KASO ASOKA

KASO ASOKA

Share

10/05/2026

*MATA AYI HAKURI*

Idan Allah bai nufeki da yin aure ba gabaki daya

tuna da nana maryam عليه السلام da yadda Allah
ya mata albarka a gidan duniya da lahira, kuma
ya yabeta da kamewa a cikin littafinsa mai
tsarki, dukda cewa batayi aure ba.

Idan Allah سبحانه و تعال bai azurtaki da haihuwa ba:
kiyi hakuri kada ki daga hankalinki ko ki damu da
zancen mata
ki tuna matar Annabi Zakariyya
عليه السلام
da tayi hakuri sai Allah ya dubi zuciyarta ya
azurta ta da haihuwa dukda da cewa ta tsufa
shekarunta sun tafi.

Idan Allah ya jarrabeki da azzalumin miji mai
sabawa Allah da bijerewa hanyarsa
sai ki tuna
Asiya matar fir'auna, da Allah ya dubi zuciyarta
sai ya sanyata ta zamto daka cikin
shuwagabannin matan Aljannah.

Idan Allah ya kaddara miki rabuwa da mijinki
ko ya sake ki
sai ki tuna fadin Allah سبحانه و تعال
"Idan s**a rabu to Allah zai azurta kowa da
rabonsa.

Idan Allah yayiwa mai gidanki rasuwa kada
kiyita sanya damuwa a zuciyarki har ki rinka
furucin cewa bazaki taba samun wani wanda ya
fishi alkhairi ba
ki tuna ummu salma matar Abu-
salma, رضي الله عنه da mijinta yayi wafati sai Allah ya
canja mata da wanda ya fishi shine Annabi
Muhammad صلى الله عليه وسلم sabida kasancewarta daga
cikin masu cewa
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un,
a lokacin musiba.

Ki sanya a zuciyarki cewa arzikin ALLAH yana
zuwa..
Kada ki kwallafa ranki ko kisa ido ga arzikin da
Allah yayiwa wata ta kusa dake ko yar'uwarki..
Ki sani cewa Allah yana sane da halin da k**e
ciki, domin shi ya halicceki, kuma ya fiki sanin
kanki da damuwarki...

Kada ki damu da abunda mutane ke furtawa a
kanki, domin basuda abinda s**a isa su miki idan
ba wannan zancen ba, kuma shi baya cutarwa.
Allah ya shiryar da bisa tafarkin Shari'a.

Abu Ja'afar Assunny ✍️

10/05/2026

Matar Aure… 2 🤍

“Zuciyar miji ba da ƙarfi ake riƙe ta ba… da hikima ake riƙe ta.”

---

💭 Mata da yawa suna tambaya:

“Yaya zan riƙe zuciyar mijina?”

Amma gaskiya ita ce:
ba duk da ƙoƙari mai yawa ake yin hakan ba… sai da abubuwa masu sauƙi amma masu tasiri.

---

🤍 1. Kyakkyawar magana 🗣️

Namiji yana son:

– kalma mai laushi
– girmamawa
– jin ana darajarsa

💡 Kalma ɗaya mai daɗi…
na iya shafe gajiyarsa ta yini.

---

🤍 2. Girmamawa 🙇‍♀️

Ko da kuna wasa…
ko da kuna cikin nishaɗi…

✔ Kada ki rage masa daraja
✔ Kada ki raina shi

💭 Namiji yana daraja mace da take girmama shi.

---

🤍 3. Fahimta 💞

Ba kowanne lokaci zai kasance cikin natsuwa ba…

– yana iya gajiya
– yana iya damuwa
– yana iya yin shiru

💡 Ki fahimta kafin ki yi fushi.

---

🤍 4. Ƙananan kulawa 💫

– murmushi 😊
– tambayar halinsa
– nuna damuwa da shi

Waɗannan ƙananan abubuwa…
suna da girman tasiri a zuciya.

---

🤍 5. Gujewa yawan gardama ⚠️

Ba kowace magana ake mayar da ita rikici ba…

✔ wani lokaci shiru ya fi
✔ wani lokaci hakuri ya fi

💭 Zaman lafiya ya fi nasara a gardama.

---

💔 Kada ki manta:

– tsawa tana raba zuciya
– raini yana kashe soyayya
– rashin kulawa yana sa nisa

---

💫 Sirrin gaskiya:

Zuciyar miji tana nan ne wajen mace da:

✔ take girmama shi
✔ take kula da shi
✔ take fahimtarsa

---

🌙✨ KARSHE

💭 Riƙe zuciyar miji ba sihiri ba ne…
ƙananan halaye ne masu kyau da ake yi kullum.

---

🤲 Allah Ya ba mu hikima da haƙuri, Ya sa mu zama matan aure masu riƙe gidajenmu da soyayya 🤍

19/03/2026

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah

Wallahi Tallahi Allah ya karɓi addu’o’inmu, sai dai mu jira lokaci, kada mu yi gaggawa.

Domin akwai abubuwan da idan ka roƙa aka baka nan take, watakila ba alkhairi bane gare ka. Amma idan aka jinkirta maka shi, sai ya zama alkhairi mafi girma, ko kuma Allah ya musanya maka da abin da yafi alheri. Wani lokaci kuma Allah yana hana ka ne domin ya kare ka daga abin da zai cutar da kai, ko kuma ya rubuta maka ladan haƙuri mai girma.

