Dan Inde Tech
05/09/2025
LABARI MAI ZAFI (WAEC 2026)
Takaitaccen rahoton taron da aka yi tsakanin wakilan makarantun sakandare da hukumar WAEC a ranar 30 ga Agusta, 2025.
Jarrabawar WASSCE ta shekarar 2026 za a gudanar da ita gaba ɗaya ta kwamfuta, ba tare da wani zaɓi ba.
Dole a yi wa ɗalibai rijista a makaranta, amma WAEC ce za ta ba su cibiyar jarrabawa.
Makarantun da suke shirye su zama cibiyar WAEC/CBT su sanar da su cikin gaggawa.
Jarrabawar "Objective" za ta kasance gaba ɗaya ta kwamfuta kuma ɗalibai za su rubuta takardu uku a rana ɗaya.
Rubutattun tambayoyi/“Theory” za a yi su a ɗakunan taro na makaranta kuma za a yi amfani da “projector”. Ba za a ba da takardun tambaya ba, sai dai takardun amsa kawai.
Ayyukan “Practical” za a yi su a cibiyoyin jarrabawa kuma malamin da zai jagoranci ɗaliban dole ya iya amfani da kwamfuta. Malamin na iya kasancewa daga makarantar ko kuma ba daga can ba.
Kayan aikin “Practical” makarantar da ɗalibanta ke rubuta jarrabawa a cibiyar ce za ta bayar.
Ba a tilasta wa wata makaranta ta sayi kwamfutoci ba saboda da shirin makaranta ko babu shi, dole ne a gudanar da jarrabawar.
Makarantun da s**a cika sharuddan zama cibiyar jarrabawa za su karɓi kuɗi daga WAEC koda ɗalibansu na daga cikin masu amfana.
Makarantu da suke da kwamfutoci 50 za a iya ɗaukar su a matsayin cibiyar CBT matuƙar za su iya ɗaukar ɗaliban wasu makarantun.
Dan Inde ✍️~
15/02/2025
Karatu kyauta a intanet. Free online courses
How to study with Certificate Online Free using this method. ( Yadda zakayi karatu a Intanet free) Follow the Dan Inde Tech Solutions channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaAznOf9xVJhidNKZq0g
15/02/2025
Gyaran whatsapp
Gyaran WhatsApp Ta Hanya Mafi Sauki Ba tareda Ansha Wahala ba. Dan Inde Tech Solutions
15/02/2025
Kasuwar hausa ta online
The First and only Hausa E-Commerce App.(Kasuwar Online Nafarko da Yaren Hausa A cikin ta)
Click here to claim your Sponsored Listing.