MMB FARM
🐐 KIWON AKUYA – JARI MAI RIBA 🐐
Kiwon akuya sana’a ce ta kasuwanci wadda ke bada riba cikin lokaci kaɗan. Akuya na saurin hayayyafa, ba ta bukatar tsada mai yawa, kuma kasuwarta tana tafiya a kowane lokaci.
🔹 Ƙananan jarin farawa
🔹 Babbar riba cikin lokaci
🔹 Kasuwa a shirye (nama, madara, bukukuwa)
🔹 Sauƙin kiwo da kulawa
Kiwon akuya ya dace da masu ƙananan jari da manyan masu saka hannun jari. Da tsari mai kyau da kulawa, kiwo na iya zama tabbatacciyar hanyar samun kudin shiga.
Daga akuya ɗaya, za ka iya gina garken da zai zama babban jari a gaba. Ka fara da kaɗan, ka dage da haƙuri, riba za ta zo.
Kiwo, hanyar dogaro da kai ce. 💪🐐
01/05/2025
Wutar daji na ci gaba da ruruwa a Isra'ila.
Masana sun ce wutar dajin ita ce mafi muni da Isra'ila ke fuskanta inda tuni ta tilasta sanya dokar ta ɓaci a ƙasar tare da neman agajin ƙasashe, bayan da bayanai ke cewa ana kuma fuskantar iska mai gudun mil 60 a cikin sa'a guda da ke kaɗawa a yankin da ake fama da wutar dajin cike da barazanar fantsama wutar zuwa wasu sassan dajin.
In dai ba a manta ba kusan watanni biyu ke nan da makamanciyar wannan wuta ta babbake birnin Les angles na Amurka, wanda ya haifar masu da assarar miliyoyin kudade har manda sarar rayukan dabbobi da na mutane.
Me kuke tunanin yana yawan kawo wadannan yankuna na turawa irin wannan wautar daji a dan tsakanin nan
Click here to claim your Sponsored Listing.