Tafida zing

Tafida zing

Share

06/06/2026

JAGABAN IN A N Y S C CAMP may god bless JAGABAN

31/05/2026

SHIN KUNSAN MEYESA THUMBPRINT ƊIN KOWANE YATSA YA BAMBANTA......✍️✍️

Fiye da shekaru 1400 da s**a gabata, Alƙur’ani ya ambaci wani sirri game da yatsun ɗan Adam wanda yake da matuƙar daidaito, wanda kimiyyar zamani ta fahimci muhimmancinsa ne bayan ƙarnika masu yawa.
أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَلَّن نَّجْمَعَ عِظَامَهُ ۝ بَلَىٰ قَادِرِينَ عَلَىٰ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُ

Allah Yace a cikin Alƙur’ani... “Shin mutum yana zaton ba za Mu tattara ƙasusuwansa ba?
Eh mana! Muna da ikon daidaita har ma da yatsunsa.”
(Al-Qiyamah 75:3–4)

A yau, kimiyyar binciken laifuka ta tabbatar da cewa zanen yatsan kowane mutum na musamman ne, hatta tsakanin tagwaye iri masu k**a ɗaya. Wannan ne yasa zanen yatsa ya zama ɗaya daga cikin hanyoyi mafi inganci wajen gane mutum.

(Forensic Science Handbook, FBI Scientific American: “No Two Fingerprints Are Alike”) Wato babu wasu yatsu guda biyu da s**a kasance iri ɗaya....

Alƙur’ani bai tsaya kawai ga ambaton ƙasusuwa ba, sai ya keɓance yatsu, yana nuna wani matakin daidaito wanda ɗan Adam bai sani ba a wancan lokacin.

Wannan aya tana daga cikin manyan ayoyin da suke nuna cikakken ilimin Allah da k**alar halittarsa. Zaka iya duba Tafsir Ibn Kathir akan Suratul Qiyamah aya ta 3–4.

Alƙur’ani ba littafin kimiyya bane, amma duk lokacin da aka gano wata gaskiyar kimiyya, za’a ci karo da abubuwa masu nuna hikima da daidaito a cikin Alƙur’ani.

وَمَنْ أَصْدَقُ مِنَ اللَّهِ حَدِيثًا
“Kuma waye yafi Allah gaskiya a magana?”
(An-Nisa’i 4:87)

Usman Abdurrazaq Gumel

03/05/2026

Shugaba ﷺ yace:
“Ina zaune, aka zo da mabudan taskokin arzikin ƙasa, aka sa su a hannuna.
In ya baka, ta bayu.
In ya hanaka, a haka zaka ƙare.

Shugaba ﷺ yace:
“Ni ne mai rabo, Allah ne Mai bayarwa.
Indai abu na Allah ne, Shugaba ne yake rarrabawa.
Karka yi dogon tunani, ka sallama kawai.”

Sallallahu Alaihi wa Sallam ﷺ

03/05/2026

IN ZAKA SAKI MACE DA ƳAƳA KANA BUƘATAR KAYI TUNANI KAMAR HAKA

1. Zata iya tafiya ta ajiye mini ƴaƴan.

2. Zata iya tafiya da su.

A halin ta bar maka ƴaƴan ya zaka yi dasu?

1. Zan bawa mahaifiyata ta kula da su. Ka sani tsaf kakarsu zata ce ba zata yi wahalarka sannan ta yi ta jikoki ba. Tsaf zata ƙi karɓa.

2. Wata zan auro ta kula da su. Tsaf zaka auro wacce zata iya kula dasu ko akasin haka.

3. Kai zaka kula da su. Wannan kam da wahala a matsayinka na Namiji.

Wani ya bawan Allah ne ya saki matarsa, ya gama yi mata cin mutunci. Kafin ta tafi ta dire masa ƴaƴansa, har ɗan shekara 2. Ya ɗauki yara uku ya kaiwa mahaifiyarsa, ita kuma ta rantse ba zata rike ba. A ƙarshe haka yazo muka tafi sulhu. Bayan dogon bada haƙuri da MUMINI ya rinƙa yi da kyar Mahaifinta ya haƙura.

A ƙarshe: mutuƙar kuna da ƴaƴa kuma MUMINA ba tazo da ɓarna mabayyaniya ba, kawai dai tana saɓa maka ne daga lokaci zuwa lokaci sai ka yi haƙuri, k**ar yadda kaima ka ke saɓawa Ubangiji kuma yake haƙuri da kai tare da cewa yana da cikakken iko akanka.

03/05/2026

With Zuwairiyyah Adamu Girei – I just got recognised as one of their top fans!

03/05/2026

🌿 TUNATARWA TA RANAR LITININ 🌿

❌ KADA KA ZAGI KOWA ❌

Rayuwa ba ta tsaya a yau ba…
Abin da ka faɗa yau, zai iya dawo maka gobe.

🗣️ Kalma mai kyau sadaka ce,
amma kalma mara kyau tana raunana zuciya
👂 Ka tuna:
Allah yana jin duk abin da kake faɗa…
💭 Idan ba za ka faɗi alheri ba,
to ka yi shiru – shi ne mafi aminci gare ka.

🤲 Ya Allah ka tsare mana harshe,
ka sa mu kasance masu magana da alheri kawai.

✨ Barka da Ranar Litinin – ka fara da kyawawan kalmomi.

Allah ya Amintar da mu

Want your business to be the top-listed Clothing Store in Lagos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Lagos