SkillNet
28/04/2026
Menene “Future Opportunities”?
“Future Opportunities” na nufin damar da za
'a samu idan akayi la'akari da Yadda zamani yake tafiya a nan gaba, musamman a fannin fasaha, kasuwanci, da rayuwa gaba ɗaya.
👉 A sauƙaƙe:
Future Opportunities = damar da zaka iya anfani da su domin samun ci gaba a gaba
🚀 Misalan Future Opportunities:
🔹 Artificial Intelligence (AI):
Amfani da fasahar kamar wajen aiki, kasuwanci da koyarwa.
🔹 Cybersecurity:
Yayin da duniya ke zama digital, buƙatar kare bayanai na ƙaruwa sosai.
🔹 Web & App Development:
Ƙirƙirar websites da apps na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗi a gaba.
🔹 Digital Marketing:
Tallata kasuwanci ta internet (Facebook, TikTok, da sauransu).
🔹 Remote Jobs:
Aiki daga gida ga kamfanoni na duniya ta hanyar internet.
👉 Me ya kamata ka yi?
Ka fara koyon sabbin skills tun yanzu
Ka kasance mai bin sabbin abubuwa
Ka yi amfani da damar internet
👉 A takaice:
Wanda ya gane damammakin da za'a samu gobe tun yau, shi ne zai fi samun nasara.
✍️ Created by SkillNet | 2026
🚀
28/04/2026
Menene IoT (Internet of Things), kuma wanene asalin sa?
IoT (Internet of Things) yana nufin haɗa na’urori daban-daban da internet domin su riƙa sadarwa da juna ba tare da mutum ya sa baki kai tsaye ba.
👉 A sauƙaƙe:
IoT = na’urori + internet + sadarwa kai tsaye
Misalai:
- Smart TV
- Smart bulb (fitila mai amfani da internet)
- Smart watch
- CCTV da ake duba daga waya
- Motoci masu amfani da sensors
Waɗannan duk suna iya aikawa da karɓar bayanai ta internet.
---
⚙️ Yaya IoT ke aiki?
Na’ura tana da sensors → tana tattara bayanai → ta tura su ta internet → wani system ya sarrafa → a ba da sakamako ko umarni.
---
👤 Wanene asalin IoT?
An fara amfani da kalmar IoT ne a shekarar 1999 daga , wanda ya bayyana yadda na’urori za su riƙa haɗuwa da internet domin aiki tare.
✍️ Created by SkillNet | 2026
🌐
26/04/2026
Wane shiri ya kamata ka yi domin fasahar da ke zuwa nan gaba?
Duniya na saurin canzawa, kuma fasaha na ci gaba da sabuntawa kullum. Idan mutum bai shirya ba, zai iya zama baya cikin lokaci.
👉 Ga wasu muhimman abubuwan da ya kamata ka fara yi tun yanzu:
🔹 Koyi sabbin ƙwarewa (Digital Skills):
Ka fara koyon abubuwa kamar programming, cybersecurity, ko amfani da AI. Misali amfani da zai taimaka maka fahimtar yadda AI ke aiki.
🔹 Kasance mai koyo kullum:
Fasaha ba ta tsaya—saboda haka ka riƙa koyon sababbin abubuwa a kai a kai.
🔹 Ka fahimci internet da manhajoji:
Ba amfani kawai ba—ka fahimci yadda suke aiki a bayan fage.
🔹 Ka kula da tsaro (Cybersecurity):
Yayin da fasaha ke ƙaruwa, haɗari ma na ƙaruwa. Ka koyi yadda zaka kare bayananka.
🔹 Ka fara amfani da damar online:
Kasuwanci, ilimi, da samun kuɗi yanzu suna kan internet—ka shiga ka koyi yadda ake anfani da su.
🔹 Ka kasance mai tunani mai buɗe ido:
Sabbin abubuwa za su zo, ka kasance mai karɓa da sauƙin sabawa.
---
👉 A takaice:
Wanda ya shirya yau, shi ne zai yi nasara gobe.
🚀
25/04/2026
Menene amfanin sanya waya a Flight Mode? ✈️
Flight Mode (Airplane Mode) wani yanayi ne da ke kashe duk hanyoyin sadarwa na waya kamar network, Wi-Fi, da Bluetooth na ɗan lokaci.
