Dharul Islam
29/04/2026
Darasi na uku acikin littafin Kitabut tauhid 03:
بسم الله الرحمن الرحيم
بَابُ مَنْ حَقَّقَ التَّوْحِيدَ دَخَلَ الْجَنَّةَ بِغَيْرِ حِسَابٍ
Babin dake magana kan wanda ya tabbatar da Tauhidi (ya tsarkake shi) zai shiga Aljanna ba tare da hisabi ba.
وَقَوْلُ اللهِ تَعَالَى: {إِنَّ إِبْرَاهِيمَ كَانَ أُمَّةً قَانِتًا لِلَّهِ حَنِيفًا وَلَمْ يَكُ مِنَ الْمُشْرِكِينَ}
Kuma fadar Allah Madaukakin Sarki: "Lallai Annabi Ibrahim ya kasance jagora (abin koyi), mai kankan da kai ga Allah, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga cikin mushirikai ba."
وَقَالَ: {وَالَّذِينَ هُمْ بِرَبِّهِمْ لَا يُشْرِكُونَ}
Kuma (Allah) ya ce: "Kuma wadanda su ne, ba sa hada Ubangijinsu da kowa (ba sa yin shirka)."
عَنْ حُصَيْنِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ قَالَ: كُنْتُ عِنْدَ سَعِيدِ بْنِ جُبَيْرٍ فَقَالَ: أَيُّكُمْ رَأَى الْكَوْكَبَ الَّذِي انْقَضَّ الْبَارِحَةَ؟
Daga Husain dan Abdurrahman ya ce: Na kasance a wurin Sa’id dan Jubair, sai ya ce: "Wane ne a cikinku ya ga tauraron da ya fado jiya da daddare?"
فَقُلْتُ: أَنَا، ثُمَّ قُلْتُ: أَمَا إِنِّي لَمْ أَكُنْ فِي صَلَاةٍ، وَلَكِنِّي لُدِغْتُ.
Sai na ce: "Ni ne," sannan na ce: "Amma dai (ina so ku sani) ba wai ina sallah ba ne (shiyasa na gani), sai dai wani abu ne ya harbe ni."
قَالَ: فَمَا صَنَعْتَ؟ قُلْتُ: ارْتَقَيْتُ. قَالَ: فَمَا حَمَلَكَ عَلَى ذَلِكَ؟
Ya ce: "To me ka yi?" Na ce: "Na nemi a yi mini rukya." Ya ce: "Me ya sa ka yi hakan (wane dalili kake da shi)?"
قُلْتُ: حَدِيثٌ حَدَّثَنَاهُ الشَّعْبِيُّ. قَالَ: وَمَا حَدَّثَكُمْ؟
Na ce: Wani hadisi ne da Ash-sha’abi ya ba mu labari. Ya ce: "Me ya ba ku labari?"
قُلْتُ: حَدَّثَنَا عَنْ بُرَيْدَةَ بْنِ الْحُصَيْبِ أَنَّهُ قَالَ: (لَا رُقْيَةَ إِلَّا مِنْ عَيْنٍ أَوْ حُمَةٍ).
Na ce: Ya ba mu labari daga Buraida dan Al-Husayb cewa ya ce: "Babu rukya (mafi amfani) sai don ta kambun ido da kambun baka (muguwar magana) ko kuma harbin wani abu mai dafi."
قَالَ: قَدْ أَحْسَنَ مَنْ انْتَهَى إِلَى مَا سَمِعَ، وَلَكِنْ حَدَّثَنَا ابْنُ عَبَّاسٍ عَنِ النَّبِيِّ ﷺ أَنَّهُ قَالَ:
Ya ce: "Lallai wanda ya tsaya ga abin da ya ji (na ilimi) ya kyauta. Sai dai Ibn Abbas ya ba mu labari daga Annabi SAW cewa ya ce:"
عُرِضَتْ عَلَيَّ الْأُمَمُ، فَرَأَيْتُ النَّبِيَّ وَمَعَهُ الرُّهَيْطُ، وَالنَّبِيَّ وَمَعَهُ الرَّجُلُ وَالرَّجُلَانِ، وَالنَّبِيَّ وَلَيْسَ مَعَهُ أَحَدٌ.
"An nuna mini al'ummomi; sai na ga wani Annabi yana tare da wasu mutane kalilan (ba su kai goma ba), da wani Annabi tare da mutum daya ko biyu, da ma wani Annabin da babu kowa tare da shi."
إِذْ رُفِعَ لِي سَوَادٌ عَظِيمٌ فَظَنَنْتُ أَنَّهُمْ أُمَّتِي، فَقِيلَ لِي: هَذَا مُوسَى وَقَوْمُهُ.
