNALISt ✍️
14/06/2026
•Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir: A Lifetime Dedicated to Islam and the Pursuit of Knowledge
•Sheikh Jingir (Hafizahullah) has devoted his life to the service of Islam, beginning from his youth with an unwavering commitment to teaching, preaching, and nurturing generations of Muslims. From his early days as a classroom teacher to his emergence as one of Nigeria’s most influential Islamic scholars, he has remained steadfast in serving both the religion and the wider society.
•Every Friday, Sheikh Jingir delivers insightful lectures that often last more than an hour, addressing issues of Islamic creed (Tawheed), moral upbringing, and sound religious understanding. Broadcast from the city of Jos, these lectures reach millions of listeners and viewers across Nigeria and beyond, making him one of the most widely followed Islamic scholars in the region.
•As the successor to the leadership legacy established by the late founder of Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Ash-Sheikh Isma’ila Idris bin Zakariyya Jos (Rahimahullah), Sheikh Jingir has distinguished himself through his firm adherence to truth, his refusal to compromise religious principles for personal interests, and his unwavering commitment to the teachings of the Qur’an and the authentic Sunnah of the Prophet Muhammad (peace be upon him).
•Beyond his scholarship, Sheikh Jingir is widely admired for his humility, respect for others, concern for his colleagues and followers, and his dedication to guiding people towards righteousness and moderation. These qualities have earned him the admiration of students, scholars, and countless Muslims, establishing him as a respected role model and a leading voice in contemporary Islamic guidance.
SURAJ JOURNALISt ✍️
•Iyayen Annabi ba yan wutæ hane Hadisin إِنَّ أَبِي وَأَبَاكَ فِي النَّارِ ya sabawa nassin Al-Qur'ani ~Sheikh Dalha Abubakar Abdullahi Kantana Al-maliky
•Gbamm 📌🧏 إِنَّ أَبِي وَأَبَاكَ فِي النَّارِ hadisin ya sabawa nassin Al-Qur'ani ~Sheikh Dalha Abubakar Abdullahi Kantana Al-maliky
13/06/2026
•Wakilin Malaman Bauchi ✊♥️
13/06/2026
•Masu s**ar hadisan Manzon Allah S.A.W manufarsu ba ta takaita ga Imam Bukhari da Imam Muslim kaɗai ba. A mafi yawan lokuta, abin da suke ƙalubalanta shi ne tushen ilimin hadisi gaba ɗaya.
•Domin idan matsalarsu littafin Sahih Al-Bukhari ko Sahih Muslim ne kawai, da sun karɓi hadisai daga sauran manyan littattafan Sunnah da malaman Musulunci s**a amince da su. Amma idan aka ga suna ƙin tsarin isnadi, suna ƙin ruwaya, kuma suna ƙin komawa ga Sunnah wajen fahimtar addini, to wannan yana nuna cewa matsalar ta fi Bukhari da Muslim girma.
•Abin lura shi ne, Al-Qur'ani mai girma ya umurci muminai da su yi biyayya ga Manzon Allah S.A.W, su karɓi abin da ya zo da shi, kuma su nisanci abin da ya hana. Hanyar da al'ummar Musulmi s**a san maganganun Manzon Allah S.A.W, ayyukansa da amincewarsa kuwa ita ce ta hanyar hadisi da isnadi.
•Saboda haka, duk wanda ya ƙi tushen hadisi gaba ɗaya, a zahiri yana ƙoƙarin cire wani muhimmin ginshiƙi daga cikin hanyoyin fahimtar addinin Musulunci ne.
•Allah Ya tsare mana Al-Qur'ani da Sunnah, Ya kuma sa mu kasance cikin masu bin gaskiya da hujja.
✍️ SURAJ JOURNALISt
13/06/2026
•Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir Hafizahullah ya sadaukar da rayuwarsa tun yana matashi wajen koyar da addinin Musulunci da yaɗa ilimi ga ɗalibai da al'ummar Musulmi. Tun daga matsayin malami a aji har zuwa shugabancin malamai a Najeriya, ya kasance cikin hidimar addini da al'umma ba tare da gajiyawa ba.
•A kowace ranar Juma'a, Sheikh Jingir yakan shafe sama da awa guda yana gabatar da darussa masu amfani da saƙonni na tarbiyya, tauhidi da fahimtar addini. Waɗannan darussa da ake gudanarwa daga birnin Jos suna isa ga miliyoyin mutane a sassa daban-daban na duniya.
