Triple H Multimedia
01/11/2025
Uwar Jam'iyar ADC tare da Jagororin Jam'iyar A jahar katsina sunyi zama karkashin Jagorancin Shugaban Jam'iyar ADCn na jahar Katsina Alhaji Musa Usman Wamba
Zaman ya wakana ne a ofishin jam'iyar na jahar katsina, yayin da yake biyani makasudin zaman Shugaban Jam'iyar ADC Alhaji Musa Wamba yaci gaba dacewa wannan zama zamane wanda zaikara kawo hadin kai tsakanin Uwar Jam'iya da kuma Wa'inda s**a shigo watau Yan Hadaka (Coaliation) dan haka yazama wajibi uwar jam'iyar tarika wannan zaman lokaci bayan lokaci dan samun hadinkan Ya'yanta domin kuwa da wanda yashigo da wanda aka iske duk daya suke babu wanda yafi wani
Shima anashi Jawabin Sanata Sadiq Yar'adu yajinjinama Uwar Jam'iyar ADC karkashin shugabanta Alhaji Usman Wamba akan irin wannan taron hadin kan domin dashi ne kowa zai fahimci kowa a hadu ayi aiki tare akumayi nasara tare wadda ita ake fata, Sanata Yar'adua Yakara dacewa muddum ya'yan Jam'iyar zasu hada kansu wuri daya to babu wanda zai iya farraqasu daga karshe yayi kira da a rika wannan zaman lokaci bayan lokaci
Shima Dr Mustapha M Inuwa yatofa albarkacin bakinsa inda yaci gaba dacewa Tsarin da jam'iyar ADC take dashi tsarine wanda kowane Danta zai samu yanci dan haka mucire tinanin sai mutum yazama zansamu mubarma Allah kawai shi zaiji da komai domin shi kadai ne keyi bawa ba abunda zaimaka
Dr Mustapha yakara dacewa Uwar Jam'iyar ADC tana kokari matuka musamman wurin kokarin ganin hadakan ya'yanta daga karshe yayi addua neman Nasara ga Allah S.W.A
Anas Sulaimain Kbai
CEO Triple H Multimedia
Click here to claim your Sponsored Listing.