WAKOKIN HAUSA RUBUTATTU

WAKOKIN HAUSA RUBUTATTU

Share

12/10/2022

KA CIYAR A CISHE KA
Daga: Nasiru G. Ahmad

Yawan ba da khairi arziƙinka yana daɗo,
Yawan naɗe hannu aibu ne ba shi kyautuwa.

Matse hannuwa bai sa wadata ta dawwama,
Ka zam basuwa in Rabbi ya ba ka ɗan uwa.

Bahili marowanci a kul ka zamo ka shi,
Ka ba mabuƙaci in ya zo ma da damuwa.

Talauci ka bar tsoron sa don ka yi kyautayi,
Ka san arziƙi Allah kaɗai shi ka basuwa.

Allah ne ya cancanci a tsoraci je masa,
Da hali na rowa don garai ba shi karɓuwar.

Ka san arziƙi yau gunka ne gobe gun wani,
Ka bayar a yau gobe ga kai za a basuwa.

A don haka in mai damuwa ya taho maka,
Ka bar ɗaure fuska ko batu mai tsanantuwa.

Ka san mawadaci mai yawan ba da taimako,
Abin son mutane har du'a'i suna yiwa.

Amma mawadaci wanda bai taimakon wani,
Kamar matsiyaci ne abin ƙi da ƙyamuwa.

A ya Rabbi ba mu arziƙi mai tabarraki,
Mu ci mu yi bayarwa gare ka mu bautuwa.

Muhammadu Nasir Ahmadu ya yi baitukan,
Cikin Hausa don ni har da ku mui faɗakkuwa.

17/08/2022

ADALCI GADON BARCI
Daga
Nasiru G. Ahmad

Kisra sarki na Farisa ya,
Ziyarci Madina yai jewa.

Amirul Muminina Umar,
Ya je domin su ganawa.

Bai iske fankacen bene,
Na sarki har da fadawa.

Domin haka nan ya saba gani,
Sarakan Fursu na yiwa.

Ya tambayi shin ina fadar,
Sarki Umar mu ganawa?

An ce ya wuce masallaci,
Yana can ya yi kwantawa.

Ya iske shi bisa rairai,
Yana barci da juyawa.

Bai iske masu gadi ba,
Tsumman riga ya ɗaurawa.

Mamaki ya cika masa rai,
Da tsoro har da ruɗewa!

Wannan shi ne ya cinye su,
Da yaƙi bai yi janyewa.

Sai al'amarin sarakansu,
Na girman kai da holewa,

Ya zam a idonsa shirme ne,
Domin ƙarshensa taɓewa.

Ya dubi Umar ya ce lallai,
Ka yo barci tsanakewa.

Ba tsoron kar a shammace,
Ka sharri gunka ai yowa.

Domin ka tsai da adalci,
Talakka ba ka cutarwa.

Halifan Ɗaha ya Umar,
Ka zarta sa'a ga kyautawa.

Tutar adalci ka yi ɗaga,
Dimkuraɗiyya abar sowa.

Allahu ya kyauta kwancinka,
Cikin rahama da yarjewa.

Salati da sallama izuwa,
Rasulu ba za mu dainawa.

Nasir Ahmad ya tsaro ta,
Ga mu domin tunatarwa.

17 ga Agusta, 2022

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Zoo Road
Kano