👉 Ga amfanin sa:
🔹 1. Ajiye batir 🔋
Yana rage amfani da battery domin waya ba ta neman signal ko internet.
🔹 2. Hana kira da saƙonni 📵
Idan kana son nutsuwa ko barci, Flight Mode zai katse duk wani kira ko notification.
🔹 3. Saurin caji ⚡
Wayarka na caji da sauri idan babu abubuwan da ke amfani da network.
🔹 4. Gyara matsalar network 📶
Idan signal ya yi rauni, kunna Flight Mode na ɗan lokaci sannan ka kashe shi na iya dawo da network.
🔹 5. Tsaro a jirgin sama ✈️
An fi amfani da shi a jirgi domin hana waya ta tsoma baki da tsarin sadarwar jirgin.
👉 A takaice: Flight Mode yana ba ka iko ka kashe duk wata sadarwa na ɗan lokaci domin sauƙi, tsaro, da rage amfani da batir.
📱
22/04/2026
Ire-iren Software (Manhajoji)
Software ba iri ɗaya ba ne—akwai nau’o’i daban-daban, kowanne da aikin sa na musamman.
👉 Ga manyan nau’o’in software tare da misalai:
🔹 1. Application Software (Manhajojin Amfani):
Waɗannan su ne apps da muke amfani da su a kullum domin ayyuka daban-daban.
Misalai: (saƙonni), (sadarwa), (binciken yanar gizo), (rubutu).
🔹 2. System Software (Manhajar Tsari):
Wannan shi ne ke sarrafa gaba ɗaya na’ura kuma ba tare da shi ba komai ba zai yiwu ba.
Misalai: , Android, da iOS—su ne ke ba waya ko kwamfuta damar aiki.
🔹 3. Programming Software (Manhajar Ƙirƙira):
Waɗannan su ne kayan aikin da masu coding ke amfani da su wajen gina apps da software.
Misalai: , PyCharm, da Notepad++.
🔹 4. Utility Software (Manhajar Kula da Na’ura):
Ana amfani da su domin gyara, tsabtacewa, da kuma kare na’ura daga matsaloli.
Misalai: Antivirus apps, CCleaner, da Disk Cleanup.
---
👉 Misalin yadda suke aiki tare (APP):
Misali, idan kana amfani da :
- Android ko iOS (System Software) ne ke tafiyar da wayarka
- (Application Software) shi kake amfani da shi wajen tura saƙo
- Internet da server suna taimaka masa ya aika saƙo
- Wasu Utility apps suna kare wayarka daga cuta
👉 Wannan yana nuna cewa duk waɗannan nau’o’i suna aiki tare domin app ɗaya ya yi aiki yadda ya kamata.
---
👉 A takaice:
- Application → abin da kake amfani da shi kai tsaye
- System → abin da ke tafiyar da na’ura
- Programming → abin da ake amfani da shi wajen ƙirƙira
- Utility → abin da ke kula da lafiyar na’ura
Idan ka fahimci wannan, zaka fara ganin yadda fasaha ke aiki a zahiri.
💻
22/04/2026
Menene Software? (Manhaja)
Software wani ɓangare ne na kwamfuta ko waya da ba a iya taɓawa da hannu ba, amma shi ne ke ba na’ura umarni ta yadda za ta yi aiki.
A sauƙaƙe, software shi ne “hankalin” na’ura—shi ke gaya mata abin da za ta yi da yadda za ta yi.
Misali, duk wani app da kake amfani da shi a waya kamar. WhatsApp app, Facebook, Chrome, da Call app, duk software ne. Haka kuma Programming ne suma software ne.
Idan ba tare da software ba, waya ko kwamfuta ba za ta iya aiki ba, domin babu abin da zai sarrafa ta.
👉 A takaice:
Hardware shine jiki, software kuwa shine ruhin da ke sa ta yi aiki.
Ku ku biyo mu a post na gaba domin sanin ire-iren Software wato Manhaja.
💻
21/04/2026
Wannan Dama ce kwarai da gaske musamman ga matasan mu maza da mata.
SkillNet ta zama duniyar Digital Knowledge.
Makarantar Digi-Master Hub Academy tare da Haɗin guiwar Kamfanin Virex Network Solution Sun Hadu sun bude Sabon shafi mai suna SkillNet.
Suna dora dukkan abubuwan da zasu canza tunani.
