DanMasani RADIO

DanMasani RADIO

Share

10/06/2026

Hare haren haɗin Gwiwar Najeriya da Amurka ya kashe sama da ’yan ta’adda 200 a Arewa maso Gabas - Hedikwatar tsaro

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa hadin gwiwar sojojin Najeriya da rundunar sojin Amurka a Afirka (AFRICOM) ta yi sanadiyyar kashe sama da ’yan ta’adda 200 tare da hallaka wasu manyan kwamandojinsu a yankin Arewa maso Gabas.

Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce ayyukan hadin gwiwar sun inganta tattara bayanan sirri, sa ido da kuma kai hare-hare kan maboyar ’yan ta’adda da cibiyoyinsu na samar da kayan aiki.

Ya kara da cewa an horar da dakarun Najeriya tare da karfafa shirye-shiryen yaki da ta’addanci, lamarin da ya taimaka wajen samun nasarori a ayyukan tsaro.

A nata bangaren, Daraktar hulda da Jama’a ta AFRICOM, Rebecca Heyse, ta ce Amurka za ta ci gaba da hada kai da Najeriya muddin akwai barazanar tsaro da kasashen biyu ke fuskanta, tana mai jaddada cewa dukkan ayyukan hadin gwiwar na gudana ne bisa gayyatar gwamnatin Najeriya da mutunta cikakken ikon kasar.

Rahoton ya kuma tuna cewa a watan Mayu, wani samame na hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka ya yi sanadiyyar kashe Abu-Bilal Al-Minuki, wanda ake zargin mataimakin shugaban kungiyar ISIS ne a Najeriya.

10/06/2026

Mazaunin Jibia Ya Koka Kan Rashin Motar Ɗaukar Gawa a Babban Asibitin Jibia, Katsina.

Wani mazaunin Ƙaramar Hukumar Jibia a Jihar Katsina ya bayyana damuwarsa kan rashin motar ɗaukar gawa a Babban Asibitin Jibia, yana mai kira ga hukumomi da su ɗauki matakin magance matsalar.

Bello Iliyasu Shimfida, ɗan asalin garin Shimfida da ke Gundumar Mallamawa, ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba, 10 ga Yunin 2026.

A cewarsa, iyalan marasa lafiya da s**a rasu a asibitin na fuskantar ƙalubale wajen samun abin hawa da za su kai gawar gida. Ya ce yayin da wasu ke iya ɗaukar hayar mota saboda halin da suke da shi, wasu kuwa kan yi amfani da adaidaita sahu sakamakon rashin wani zaɓi.

Ya bayyana cewa amfani da adaidaita sahu wajen ɗaukar gawa ba hanya ce mai kyau ba, domin sau da yawa ba a iya rufe gawar yadda ya kamata, lamarin da kan jawo damuwa ko firgici ga jama'a, musamman a wuraren da ake da cunkoson ababen hawa.

Shimfida ya tuna cewa a baya wasu asibitoci kan kasance da motocin ɗaukar gawa da ake amfani da su wajen kai mamata gidajensu ba tare da ɗora wa iyalansu wani ƙarin nauyi ba.

Saboda haka, ya yi kira ga gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki da su samar da motar ɗaukar gawa a Babban Asibitin Jibia domin rage wa iyalan mamata wahala da ƙarin damuwa a lokacin da suke cikin alhini da jimamin rashin 'yan'uwansu.

Hikaya TV

10/06/2026

Ba Zamu Maida Matsalar Tsaro Hanyar Samun Kudi Ba” -- Sen. Yakubu Lado

Ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina na Jam'iyyar PDP, Sen. Yakubu Lado Ɗanmarke, ya ce idan jam’iyyar ta samu mulki, ba za ta maida matsalar tsaro hanyar samun kuɗi ba.

A cewar, Yakubu Lado da yawan shuwagabanni sun maida harkar tsaro hanyar samun kudi.
jonal

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

No. B27. Khalil Raman Shopping Complex. High Court Roundabout. Daura Road Katsina
Katsina
820221