SLT MEDIA
29/03/2025
A jihar Edo, wasu 'yan bindiga sun yi kisan gilla ga mafarauta 16 daga Arewa, wanda hakan ya haifar da tashin hankali a tsakanin al'umma. An kashe su ne a cikin wani mummunan harin da ya faru yayin da suke cikin aikin farauta. Wannan kisan gilla ya jawo hankalin kungiyoyin mafarauta da kuma al'umma, inda aka bukaci gwamnatocin Tarayya da na jihar Edo su dauki matakai cikin gaggawa don kamo wadanda s**a aikata wannan mummunan aiki.
Kungiyar mafarauta ta yankin Arewa ta yi kira ga gwamnatocin Tarayya da na jihar Edo su dauki mataki cikin sauri kan wadanda s**a yi kisan kai ga 'yan uwansu mafarauta guda 16 a jihar Edo. Sun bai wa gwamnatocin awowi 24 su kamo wadanda s**a aikata wannan mummunan kisan, kuma su fuskanci hukunci a bainar duniya.
Idan har ba a dauki mataki ba, daga wurin Sallar Idi, za su dauki matakin da ya dace. Kungiyar ta nuna rashin amincewa da daukar doka a cikin jeji, tana mai kira ga gwamnati ta tabbatar da adalci ga wadanda aka kashe da iyalansu.
Allah ya taimaka, ya basu nasara wajen ganin an samu adalci da hukunci mai kyau! 🙏
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Makarfi