•A matsayinsa na wanda ya gaji jagorancin da marigayi mu'assisin Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah, Ash-Sheikh Isma'ila Idris bin Zakariyya Jos Rahimahullah ya assasa, Sheikh Jingir ya kasance mutum mai tsayawa kan gaskiya, mai ƙin karkata ga son rai, kuma mai jajircewa wajen kare koyarwar Al-Qur'ani da Sunnah.
•Haka kuma, an san shi da mutunta mabiyansa, kula da abokan aikinsa, da kuma ƙoƙarin ganin duk waɗanda yake jagoranta sun kasance a kan tafarkin gaskiya da daidaito. Wannan ne ya sa ya zama abin koyi ga ɗalibai, malamai da al'ummar Musulmi gaba ɗaya.
SURAJ JOURNALISt ✍️
13/06/2026
•When the preservation of the Sunnah and the noble Hadith of Prophet Muhammad (peace and blessings of Allah be upon him) is discussed, few names shine as brightly as Imam Malik ibn Anas (rahimahullah).
•For Imam Malik, Hadith was not merely a field of study; it was a sacred trust. Such was his reverence for the words of the Messenger of Allah (peace be upon him) that whenever he intended to narrate a Hadith, he would perform ablution, wear clean and dignified clothing, apply perfume, and sit with utmost composure and respect.
•His commitment to authenticity was unmatched. He was extremely cautious in accepting narrations and would not take Hadith from a person solely because of their piety or social standing. Rather, he carefully examined their honesty, reliability, memory, and precision before accepting their reports.
•Imam Malik famously said:“I met seventy men in this mosque who could be trusted with the public treasury, yet I did not narrate Hadith from any of them.”
•Their integrity was never in question. However, preserving and transmitting the words of the Prophet (peace be upon him) demanded a level of expertise, accuracy, and scholarly discipline beyond ordinary trustworthiness.
•Perhaps one of the clearest signs of his greatness was his humility. Despite being recognized as the Imam of Madinah and one of the foremost scholars of Islam, whenever he was asked about a matter he did not know, he would simply reply:
“لا أدري”
“I do not know.”
•In an age when many people hesitate to admit the limits of their knowledge, Imam Malik left behind a timeless lesson: true scholarship is not measured by how much one speaks, but by knowing when to say, “I do not know.”
•His life remains a powerful testimony to the respect, caution, and humility required in preserving the legacy of the Prophet Muhammad (peace and blessings be upon him).
SURAJ JOURNALISt ✍️
13/06/2026
•YAYA AKE SON ANNABI S.A.W SOYAYYA TA GASKIYA?
•Mutane da yawa suna ikirarin son Annabi Muhammad S.A.W, amma shin soyayyar da muke yi masa tana tafiya ne bisa koyarwar Allah da Sunnarsa?
•Allah Madaukakin Sarki Ya sanya mana ma'aunin soyayya ta gaskiya inda Ya ce "Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah Ya so ku kuma Ya gafarta muku zunubanku." [Ali Imran: 31]
•Don haka, soyayyar Annabi S.A.W ba ta tsaya ga furta kalmomi ko nuna jin dadi kawai ba. Soyayya ta gaskiya ita ce:
•Bin umarninsa.
•Koyi da sunnarsa.
•Girmama koyarwarsa.
•Kare martabarsa da addinin da ya zo da shi.
•Gabatar da maganarsa akan ra'ayin kowa.
•A lokaci guda kuma, soyayya ta gaskiya ba ta nufin wuce gona da iri a kansa. Annabi S.A.W da kansa ya yi gargadi cewa kada a ɗaukaka shi fiye da matsayin da Allah Ya ba shi. Shi bawan Allah ne kuma Manzonsa mafi daraja.
•Saboda haka, duk wanda yake son Annabi S.A.W da gaske, zai nemi ya yi rayuwarsa bisa tafarkin da ya koyar, domin mafi girman shaidar soyayya ita ce biyayya.
•Ba a auna soyayyar Annabi S.A.W da yawan da'awa ake yi, ana aunata ne da yawan bin Sunnarsa.
•SURAJ JOURNALISt ✍️
Click here to claim your Sponsored Listing.