Dandume FORUM

Dandume FORUM

Share

04/10/2025

Isa Kaita College of Education ta Buɗe Damar Ilimi ga Mata da Taimakon Agile

Kwalejin Ilimi ta Isah Kaita College of Education (IKCOE), Dutsin-Ma, Jihar Katsina, ta bayyana wani shiri na musamman da aka tanada domin baiwa mata damar ci gaba da karatu a makarantar.

Shirin, wanda aka shirya tare da tallafin Agile Project, ya kunshi baiwa mata damar samun karatu ba tare da la’akari da halin zamantakewarsu ba. Wannan dama tana buɗe kofa ga mata aure, marasa aure, da kuma wadanda s**a taba yin aure amma s**a rabu da mazajensu.

A cewar hukumar makarantar, duk wata mace da take da sha’awar karatu a kwalejin na da buƙatar tura bayanan karatunta (qualification), lambar wayarta, da kuma inda take zaune.

Hukumar makarantar ta ce wannan dama ta musamman ce wadda za ta baiwa mata damar samun ilimi, kuma tana kira ga al’umma da su yada wannan sanarwa domin ta kai ga duk wanda abin ya shafa.

Domin ƙarin bayani ko tura sunan mace da ta cancanta, za a iya tuntubar lambar:

📞 08084462041
📞 08031569555

Makarantar ta yi kira da a yi gaggawar amfani da wannan dama domin tabbatar da cewa mata sun sami damar karatu da inganta rayuwarsu ta hanyar ilimi.

12/09/2025

🌾 Dandume Forum Special Report 🌾

Faduwar Farashin Hatsi: Rahama ga Talaka, Barazana ga Manomi

A halin yanzu, faduwar farashin hatsi a Najeriya na zama babbar barazana ga manoma. Duk da cewa saukar farashi ya taimaka wa masu siye, manoma na shiga cikin matsanancin hali:

Da dama suna cikin bashi kuma ba sa samun riba.

Wasu na tunanin daina noma gaba ɗaya.

Iyalan karkara na fuskantar ƙarin talauci.

Masana sun gargadi cewa idan aka bar wannan yanayi ya ci gaba, zai iya haifar da:

Ƙarancin abinci a nan gaba.

Dogaro da shigo da hatsi daga ƙasashen waje.

Rage darajar tattalin arzikin ƙasar.

Kiranmu a Dandume Forum:
“Manomi shi ne ginshiƙin ƙasar mu. Idan aka bar shi ya yi kuka shi kaɗai, to gobe duk al’umma za su yi kuka tare da shi.”

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Katsina