Don haka mu dage da addu’a, mu yi yakini da Allah, mu guji gaggawa, domin Manzon Allah (S.A.W) yace: ana amsa addu’ar bawa muddin bai yi gaggawa ba.

Allah ya ƙara mana haƙuri da juriya, ya sa mu cikin bayinSa masu yawan addu’a da kyakkyawan zato gareShi. Allah ya karɓi ibadunmu da addu’o’inmu, ya biya mana buƙatunmu na alkhairi duniya da lahira, Ameen.

23/12/2025

*KADA KIYI FADA DA MIJINKI.*
-
"Ba sai kinyi faɗa ko hayaniya haɗi da zuwa gurin boka ba sannan za ki hana mijinki ƙaro aure, ki fahimci dukkanin abin da yafi so a rayuwar aurenku sai ki lazimci yi masa su, ki lazimci yi masa biyayya sau da ƙafa a cikin dukkanin abin da baici karo da shari'ar Allah ba, in sha Allahu cikin sauƙi za ki mallake shi, zai ji cewa ko ya ƙaro auren ma waccen baza ta iya biya masa irin buƙatun da k**e biya masa ba. Amma muddin kika ce za ki hana shi ƙaro aure alhalin ke kuma ba kya yi masa abinda yake da buƙata, to haƙiƙa kina yin faɗa ne da abin da yafi ƙarfinki"
-
"Mata da yawa sun ɗauka cewa sai sunyi hayaniya da mazajensu sannan za su hanasu ƙaro aure, wanda kuma hakan ba ƙaramin kuskure bane wanda zai iya haifar mata da matsala ga rayuwar aurenta"
-
"Da sannu za ki iya hana mijinki ƙaro aure kuma ba tareda kin saɓawa Allah ba. Shi ne ta hanyar yi masa biyayya da kyautata masa, da kuma biya masa dukkanin buƙatun da ya nema daga gareki, wanda hakan shi ake kira da halastaccen sihiri wanda babu saɓon Allah a cikinsa."

Ku biyomu a WhatsApp GA link dinmu
👇👇👇👇
Follow the Kaso Asoka channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7NYqaFsn0hWucSEc1G

21/12/2025

*ZIKIRORIN SAFE DA YAMMA*

Yin sakaci da Azkar din safe da Yamma kamar yin sakaci ne ka bar wata ƙofa da sharri ko cutarwa za su iya isowa gareka!

Ki/Ka yi Azkar din ka kuwa???

💠Ayatul kursiyyu (1).
💠Qul huwaLLahu Ahad (3×).
💠Qul a'udhu bi Rabbil falaq (3×).
💠Qul a'udhu bi Rabbin naas (3×).

💠Asbahnaa wa asbahal mulku Lillah (Idan da yamma ne kuma: Amsainaa wa amsal mulku Lillah), walhamdu Lillahi, laa ilaaha illaLLahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wahuwa alaa kulli shay'in k'adeer, Rabbi as'aluka khaira maa fi hazal yaumi wa khaira maa ba'adahu, wa a'udhu bika min sharri ma fi hazal yaumi wa sharri maa ba'adahu (da yamma kuma: Rabbi as'aluka khaira ma fi hazihil lailah wa khairi ma ba'adahu, wa a'udhu bika min sharri ma fi hazihil lailati wa sharri ma ba'adahu), Rabbi a'udhu bika minal kasal, wa suu'il kibar, Rabbi a'udhu bika min azabin fin naari, wa azabin fil ƙabar.

💠Allahumma bika asbahna wa bika amsainaa, wa bika nahyaa, wa bika namuutu wa ilaakan nushuur.
Idan kuma da Yamma ne:
Allahumma bika amsaina wa bika asbahnaa, wa bika nahyaa wabika namuutu wa ilaikal maseer.

💠Allahumma Anta Rabbiy laa ilaaha illa Anta, khalaƙtaniy wa ana abduka, wa ana alaa ahdika wa wa'dika mastaɗa'atu, a'udhu bika min sharri ma sana'atu, abuu'u laka bini'matika alayya, wa abuu'u bidhambiy fagfirliy fa'innahu laa yagfiruz dhunuba illa anta.

💠Allahumma inniy asbahtu (Idan kuma da yamma ne: Amsaitu) ushhiduka wa ushhidu hamalata Arshika, wa malaa'ikatika wa jamee'i khalƙika, annaka AntaLLaahu laa ilaaha illa Anta wahdaka laa shareeka laka, wa anna Muhammadan abduka wa rasuuluka.

💠Hasbiyallahu laa ilaaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa Rabbul Arshil azeem (Sau 7).

💠Allahumma inniy as'alukal afwa wal aafiyata fidduniya wal aakhirah, Allahumma inniy as'alukal afwa wal aafiyata fi deeniy wa dunyaya wa ahlee, wa maaliy, Allahummas-tur auraatiy, wa aamin rau'aatiy, Allahummah-fizniy min baini yadayya wa min khalfiy, wa an yameeniy, wa an shimaali

Follow the Kaso Asoka channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7NYqaFsn0hWucSEc1G

30/11/2025

Ku biyomu a WhatsApp channel dinmu
Kaso Asoka
👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029Vb7NYqaFsn0hWucSEc1G

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Katsina