DAN ALI TV
13/10/2025
YAN SOCIAL MEDIA NA PDP SHIGA TA KAWO GARE KU........
Hon Isah Mukhtar Gusau IG yayi kyakkyawan tsari na bada tallafi ga yan social media masu Watsa manufofin Mai daraja Gwamna Dauda Lawal da kuma watsa ayukkan Alkhairi da shi Hon Mukhtar Isah Gusau IG yake yi a cikin al'umma.
Wannan tsarin na tallafawa Yan Social Media zai zone Batch A da Batch B.
Rukuni na farko zasu karbi forms ɗinsu daga gobe 13th Oct, 2025 In sha Allah kuma su dawo da shi zuwa Ranar Jumu'a.
Allah ya sakama Hon Mukhtar Isah Gusau IG da Mafificin Alkhairi akan wannan tallafi da yake bayarwa a kowane Mataki na Al'umma.
Ɗan Ali Online Tv
+2347065535695
29/07/2025
Da dumi-dumi
Gwamna Dauda Lawal Ya Nada Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a Matsayin Sarki na 16 na Masarautar Gusau
A ranar 29 ga Yuli, 2025, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da nadin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin Sarki na 16 na Masarautar Gusau, wanda ya gaji mahaifinsa, Marigayi Dr. Ibrahim Bello, da ya rasu a ranar 25 ga Yuli bayan shekaru goma yana sarauta.
Nadin ya biyo bayan shawarwarin masu zaben sarki na masarautar Gusau, tare da bin al’adun gargajiya da dokoki na kasa.
Alhaji Abdulkadir, wanda shi ne babban ɗan marigayi sarki, yana rike da sarautar Bunun Gusau kafin wannan nadin. Shi ɗan asalin Malam Sambo Dan Ashafa ne.
Gwamna Dauda Lawal ya taya sabon sarki murna tare da kira gare shi da ya ci gaba da gadon kyakkyawar rayuwa da dabi’un sarakunan da s**a gabata, wanda zai zama jigo wajen ɗorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a masarautar Gusau da ma kewaye
Click here to claim your Sponsored Listing.