Follow SkillNet on Facebook 🔗 Link 👇👇👇👇
21/04/2026
Yaya aka gano Internet har ya zama abokin rayuwar jama’a?
Internet bai zo kwatsam ba—ya samo asali ne daga bincike da ƙoƙarin haɗa kwamfutoci su riƙa sadarwa da juna.
A shekarun 1960s, wata ƙungiya a Amurka mai suna ta fara wani aiki domin ƙirƙirar hanyar sadarwa tsakanin kwamfutoci. Wannan ya haifar da tsarin da ake kira —shi ne asalin internet na farko.
Daga baya, masana kamar da s**a ƙirƙiri tsarin da ake kira TCP/IP, wanda ya ba kwamfutoci damar sadarwa cikin tsari ɗaya. Wannan ne ya zama ginshiƙin internet na zamani.
A shekarar 1989 kuma, ya ƙirƙiri World Wide Web (WWW), wanda ya ba da damar buɗe shafukan yanar gizo (websites) cikin sauƙi—nan ne mutane s**a fara amfani da internet sosai.
Tun daga wannan lokaci, internet ya bunƙasa har ya zama wani ɓangare na rayuwar yau da kullum—daga sadarwa, kasuwanci, ilimi, zuwa nishadi.
A yau, internet ba kawai fasaha ba ce—ya zama kamar “rayuwa a hannu”, domin kusan komai yana tafiya a kansa.
🌐
21/04/2026
📯 SkillNet
Cikakken bayani game da CCTV da yadda take aiki
CCTV (Closed-Circuit Television) wata kyamara ce ta tsaro da ake amfani da ita domin kula da wurare kamar gida, shago, ofis ko tituna. Ba kamar TV na yau da kullum ba, ita CCTV tana aika hotuna ne zuwa wuri na musamman domin sa ido.
A sauƙaƙe, yadda take aiki shi ne: kyamara tana ɗaukar bidiyo → ta tura shi zuwa na’urar ajiya (DVR ko NVR) → sannan a kalla a kan allo ko a waya. A wasu lokuta ma ana iya adana bidiyon a cloud domin a duba daga ko’ina.
Babban abin da ya sa mutane ke amfani da CCTV shi ne tsaro. Tana taimakawa hana sata, gano masu laifi, da kuma kula da abin da ke faruwa ko da ba ka wurin. A yau ma, ana iya haɗa ta da internet, ka dinga dubawa kai tsaye daga wayarka ko da kana nesa.
Sai dai kuma, tana da wasu ƙalubale—kamar bukatar wuta, ajiyar bayanai, da kuma yiwuwar kutse idan ba a tsare ta da kyau ba.
A takaice, CCTV kamar ido ne na biyu—yana baka damar ganin abin da ba ka gani a kowane lokaci.
🔐🎥
20/04/2026
Wanne ne ya fara tunanin kirkirar manhaja (software)?
Ba mutum guda ne ya fara tunanin “manhaja ba” kamar yadda muke amfani da ita a yau , amma akwai wasu manyan mutane a tarihin fasaha da s**a kafa ginshiƙin wannan fasahar daga farko.
👉 Mafi farko a tarihi, Ada Lovelace ita ake ɗauka a matsayin mutum na farko da ya fara tunanin “programming” a duniya.
Ta yi aiki tare da na’urar farko mai suna Analytical Engine wacce Charles Babbage ya tsara. Ada Lovelace ta rubuta umarnin yadda na’urar za ta yi lissafi—wannan shi ne abin da ake ɗauka a matsayin farkon “software” a tarihi.
👉 Daga baya kuma: Alan Turing ya ƙara zurfafa wannan tunani, inda ya kafa ginshiƙan computer science na zamani da yadda kwamfuta ke aiki da umarni (algorithms).
⚙️ A takaice:
Ada Lovelace → ta kafa turken farkon na tunanin yadda programming yake.
Charles Babbage → Wanda ya girka injin kwamfutana farko.
Alan Turing → Wanda ya samar da ginshiƙin kwamfuta ta zamani.
👉 Saboda haka, manhaja (software) ba ta fito kwatsam ba—ta samo asali ne daga tunani, lissafi, injiniyoyi, bisa umarnin kwamfuta.
💻
Click here to claim your Sponsored Listing.
Website
Address
Kano
730101