Fatima Labarina

Fatima Labarina

Share

Photos from Fatima Labarina's post 17/05/2026

Ya Allah kai mana arzikin cikawa da imani Amin ✨🥰❤️🤲

Photos from Fatima Labarina's post 17/05/2026

____📸✌️

17/05/2026

Ku bani shawara masoyana ❤️‍🩹🥰💞👇

17/05/2026

Wani mutum y binne Kare a maƙabartar musulmai.

Mutane s**a kai ƙara wajen Alƙali. Alƙali ya ce, da gaske ne abin da ake tuhumarka da shi..!!??

Mai Kare ya ce, ƙwarai ma kuwa (Allah y ƙara maka Imani), shi Karen ne ya yi wasiyya ya ce a binne shi a nan...!!

Alƙali ya ce, Izgili za ka yi mini?

Mai Kare ya ce, Allah ya kyautata aikin Malam! Ba izgili na ke yi maka ba, domn kafin marigayi ya cika ya sake yi mini wasiyya da a baka dirhami 1000.

Cikin hawaye Alƙali ya ce, Allahu Akbar, Allah ya ji ƙan marigayi.

Mutane s**a yi mamakin yadda Alƙali ya canza lokaci ɗaya.

Alƙali ya ce, kar ku yi mamaki, bincike ne ya tabbatar da cewa marigayi yana da nagarta sosai kuma yana da kirki, sannan kuma yana daga cikin jikokin Karnukan "As'habul Kahfi"...!!!

Photos from Khadija Mai Numfashi's post 17/05/2026
16/05/2026

Kada kayi sakaci wurin addu'a. Ka roƙi Allah duk abinda kake buƙata domin Shi ke da komai.

Ya Allah ka biya mana buqatun mu na alkairi Amin🙏🤲

Photos from Fatima Labarina's post 16/05/2026

Hama 😂😄

Photos from Fatima Labarina's post 15/05/2026

Ya Allah kasa Muzama Mabudin Alkhairi Ga Mutane, Mukuma zama Sanyin Idanuwa Ga Masoyan Mu dan Falalar Wannan Rana Ta Juma’a.

Juma’at Mubarak🖤

🕋🕌🙏

15/05/2026

Babbar ni’imar da allah yayi muna wadda muke gode masa akanta a koh wanne lokaci bata wuce kasancewar mu a musulmai bah 😩❤️

Ya allah ka amshi rayuwarmu muna musulmai 🌙✨🤲🏿

15/05/2026

DON ALLAH A MATSAYINKA NA MATASHI KA KULA DA WAƊANNAN ABUBUWAN A RAYUWARKA.

Kuruciya gajeruwar riga ce wacce take yaudarar kwakwalwar matasa da yawa. A yanzu kana ganin jinin jikinka yana da zafi, kana ganin kamar kana da isasshen lokacin da zaka yi wasa yau ka nemi arziki gobe. Wallahi abun ba haka bane Abin da ka shuka a 20s dinka, shi zaka girba a 30s zuwa 40s har tsufa.

Kafin ka gama cinye asalin jarin kuruciyarka a wajen burge abokan banza, don Allah ka rike wadannan abubuwa guda 4 da kyau:

1. Lafiyarka:
Jikinka shi ne asalin ofishinka da jarinka na farko. Daina lalata lafiyarka da shaye-shaye, ko yawan kwana kana latsa waya baka barci mai kyau. Randa koshin lafiyarka ya lalace, duk wani burin arziki da kake da shi ya zama tamkar iska.

2. Neman Kuɗin Ka:
Ka Daina mika kokon baran neman taimako wajen 'yan uwa ko 'yan siyasa. Fafutukar neman na halas dinka komai kankantarsa, shi zai baka 'yancin fada a ji a gaban kowa. Gumin kuruciya yana hana hawayen tsufa.

3. Neman Ilimi:
Ba ina nufin takardar Digiri kawai ba; ina nufin Ilimin addini da ilimin da zai sa ka san yadda ake juya kudi da karkato da hankalin jama'a. Koyi sabbin sana'o'i na zamani. Kwakwalwar da bata karatu ko koyon sabon abu, gidan gizo-gizo ne zai cika ta.

4. Ibada:
Babban kuskuren matasa shine tunanin cewa ibada ta tsofaffi ce. Ka sani cewa idan baka gina kyakkyawar alaka da Mahaliccinka a lokacin da kake da karfi ba, Allah zai bar ka da wayonka a lokacin da kake neman budi a kasuwancinka.

Ina son ku sani idan babu wadannan abubuwan a rayuwarka... wallahi tsufa zai zo maka da wulakanci, talauci, da kuma nadamar da babu wanda zai iya goge maka ita. Ka Tashi ka gyara gobenka tun yau.

Allah yasa mudace🤲🏻🤲🏻🤲🏻
Ina kaunar ku Masoyana 🥰🥰🙏🏻

15/05/2026

Ya Allah kaci gaba da faranta mana muda masu kaunar mu dan alfarmar Annabi MUHAMMADU S.AW Amin✨❤️🤲

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address

287 Fulton Street
Kano
10007