Faje Media Update

Faje Media Update

Share

Sultan confirms July 9 as 2022 Eid-el-Kabir celebration day 04/07/2022

Sultan confirms July 9 as 2022 Eid-el-Kabir celebration day The Sultan of Sokoto and President of the Nigerian Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA), Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, has declared July 9 for

Photos from Rariya's post 30/06/2022

Operation show me your PROJECTS, NIGER STATE WHY na

Photos from Rariya's post 29/06/2022
2023: Har yanzu ina kokarin neman wanda zai min Mataimaki — Tinubu 27/06/2022

2023: Har yanzu ina kokarin neman wanda zai min Mataimaki — Tinubu Ya ce har yanzu bai kai ga yanke shawara a kan wanda zai dauka ba

26/06/2022

ZABEN 2023: Abubuwa Guda Biyar Da Atiku Ya Fi Kaf Masu Neman Mulkin Nijeriya

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Tabbas Allah ya azurya Alhaji Atiku Abubakar da wasu abubuwa guda biyar wanda kaf yan takarar neman mulkin Nijeriya basu dashi.

1) ilimin tsare iyakokin Nijeriya.

Ko shakka babu akan dukkan mu mun yadda da cewa Alhaji Atiku Abubakar tsohon jami'in kwastom ne wanda hakan ke nufin ya samu ilimin tsare iyakokin Nijeriya kuma babban matsalar Nijeriya a yanzu itace tsaro.

Bana raba dayan biyu akan cewa insha Allahu Alhaji Atiku Abubakar zai samu nasarar dawo da zaman lafiya cikin Nijeriya domin zai tsare iyakokin Nijeriya ta yadda miyagun mutane bazasu iya shigo da mak**ai cikin Nijeriya ba.

2) iya gudanar da mulki cikin ruwan sanyi.

Nasan dukkanmu munsan cewa Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban Nijeriya ne domin ya zama mutum na biyu a cikin Nijeriya daga 1999 zuwa 2007.

Basai nayi dogon jawabi ba amma dai nasan cewa dukkan mu munsan yadda Alhaji Atiku Abubakar ya yi gwagwarmaya wajan tafiyar da gwamnati a matsayin shi na mataimakin shugaban kasa wanda tarihi ya nuna cewa tun daga 1999 zuwa yanzu ba'ayi mataimakin shugaban kasa k**ar Alhaji Atiku Abubakar ba.

Domin shine mataimakin shugaban kasar da ya gudanar da aiki cikin ruwan sanyi kuma ya rege kaf gwamnonin arewacin Nijeriya a hannun shi wanda hakan ya haifar da babban rikici tsakanin shi da uban gidan shi kuma ya yi nasara akan uban gidan na shi.

3) Hada hadar kasuwanci da kuma Siyasa

Ayanzu haka kaf cikin masu neman mulkin Nijeriya a 2023 babu wani dan siyasa kuma dan kasuwa sai Alhaji Atiku Abubakar.

Domin Alhaji Atiku Abubakar gogaggen dan kasuwa ne kuma dan siyasa ne wanda ya shafe shekaru da dama yana jan zaren siyasar Nijeriya. Hasalima yana daya daga cikin jiga-jigan mutanen da s**a kafa jam'iyyar PDP.

Tarihin kasuwancin Atiku Abubakar' ya nuna cewa Atiku Abubakar ya fara kasuwanci yayin da yake zuba jari a cikin gidaje. Ƙarin lada shine ƙananan kasuwancin mai da iskar gas da ya fara tare da abokin tarayya na Italiya, Gabriel Volpi a cikin 1980s.

Atiku Abubakar ya yi rijistar kasuwancinsa a matsayin sabis na kwantena na Nijeriya (NICOTES) kuma yana aiki a ofishin kwantena a farkon kwanakin sa a tashar jiragen ruwa na Apapa, dake Legas.

Dukkan mu munsan cewa duniya takarkata ne yanzu akan manyan abubuwa guda biyu watau kasuwanci da kuma siyasa kuma ko shakka banayi akan cewa Atiku Abubakar ya samu ilimin siyasa da kuma kasuwanci wanda hakan ke nuna cewa Atiku Abubakar zai fadada hada hadar kasuwancin Nijeriya ta fuskar siyasa domin inganta tattalin arzikin Nijeriya.

4) Sakin Lalitar kasa domin wadatar da yan kasa ta fuskar rayuwar yau da kallum.

Dukkan mu mun yadda da cewa Atiku Abubakar mutum ne mai yawan kyauta tare da bada tallafi ga mabukata wanda hakan ke nuna mana cewa idan har Atiku Abukakar ya zama shugaban kasa toh yan kasa bazasuyi kukan tsadar rayuwa ba insha Allahu.

5) Kawar da kabilanci a cikin Nijeriya

Tarihi ya tabbatar da cewa babu kabilanci a cikin zuciyar Atiku Abubakar domin a yanzu shine dan takarar da ba'a taba samun shi da kyarar al'ummar wata yanki ko jinsi a cikin Nijeriya ba.

Muna rokon ubangiji Allah ya taimaki Atiku Abubakar akan kyawawan manufufin shi na alkairi.

Want your business to be the top-listed Media Company in Minna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Unguwan Liman FAJE Mashegu LG
Minna