"Kwatsam sai aka ɗaga mini wani babban taron (mutane da yawa), sai na zata al'ummata ce, sai aka ce mini: 'Wannan Musa ne da mutanensa'."
فَنَظَرْتُ فَإِذَا سَوَادٌ عَظِيمٌ، فَقِيلَ لِي: هَذِهِ أُمَّتُكَ، وَمَعَهُمْ سَبْعُونَ أَلْفًا يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ بِغَيْرِ حِسَابٍ وَلَا عَذَابٍ.
"Sai na sake dubawa sai na ga wani babban taro mai yawan gaske, sai aka ce mini: 'Wannan ita ce al'ummarka, kuma tare da su akwai mutum dubu saba'in (70,000) da za su shiga Aljanna ba tare da hisabi ba, kuma ba tare da azaba ba'."
ثُمَّ نَهَضَ فَدَخَلَ مَنْزِلَهُ، فَخَاضَ النَّاسُ فِي أُولَئِكَ، فَقَالَ بَعْضُهُمْ: فَلَعَلَّهُمْ الَّذِينَ صَحِبُوا رَسُولَ اللهِ ﷺ.
Sannan (Annabi) ya tashi ya shiga gidansa. Sai mutane s**a shiga tattaunawa a kan wadannan mutanen (dubu saba'in ɗin). Wasu s**a ce: "Wataƙila su ne waɗanda s**a yi abota da Manzon Allah SAW."
وَقَالَ بَعْضُهُمْ: فَلَعَلَّهُمْ الَّذِينَ وُلِدُوا فِي الْإِسْلَامِ فَلَمْ يُشْرِكُوا بِاللهِ شَيْئًا.
Wasu kuma s**a ce: "Wataƙila su ne waɗanda aka haifa a cikin Musulunci kuma ba su taɓa yin shirka da Allah ba."
فَخَرَجَ عَلَيْهِمْ رَسُولُ اللهِ ﷺ فَأَخْبَرُوهُ فَقَالَ: هُمُ الَّذِينَ لَا يَسْتَرْقُونَ، وَلَا يَكْتَوُونَ، وَلَا يَتَطَيَّرُونَ، وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ.
Sai Manzon Allah SAW ya fito gare su, s**a gaya masa (abun da suke tattaunawa), sai ya ce: "Su ne waɗanda:
Ba sa neman a yi musu rukya (domin tsantsar tawakkali).
Ba sa yin Tsakiya da wuta (ƙuna).
Ba sa yin camfi.
Kuma ga Ubangijinsu ne kaɗai suke dogara.
فَقَامَ عُكَّاشَةُ بْنُ مِحْصَنٍ فَقَالَ: ادْعُ اللهَ أَنْ يَجْعَلَنِي مِنْهُمْ، فَقَالَ: أَنْتَ مِنْهُمْ.
Sai Ukasha dan Mihsan ya tashi ya ce: "Ka roƙar mini Allah ya sanya ni daga cikinsu." Sai Annabi ya ce: "Kana daga cikinsu."
ثُمَّ قَامَ رَجُلٌ آخَرُ فَقَالَ: ادْعُ اللهَ أَنْ يَجْعَلَنِي مِنْهُمْ، فَقَالَ: سَبَقَكَ بِهَا عُكَّاشَةُ.
Sannan wani mutumin ya tashi ya ce: "Ka roƙar mini Allah ya sanya ni daga cikinsu." Sai ya ce: "Ukasha ya riga ka."
فِيْهِ الْمَسَائِل
(Akwai Mas'alolin da ke cikin babin):
الأُولَى: مَعْرِفَةُ مَرَاتِبِ النَّاسِ فِي التَّوْحِيدِ.
Na ɗaya:Sanin matsayin mutane mabambanta a kan Tauhidi.
الثَّانِيَةُ: مَا مَعْنَى تَحْقِيقِهِ.
Na biyu:Menene ma’anar "Tahqiq" (tabbatar da/tsarkake) Tauhidi.
الثَّالِثَةُ: ثَنَاؤُهُ سُبْحَانَهُ عَلَى إِبْرَاهِيمَ بِكَوْنِهِ لَمْ يَكُ مِنَ الْمُشْرِكِينَ.
Na uku:Yabon da Allah ya yi wa Annabi Ibrahim na cewa bai kasance daga cikin mushirikai ba.
الرَّابِعَةُ: ثَنَاؤُهُ عَلَى سَادَاتِ الْأَوْلِيَاءِ بِسَلَامَتِهِمْ مِنَ الشِّرْكِ.
