Bello Abdullahi Rogo
29/11/2025
Copy.copy.copy... Yunkuri da Mai Girma Tsohon Gomnan Kano Dr Abdullahi Ganduje yakeyi na kirkiro Hukumar Hisbah , Babban Kuskure ne, Ta'addanci ne da cin mutuncin Demokradiya ne, Sabawa Dokane, Yunkurin Tada Husumiya ce, Kuma Barazana ce ga Tsaron Jahar Kano.
Da farko dai a yanzu dai Baba Ganduje ba shi da hurumin zartarwa , Iko ko yunkurin Kafa wata Rundunar Hisbah a jahar kano a karkashin dokar Najeriya.
Sashi na 176(2) na Kundin Tsarin Mulkin kasa 1999 ( Constitution) ya ce: Gwamna jaha ne zai zama shugaban gudanarwa na Jihar da yake mulka. Abin nufi shine, mutum daya tilo ne da ke rike da waccan ofishin tsarin mulki a Kano shi ne Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kundin tsarin mulkin kasa bai bai wa tsofaffin gwamnoni ko wani mutum wani iko na zartaswa ko kuma kafa wata hukuma ko rundunar Hisba ba, haka kuma bai ba bawa wani tsohon gomna damar kafa hukumomin da za su iya yin tasiri kan zaman lafiyar jama’a ko sauya tsarin tafiyar da harkokin mulki na Jiha ba.
Daman can Ita Jahar kano tana da Hukumar Hisbah, wanda take da Dokokin da s**a kafata, tsarin gudanarwa da kuma hurumin da take aiki akai da kuma kotuna da suke da hurumin saurarar karaki a s**a shafe ta.
Idan Har Baba Ganduje yana da Niyyar kafa wata rundina na tsaro ko kuma hukumar Hisbah, yakamata ya Aika da bukatar hakan wajen Gomnan jahar kano ko kuma ya Aika fadar dokokin jahar kano ( Kano State House of Assembly) ko kuma ya samu Member mai Wakiltar Yankinsa, Anma akasin haka zai iya haifar da mummnar ta'addanci da haifar da manyan matsalolin shari'a da tsaro:
Tsarin Mulki na 1999 ya sanya duk abubuwan da s**a shafi hukumar 'yan sanda da jami'an tsaro a ƙarƙashin jerin dokoki na musamman (Sashe na 4 da Sashe na I, Jadawalin Na biyu). Gwamnatin Tarayya ce kawai za ta iya kafa ’yan sanda ko jami’an tsaro. Yayin da JIHOHI kuma na iya ƙirƙirar ƙungiyoyin gudanarwa ko al'adu/addini kamar Hisbah, waɗannan ƙungiyoyin dole ne su yi aiki a ƙarƙashin ikon gomnan jiha. Mutum da Gomna ba bashi da ikon kafa wata rundunar tsaro ko hisba a kowane jaha. Wannan babbar Fyade ne ga demokradiya da kuma tsarin mulkin kasa.
Dokar Hisbah ta Jihar Kano: Jihar Kano ta riga ta mallaki hukumar Hisbah da aka amince da ita. Gwamna mai ci da ‘yan majalisar jiha ne kawai za su iya kirkira, gyara, ko sake fasalin irin wannan hukuma. Tsohon gwamna, ba tare da izini, iko, ko goyon bayan tsarin mulki ba, bai dace yayi kutse ba ko kuma yayi irin wannan mummunar yunkurin.
Babban Hadari ne Kafa Jami'an tsaro masu zaman kansu kamar Hisah da Ganduje ke niyyar kafawa;
Sashi na 227 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya haramta wannan yunkuri kai tsaye: sashin ya ce " A Kiyaye kafa duk wani jami'in tsaro mai zaman kansa, 'yan bindiga, ko kungiya makamancin haka."
Shawarar da Ganduje ya zo da ita, na dauke da abubuwan da ke da matukar hadari da muni da baza 'a iya mantawa da su ba , musamman idan aka yi la’akari da ma’auni ( na daukan ma’aikatan Hisbah 12,000) da ayyukan tsaro da aka tsara. Irin wannan matakin haramun ne a tsarin mulkin kasa kuma yana da hadari, ba wai ga jihar Kano kadai ba, har ma demokaradiya da Nigeria gaba ki daya.
Wannan Yunkuri da Tsohon Gomna ke da niyyar yi, yayi kamanceceniya da yunkurin da Nmandi kanu na Yankin Nyamurai yake so yayi na kafa Rundunar Tsaron Biafra "Ipob armies" da kuma na bangaren yarabawa mr Sunday Igboho na kafa Rundunar Tsaro , saboda dukkaninsu suna da yunkurin kafa wata rundunar tsaro ne.
Shawarana ga Mai Girma Tsohon Gomnan kano, Dr Abdullahi Ganduje da ya dubi Allah, ya mutunta Gomantin da mutanen kano S**a zaba, ya girmama Dokar Kasa, ya san cewa Abinda yake yunkurin yi , Ta'addanci ne kuma ya sabawa duk dokokin tsarin mulkin kasa.
Ya saka Ci gaban jahar kano a zuciyansa, ya cire son rai da kuma neman tada zaune tsaye. Wannan yunkuri idan ya tabbata lalle zai jefa jahar kano cikin masifar da baza'a taba fita daga cikiba.
Hamza N. Dantani
Lawyer mai rajin kare hakkin Dan Adam .
Lawyer na tsarin mulkim kasa.
26/11/25.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Ore
MAYMARYAM