Arewa Reporters TV
28/03/2025
AlhamdulilLah, ana ta daɗa rage mugun iri!
Har yanzu akwai sauran rina-a-kaba a yaƙi da mugaye ƴan ta'addan daji amma ko shakka babu ana ganin haske. Daga shigowar gwamnatin Bola Tinubu zuwa yau an yiwa ƴan daji ɓarnar da ba a taɓa yi musu ba. Ya zuwa yanzu an kashe fitattun ɓarayin daji kamar haka:
1. Ali Kachalla/Ƙawaje
2. Kachallah Dogo Kwaddi
3. Lawali Dodo
4. Ɓoderi
5. Sani Wala-birki
6. Kachallah Hana-Zuwa
7. Damina
8. Kachalla Sani Dangote
9. Kachalla Adamu
10. Halilu Sububu
11. Baleri
12. Modi Modi
13. Kachalla Mai Shayi
14. Kachalla Tsoho Lulu
15. Ibrahim Nagure
16. Kachalla Makore
17. Bulak
18. Tukur Sharme
19. Hassan Ɗantawaye
20. Ɗan-Isuhu
Wannan nasara da ake samu ta kawo sauƙi ƙwarai ga al'ummomin dake maƙwabtaka da waɗannan miyagu. Insha Allah za a cigaba da nasara akan mugaye domin ƴantar da mutanen da suke ƙuntatawa a ko-ina-da-ina.
Allah ya cigaba da ɗora nagari akan mugu!
26/02/2025
Na yi farin ciki da saukowar farashin kayan abinci musamman ma yanzu da muke fuskantar azumi. Muna ganin haske da cigaba. Yayin da ƙasashe da yawa ke fama da matsaloli, mu a Najeriya muna ganin sauyi me kyau. A hankali al'amura na daidaita, sauƙi na ƙara samuwa. Mungodewa Allah!
– Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron ƙoli na jam'iyyar APC
FIFTEEN years ago, the matter was raised and addressed. 👇🏽
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Katsina