Na huɗu:Yabon manyan bayin Allah kan kubutarsu daga shirka.
الْخَامِسَةُ: كَوْنُ تَرْكِ الرُّقْيَةِ وَالْكَيِّ مِنْ تَحْقِيقِ التَّوْحِيدِ.
Na biyar:Barin neman rukya da Yin tsakiya da wuta na daga cikar Tauhidi.
السَّادِسَةُ: كَوْنُ الْجَامِعِ لِتِلْكَ الْخِصَالِ هُوَ التَّوَكُّلُ.
Na shida:Kasancewar abin da ya tara waɗannan dabi’un shi ne dogara ga Allah Tawakkali.
السَّابِعَةُ: عُمْقُ عِلْمِ الصَّحَابَةِ بِمَعْرِفَتِهِمْ أَنَّهُمْ لَمْ يَنَالُوا ذَلِكَ إِلَّا بِعَمَلٍ.
Na bakwai:Zurfin ilimin Sahabbai da s**a gane cewa ba a samun wannan matsayi sai da aiki.
الثَّامِنَةُ: حِرْصُهُمْ عَلَى الْخَيْرِ.
Na takwas:Kwadayin Sahabbai wajen neman alheri.
التَّاسِعَةُ: فَضِيلَةُ هَذِهِ الْأُمَّةِ بِالْكَمِّيَّةِ وَالْكَيْفِيَّةِ.
Na Tara:Falalar wannan al'umma ta fuskar yawa da kuma inganci.
الْعَاشِرَةُ: فَضِيلَةُ أَصْحَابِ مُوسَى.
Na Goma:Falalar mabiyan Annabi Musa.
الْحَادِيَةَ عَشْرَةَ: عَرْضُ الْأُمَمِ عَلَيْهِ ﷺ.
Na sha daya:Nuna wa Annabi SAW dukkan al'ummomi.
الثَّانِيَةَ عَشْرَةَ: أَنَّ كُلَّ أُمَّةٍ تُحْشَرُ وَحْدَهَا مَعَ نَبِيِّهَا.
Na sha biyu:Kowace al’umma za a tashe ta ne tare da Annabinta.
الثَّالِثَةَ عَشْرَةَ: قِلَّةُ مَنِ اسْتَجَابَ لِلْأَنْبِيَاءِ.
Na sha uku: Ƙarancin mutanen da s**a amsa kiran Annabawa.
الرَّابِعَةَ عَشْرَةَ: أَنَّ مَنْ لَمْ يُجِبْهُ أَحَدٌ يَأْتِي وَحْدَهُ.
Na sha huɗu:Annabin da kowa bai bi shi ba, zai zo shi kaɗai ranar kiyama.
الْخَامِسَةَ عَشْرَةَ: ثَمْرَةُ هَذَا الْعِلْمِ وَهُوَ عَدَمُ الِاغْتِرَارِ بِالْكَثْرَةِ وَعَدَمُ الزُّهْدِ فِي الْقِلَّةِ.
Na sha biyar:Amfanin wannan ilimin shi ne: rashin ruɗuwa da yawa, da kuma rashin raina abu saboda ƙarancinsa.
السَّادِسَةَ عَشْرَةَ: الرُّخْصَةُ فِي الرُّقْيَةِ فِي الْعَيْنِ وَالْحُمَةِ.
Na sha shida: Sauƙi/Halaccin yin rukya saboda harbi ko mugun gani.
السَّابِعَةَ عَشْرَةَ: عُمْقُ عِلْمِ السَّلَفِ لِقَوْلِهِ (قَدْ أَحْسَنَ مَنِ انْتَهَى إِلَى مَا سَمِعَ).
Na sha bakwai:Zurfin ilimin magabata wajen faɗin cewa "wanda ya tsaya ga abin da ya ji ya kyauta".
الثَّامِنَةَ عَشْرَةَ: بُعْدُ السَّلَفِ عَنْ مَدْحِ الْإِنْسَانِ بِمَا لَيْسَ فِيهِ.
Na sha takwas:Nisantar magabata daga yabon mutum da abin da ba shi da shi.
التَّاسِعَةَ عَشْرَةَ: قَوْلُهُ (أَنْتَ مِنْهُمْ) عَلَمٌ مِنْ أَعْلَامِ النُّبُوَّةِ.
Na sha tara:Fadin Annabi "Kana cikinsu" wata babbar aya ce ta annabta (domin Ukasha ya mutu a kan haka).
الْعِشْرُونَ: فَضِيلَةُ عُكَّاشَةَ.
Na Ashirin:Falalar Ukasha (Allah ya yarda da shi).
