Hon Hassan Cikinza Rano

Hon Hassan Cikinza Rano

Share

21/11/2025

Dalilin da yasa Shugaba Tinubu ya zaɓi Matawalle don jagorantar magance matsalar sace ’yan matan Kebbi

Dr. Bello Matawalle baya sanya kayan soja, amma abu guda da baza a iya musanta masa ba shi ne zurfin fahimtarsa game da matsalolin tsaro a Najeriya—musamman a Arewa maso Yamma, inda ’yan fashi da makami da garkuwa da mutane s**a daɗe suna azabtar da al’umma. Don haka, lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci karamin Ministan Harkokin Tsaro ya koma Jihar Kebbi domin jagorantar aikin ceto ’yan matan da aka sace, ba alama ce kawai ba. Zabe ne na dabara, bisa ƙwarewa, gogewa, da sanin da ba kasafai ake samu ba na yankin da halayensa. Da dama ba sa fahimtar cewa naɗin Dr. Matawalle a matsayin ƙaramin Ministan Harkokin Tsaro ya fito ne daga kyakkyawan tarihin bajintarsa.

A matsayinsa na Gwamnan Zamfara, Dr. Matawalle ya kafa tarihi wajen fuskantar ’yan bindiga ta hanyar haɗa tsattsauran mataki da kuma tattaunawar dabaru. Ya taɓa faɗa a bainar jama’a cewa a zamaninsa, Zamfara ta yi fiye da shekara guda ba tare da ko harin ’yan bindiga ba—nasara da ba ta zo da sauƙi ba, illa dai saboda ingantacciyar dabarar da ta dawo da zaman lafiya a jihar.

Ƙoƙarinsa ba su tsaya ga hana hare-hare ba; sun haɗa har da ceto mutanen da aka sace—aikin da ake bukatar ya sake jagoranta yau. A 2020, ta hanyar Zamfara Peace Initiative, ya samar da sakin mutum 11 da aka yi garkuwa da su ba tare da an biya kudin fansa ba. Zuwa Yuni 2022, gwamnatin Zamfara ta sanar da cewa sama da mutum 3,000 da aka sace an ceto su daga Satumba 2019 zuwa Janairu 2022. Wannan ya haɗa da ɗalibai, mata, da maza daga sassa daban-daban. Manyan ayyukan ceto sun faru ne a dajin Gando—daya daga cikin manyan mafakar miyagun kungiyoyi a yankin. Sanin Matawalle game da yankin da kuma haɗin gwiwarsa da jami’an tsaro ya taka rawar gani wajen gano maboyar miyagun, korarsu, da kuma dawo da fursunonin gida.

Sannan fahimtarsa ta wuce kan iyakokin Najeriya. Da amincewar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, ya kai ziyartar tsaro sau da dama zuwa birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar, inda ya gana da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, kan hadin gwiwa, tsaron iyaka, da dakile shigowar mak**ai masu haɗari zuwa Arewa maso Yamma. Kaɗan ne daga cikin shugabannin yankin da ke da irin wannan ƙwarewar tsaro ta ƙetare ƙasa.

Karfin Matawalle ba na rubutu ba ne—na aiki ne. Yana da fahimtar halayen jama’ar Arewa maso Yamma: al’adu, dangantaka, ginshikan kabilu, tsarin girmamawa, da kuma haɗaɗɗen yanayin koke-koken al’umma, damuwar rayuwa, da ta’addancin da ke haifar da matsalar tsaro. Aiki irin na tattaunawa da masu garkuwa da mutane don ceton fursunoni ba ya bukatar iko kawai; yana bukatar amincewa, haƙuri, kwarjini, da sanin yanayi wanda ba a koya shi a aji. Dr. Matawalle ya sha nuna cewa yana da waɗannan dukkanin siffofin.

Mai yiwuwa mafi shaida ga ƙwarewarsa shi ne abin da ya faru a 2021, lokacin da aka sace fiye da ɗalibai 300 a Kankara, Jihar Katsina. Shi ne Shugaba Buhari ya kira kai tsaye. Kuma shi ne ya jagoranci cetonsu—kowa-da-kowa—ba tare da an harba ko harsashi guda ɗaya ba, ba tare da an biya kudin fansa ba.

Wannan shi ne dalilin da ya sa matsalar Kebbi ta zarce tura sojoji kawai. Tana bukatar wanda ya san halayen masu laifin, wanda zai iya shiga kananan hanyoyi masu sarkakiya, kuma ya san yadda ake juya bayanan sirri zuwa sak**ako ba tare da tayar da jijiyar wuya ba. Shawarar Shugaba Tinubu na tura Matawalle Kebbi ta nuna haske: ya san wanda ya fi dacewa da wannan aiki.

Dr. Matawalle ɗan asalin yankin Arewa maso Yamma ne ta kowace fuska. Rayuwa ta gina shi, ya san dukkan sassan yankin, kuma ana girmama shi ko a cikin wuraren da ba sa bin tsarin gwamnati. A irin wannan lokaci, irin wannan ilimi ya zama makami mai ƙarfi k**ar bindiga ko dabarun soja.

Sai dai aikin da yake gabansa yana da matuƙar nauyi, sarkakiya, kuma gaggawa. Amma ga ’yan matan Kebbi da aka sace—wadanda ake tsare da su cikin tsoro da mawuyacin hali— akwai fata domin an mika al’amarin ga wanda ya taɓa yin hakan sau da dama.

Domin su, da kuma domin ƙasarmu, muna fatan wannan hukunci zai haifar da sak**akon da kowa ke so: dawowar su lafiya, cikin gaggawa.

— Dahiru Bashir Hassan, mai bincike kan harkokin tsaro, daga Abuja.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address

Kano