الْحَادِيَةُ وَالْعِشْرُونَ: اسْتِعْمَالُ الْمَعَارِيضِ.
Na ashirin da daya:Yin amfani da hikima wajen magana don kauce wa abin da ba a so.
الثَّانِيَةُ وَالْعِشْرُونَ: حُسْنُ خُلُقِهِ ﷺ.
Na ashirin da biyu:Kyawun ɗabi'un Manzon Allah SAW.
والله أعلم.
Allah ne mafi sani.
Follow me for more share like comment 🙏✅
28/04/2026
Darasi na biyu acikin littafin Kitabut tauhid 02:
بسم الله الرحمن الرحيم
(Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai)
بَابُ فَضْلِ التَّوْحِيدِ وَمَا يُكَفِّرُ مِنَ الذُّنُوبِ
Babi dake magana a kan falalar Tauhidi da abubuwan da yake kankarewa na zunubai.
وَقَوْلُ اللهِ تَعَالَى: {الَّذِينَ آمَنُوا وَلَمْ يَلْبِسُوا إِيمَانَهُمْ بِظُلْمٍ}
Kuma fadar Allah Madaukakin Sarki: "Wadanda s**a yi imani, kuma ba su gauraya imaninsu da zalunci (shirka) ba."
عَنْ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ ﷺ:
Daga Ubada dan Samit ya ce: Manzon Allah SAW ya ce:
«مَنْ شَهِدَ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ»
"Duk wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai, ba shi da abokin tarayya,"
«وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ»
"Kuma lallai Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne,"
«وَأَنَّ عِيسَى عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ، وَكَلِمَتُهُ أَلْقَاهَا إِلَى مَرْيَمَ وَرُوحٌ مِنْهُ»
"Kuma lallai (Annabi) Isah bawan Allah ne kuma Manzonsa ne, kuma kalmarsa ce da ya jefa ta zuwa ga Maryam, kuma ruhi ne daga gare shi,"
«وَالْجَنَّةُ حَقٌّ وَالنَّارُ حَقٌّ، أَدْخَلَهُ اللهُ الْجَنَّةَ عَلَى مَا كَانَ مِنَ الْعَمَلِ»
"Kuma Aljanna gaskiya ce, wuta ma gaskiya ce, to Allah zai shigar da shi Aljanna a kan duk irin aikin da ya gabatar."
وَفِي حَدِيثِ عِتْبَانَ: «فَإِنَّ اللهَ حَرَّمَ عَلَى النَّارِ مَنْ قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ يَبْتَغِي بِذَلِكَ وَجْهَ اللهِ»
A cikin hadisin Utban: "Lallai Allah ya haramta wa wuta duk wanda ya ce 'Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah'kuma yana nufin neman yardar Allah da hakan."
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ عَنْ رَسُولُ اللهِ ﷺ قَالَ: قَالَ مُوسَى: يَا رَبِّ عَلِّمْنِي شَيْئًا أَذْكُرُكَ وَأَدْعُوكَ بِهِ.
Daga Abu Sa’idul-Khudri: Annabi Musa ya ce: Ya Ubangiji! Ka koya mini wani abu da zan rika ambatonka kuma in rika rokonka da shi.
قَالَ: قُلْ يَا مُوسَى لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ. قَالَ: يَا رَبِّ كُلُّ عِبَادِكَ يَقُولُونَ هَذَا.
(Allah) ya ce: Ka ce ya Musa: La'ilaha illallahu. Sai (Musa) ya ce: Ya Ubangiji! Ai dukkan bayinka suna fadar wannan.
قَالَ: يَا مُوسَى لَوْ أَنَّ السَّمَوَاتِ السَّبْعَ وَعَامِرَهُنَّ غَيْرِي وَالْأَرَضِينَ السَّبْعَ فِي كِفَّةٍ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ فِي كِفَّةٍ، مَالَتْ بِهِنَّ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ.
(Allah) ya ce: Ya Musa! Da za a sanya sammai guda bakwai da mazaunansu — in ba ni ba — da kuma kassai guda bakwai a sikeli guda, a sanya 'La'ilaha illallahu' a daya bangaren, to lallai wannan kalmar (La'ilaha illallahu) ita za ta nauyaya/yi rinjaye a kansu.
قَالَ اللهُ تَعَالَى: يَا ابْنَ آدَمَ، لَوْ أَتَيْتَنِي بِقُرَابِ الْأَرْضِ خَطَايَا ثُمَّ لَقِيتَنِي لَا تُشْرِكُ بِي شَيْئًا لَأَتَيْتُكَ بِقُرَابِهَا مَغْفِرَةً.
Allah Madaukakin Sarki ya ce: Ya dan Adam! Da za ka zo mini da kura-kurai na (zunubai) kusan cikin kasa, sannan ka hadu da ni ba ka yi mini shirka da komai ba, to zan zo maka da misalin cikin kasar don nama gafara.
فِيْه الْمَسَائِلُ
Abubuwan da aka koya daga babin:
الأُولَى: سَعَةُ فَضْلِ اللهِ.
Na ɗaya:Fa ɗin falalar Allah.
الثَّانِيَةُ: كَثْرَةُ ثَوَابِ التَّوْحِيدِ عِنْدَ اللهِ.
Na biyu:Yawan ladar Tauhidi a gun Allah.
الثَّالِثَةُ: تَكْفِيرُهُ مَعَ ذَلِكَ لِلذُّنُوبِ.
Na uku:Kasancewarsa yana kankare zunubai.
الرَّابِعَةُ: تَفْسِيرُ الآيَةِ الَّتِي فِي سُورَةِ الأَنْعَامِ.
Na huɗu:Tafsirin ayar Suratul An'am.
الخَامِسَةُ: تَأَمُّلُ الخَمْسِ اللَّوَاتِي فِي حَدِيثِ عُبَادَةَ.
Na biyar:Yin tunani a kan abubuwa biyar na hadisin Ubada.
السَّادِسَةُ: أَنَّكَ إِذَا جَمَعْتَ بَيْنَهُ وَبَيْنَ حَدِيثِ عِتْبَانَ تَبَيَّنَ لَكَ مَعْنَى "لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ".
Na shida:Idan ka hada hadisin Ubada da na Itban, ma'anar "La'ilaha illallahu" za ta bayyana gare ka.
السَّابِعَةُ: التَّنْبِيهُ لِلشَّرْطِ الَّذِي فِي حَدِيثِ عِتْبَانَ.
Na bakwai:Ankararwa kan sharadin da ke cikin hadisin Itban.
الثَّامِنَةُ: كَوْنُ الأَنْبِيَاءِ يَحْتَاجُونَ لِلتَّنْبِيهِ عَلَى فَضْلِ "لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ".
Na takwas:Kasancewar Annabawa ma suna bukatar a ankarar da su kan falalar wannan kalmar ta Tauhidi.
التَّاسِعَةُ: التَّنْبِيهُ لِرُجْحَانِهَا بِجَمِيعِ المَخْلُوقَاتِ.
Na tara:Ankararwa kan nauyin wannan kalma a kan dukkan halittu.
العَاشِرَةُ: النَّصُّ عَلَى أَنَّ الأَرَضِينَ سَبْعٌ كَالسَّمَوَاتِ.
Na goma:Nassin cewa kassai ma bakwai ne kamar sammai.
الحادية عشرة: أن لهنَّ عمَّارًّا.
Na sha ɗaya:Lallai suna da masu kulawa da su.
الثَّانِيَةَ عَشْرَةَ: إِثْبَاتُ الصِّفَاتِ خِلافاً لِلأَشْعَرِيَّةِ.
Na sha biyu:Tabbatar da siffofin Allah, akasin ra'ayin Ash'ariyyah.
الثَّالِثَةَ عَشْرَةَ: مَعْرِفَةُ أَنَّ تَرْكَ الشِّرْكِ لَيْسَ قَوْلَهَا بِاللِّسَانِ فَقَطْ.
Na sha uku:Sanin cewa barin shirka ba kawai fadar kalmar da harshe ba ne zalla.
الرَّابِعَةَ عَشْرَةَ: تَأَمُّلُ الجَمْعِ بَيْنَ كَوْنِ عِيسَى وَمُحَمَّدٍ عَبْدَيِ اللهِ.
Na sha hudu:Tunani kan matsayin Annabi Isah da Annabi Muhammad SAW a matsayin bayin Allah.
الخَامِسَةَ عَشْرَةَ: مَعْرِفَةُ كَوْنِ عِيسَى كَلِمَةَ اللهِ.
Na sha biyar:Sanin cewa Annabi Isah kalmar Allah ne.
السَّادِسَةَ عَشْرَةَ: مَعْرِفَةُ كَوْنِهِ رُوحاً مِنْهُ.
Na sha shida:Sanin cewa Annabi Isah ruhi ne daga Allah.
السَّابِعَةَ عَشْرَةَ: مَعْرِفَةُ فَضْلِ الإِيمَانِ بِالجَنَّةِ وَالنَّارِ.
Na sha bakwai:Sanin falalar imani da Aljanna da Wuta.
الثَّامِنَةَ عَشْرَةَ: مَعْرِفَةُ قَوْلِهِ "عَلَى مَا كَانَ مِنَ العَمَلِ".
Na sha takwas:Fahimtar fadar Annabi cewa "a kan duk irin aikin da ya gabatar".
التَّاسِعَةَ عَشْرَةَ: مَعْرِفَةُ أَنَّ المِيزَانَ لَهُ كَفَّتَانِ.
Na sha tara:Sanin cewa ma'aunin aiki yana da kwanuka biyu.
العِشْرُونَ: مَعْرِفَةُ ذِكْرِ الوَجْهِ.
Na ashirin:Sanin cewa Allah yana da siffar Fuska.
والله أعلم.
Allah ne mafi sani. 🙏
28/04/2026
HATSARIN BARIN SALLAH DA GANGAN!
An ruwaito a cikin Sunna cewa Manzon Allah, tsira da amincin Allah sun tabbata a gare shi, ya ce: "Duk wanda ya bar sallah da gangan, za a cire masa kariyar Allah."
Imam Ahmad ne ya rawaito shi (26818)
AL-KABA'IR📚
28/04/2026
Darasi na farko acikin littafin Kitabut tauhid 01:
كِتَابُ التَّوْحِيْدِ
(Littafin Kadaita Allah)
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
(Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai)
اَلْحَمْدُ لِلّٰهِ نَحْمَدُهُ وَنَسْتَعِيْنُهُ وَنَسْتَغْفِرُهُ وَنَتُوْبُ إِلَيْهِ
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafararsa, kuma muna tuba zuwa gare shi,
وَنَعُوْذُ بِاللهِ مِنْ شُرُوْرِ أَنْفُسِنَا وَسَيِّئَاتِ أَعْمَالِنَا
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu,
مَنْ يَهْدِ اللهُ فَلَا مُضِلَّ لَهُ، وَمَنْ يُضْلِلْ فَلَا هَادِيَ لَهُ
Duk wanda Allah ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓatar babu mai shiryar da shi,
وَأَشْهَدُ أَنْ لَا إِلٰهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيْكَ لَهُ
Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya,
وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُوْلُهُ، أَمَّا بَعْدُ:
Kuma na shaida lallai Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne. Bayan haka:
فَيَقُوْلُ اللهُ تَعَالَى: ﴿وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُوْنِ﴾ [الذاريات/ ٥٦]
Allah Maɗaukaki yana cewa: "Ban halacci aljannu da mutane ba sai don su bauta mini." [Suratul Zariyat:Aya ta 56]
وَقَوْلُهُ: ﴿وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُوْلًا أَنِ اعْبُدُوا اللهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوْتَ﴾ [النحل/ ٣٦]
Da faɗinsa: "Kuma lallai mun aika manzo a cikin kowace al'umma (don ya gaya musu) ku bautawa Allah kuma ku nisanci ɗagutu/gumaka." [Suratun Nahl:Aya ta 36]
وَقَوْلُهُ: ﴿وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوْا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا﴾ [الإسراء/ ٢٣]
Da faɗinsa: "Kuma Ubangijinka ya hukunta kada ku bautawa kowa sai Shi kaɗai, kuma ku kyautatawa mahaifa (iyaye guda biyu)." [Suratul Isra'i:Aya ta 23]
وَقَوْلُهُ: ﴿وَاعْبُدُوا اللهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا﴾ [النساء/ ٣٦]
Da faɗinsa: "Ku bautawa Allah kuma kada ku haɗa shi da wani abu (wajen bauta)." [Suratun Nisa'i:Aya ta 36]
وَقَوْلُهُ: ﴿قُلْ تَعَالَوْا أَتْلُ مَا حَرَّمَ رَبُّكُمْ عَلَيْكُمْ أَلَّا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا﴾ [الأنعام/ ١٥١]
Da faɗinsa: "Ka ce: Ku zo in karanta muku abin da Ubangijinku ya haramta muku; (shi ne) kada ku haɗa Shi da komai." [Suratul An'am:Aya ta 151])
قَالَ ابْنُ مَسْعُوْدٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ: مَنْ أَرَادَ أَنْ يَنْظُرَ إِلَى وَصِيَّةِ مُحَمَّدٍ ﷺ الَّتِي عَلَيْهَا خَاتَمُهُ فَلْيَقْرَأْ قَوْلَهُ تَعَالَى: ﴿قُلْ تَعَالَوْا أَتْلُ مَا حَرَّمَ رَبُّكُمْ عَلَيْكُمْ أَلَّا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا﴾ - إِلَى قَوْلِهِ: ﴿وَأَنَّ هٰذَا صِرَاطِيْ مُسْتَقِيْمًا﴾ [الأنعام/ ١٥١-١٥٣]
Abdullahi ɗan Mas'ud ya ce: "Wanda yake son ya ga wasiyyar Annabi Muhammad SAW wadda take kamar akwai hatiminsa a kanta (don muhimmancinta), to ya karanta faɗin Allah: (Ka ce: Ku zo in karanta muku...) har zuwa faɗinsa: (Kuma lallai wannan ita ce hanyata madaidaiciya)." [Suratul An'am:Aya ta 151-153])
عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: كُنْتُ رَدِيْفَ النَّبِيِّ ﷺ عَلَى حِمَارٍ
Daga Mu'azu ɗan Jabal (RA) ya ce: "Na kasance Ɗangoyo a bayan Annabi SAW a kan wani jaki."
فَقَالَ لِي: يَا مُعَاذُ؛ أَتَدْرِي مَا حَقُّ اللهِ عَلَى الْعِبَادِ، وَمَا حَقُّ الْعِبَادِ عَلَى اللهِ؟
Sai ya ce mini: "Ya Mu'azu, shin ka san mene ne haƙƙin Allah a kan bayinsa, kuma mene ne haƙƙin bayi a kan Allah?"
قُلْتُ: اللهُ وَرَسُوْلُهُ أَعْلَمُ
Na ce: "Allah da Manzonsa ne mafi sani."
قَالَ: حَقُّ اللهِ عَلَى الْعِبَادِ أَنْ يَعْبُدُوْهُ وَلَا يُشْرِكُوْا بِهِ شَيْئًا
Ya ce: "Haƙƙin Allah a kan bayi shi ne su bauta masa kuma kada su haɗa shi da komai."
وَحَقُّ الْعِبَادِ عَلَى اللهِ أَنْ لَا يُعَذِّبَ مَنْ لَا يُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا
“Haƙƙin bayi kuma a kan Allah shi ne kada ya azabtar da wanda bai haɗa shi da komai ba.”
قُلْتُ: أَفَلَا أُبَشِّرُ النَّاسَ؟ قَالَ: لَا تُبَشِّرْهُمْ فَيَتَّكِلُوْا. أَخْرَجَاهُ فِي الصَّحِيْحَيْنِ.
Na ce: "Shin ba zan yi wa mutane bushara ba?" Sai ya ce: "Kada ka yi musu bushara (yanzu) gudun kada su dogara (su daina aiki)." Bukhari da Muslim ne s**a rawaito shi.
فِيْهِ مَسَائِلُ:
Akwai mas'aloli (darussa) a cikin wannan babin:
الأُوْلَى: الْحِكْمَةُ مِنْ خَلْقِ الْجِنِّ وَالْإِنْسِ.
Na farko: Hikimar halittar aljannu da mutane.
الثَّانِيَةُ: أَنَّ الْعِبَادَةَ هِيَ التَّوْحِيْدُ، لِأَنَّ الْخُصُوْمَةَ فِيْهِ.
Na biyu: Lallai bauta ita ce kadaita Allah (Tauhidi), domin a kansa ne aka yi jayayya.
الثَّالِثَةُ: أَنَّ مَنْ لَمْ يَأْتِ بِهِ لَمْ يَعْبُدِ اللهَ.
Na uku: Wanda bai zo da Tauhidi ba, to bai bautawa Allah ba (ko da yana sallah).
الرَّابِعَةُ: الْحِكْمَةُ فِي إِرْسَالِ الرُّسُلِ.
Na huɗu: Hikimar aiko da Manzanni.
الْخَامِسَةُ: أَنَّ الرِّسَالَةَ عَمَّتْ كُلَّ أُمَّةٍ.
Na biyar: Lallai saƙon Allah ya game kowace al'umma.
السَّادِسَةُ: أَنَّ دِيْنَ الأَنْبِيَاءِ وَاحِدٌ.
Na shida: Addinin Annabawa duka ɗaya ne (Tauhidi).
السَّابِعَةُ: الْمَسْأَلَةُ الْكَبِيْرَةُ: أَنَّ عِبَادَةَ اللهِ لَا تَحْصُلُ إِلَّا بِالْكُفْرِ بِالطَّاغُوْتِ.
Na bakwai: Zance mai girma: Bautar Allah ba ta tabbata sai an kafirce wa gumaka.
الثَّامِنَةُ: أَنَّ الطَّاغُوْتَ عَامٌ فِي كُلِّ مَا عُبِدَ مِنْ دُوْنِ اللهِ.
Na takwas: Ɗagutu ya ƙunshi duk wani abu da ake bauta masa ba Allah ba.
التَّاسِعَةُ: عِظَمُ شَأْنِ الثَّلَاثِ الآيَاتِ الْمُحْكَمَاتِ فِي سُوْرَةِ الأَنْعَامِ عِنْدَ السَّلَفِ، وَفِيْهَا عَشْرُ مَسَائِلَ، أَوْلَاهَا النَّهْيُ عَنِ الشِّرْكِ.
Na tara: Girman matsayin ayoyi uku kwarara na cikin suratul An'am a wurin magabata, waɗanda s**a ƙunshi mas'aloli goma, na farkon su ne hani ga shirka.
الْعَاشِرَةُ: الآيَاتُ الْمُحْكَمَاتُ فِي سُوْرَةِ الإِسْرَاءِ، وَفِيْهَا ثَمَانِيَ عَشْرَةَ مَسْأَلَةً بَدَأَهَا اللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿لَا تَجْعَلْ مَعَ اللهِ إِلٰهًا آخَرَ فَتَقْعُدَ مَذْمُوْمًا مَخْذُوْلًا﴾.
Na goma: Ayoyin suratul Isra'i waɗanda suke ƙunshe da mas'aloli goma sha takwas, Allah ya fara su da: "Kada ka sanya wani abin bauta na daban tare da Allah."
وَخَتَمَهَا بِقَوْلِهِ: ﴿وَلَا تَجْعَلْ مَعَ اللهِ إِلٰهًا آخَرَ فَتُلْقَى فِي جَهَنَّمَ مَلُوْمًا مَدْحُوْرًا﴾.
Kuma ya kammala su da faɗinsa: "Kada ka sanya wani abin bauta na daban tare da Allah, har a jefa ka a Jahannama kana wanda ake zargi, korarre."
وَنَبَّهَنَا اللهُ سُبْحَانَهُ عَلَى عِظَمِ شَأْنِ هٰذِهِ الْمَسَائِلِ بِقَوْلِهِ: ﴿ذٰلِكَ مِمَّا أَوْحَى إِلَيْكَ رَبُّكَ مِنَ الْحِكْمَةِ﴾.
Allah ya faɗakar da mu kan girman waɗannan mas'aloli da faɗinsa: "Wannan yana daga abin da Ubangijinka ya yi maka wahayi na hikima."
الْحَادِيَةَ عَشْرَةَ: آيَةُ سُوْرَةِ النِّسَاءِ الَّتِي تُسَمَّى آيَةَ الْحُقُوْقِ الْعَشْرَةِ، بَدَأَهَا اللهُ تَعَالَى بِقَوْلِهِ: ﴿وَاعْبُدُوا اللهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا﴾.
Na sha ɗaya: Ayar suratul Nisa'i da ake kira 'Ayar hakkoki goma', wadda Allah ya fara ta da cewa: "Ku bautawa Allah kuma kada ku haɗa shi da komai."
الثَّانِيَةَ عَشْرَةَ: التَّنْبِيْهُ عَلَى وَصِيَّةِ رَسُوْلِ اللهِ ﷺ عِنْدَ مَوْتِهِ.
Na sha biyu: Faɗakarwa kan wasiyyar Manzon Allah SAW kafin rasuwarsa.
الثَّالِثَةَ عَشْرَةَ: مَعْرِفَةُ حَقِّ اللهِ عَلَيْنَا.
Na sha uku: Sanin haƙƙin Allah a kanmu.
الرَّابِعَةَ عَشْرَةَ: مَعْرِفَةُ حَقِّ الْعِبَادِ عَلَيْهِ إِذَا أَدَّوْا حَقَّهُ.
Na sha huɗu: Sanin haƙƙin bayi a wurin Allah idan sun sauke haƙƙinsa.
الْخَامِسَةَ عَشْرَةَ: أَنَّ هٰذِهِ الْمَسْأَلَةَ لَا يَعْرِفُهَا أَكْثَرُ الصَّحَابَةِ.
Na sha biyar: Lallai wannan mas'alar (ta Mu'azu) mafi yawan sahabbai ba su sani ba (a wancan lokacin).
السَّادِسَةَ عَشْرَةَ: جَوَازُ كِتْمَانِ الْعِلْمِ لِلْمَصْلَحَةِ.
Na sha shida: Halaccin ɓoye ilimi don wata maslahar (kamar gudun kar mutane su daina aiki).
السَّابِعَةَ عَشْرَةَ: اسْتِحْبَابُ بِشَارَةِ الْمُسْلِمِ بِمَا يَسُرُّهُ.
Na sha bakwai: Mustahabbancin yi wa musulmi bushara da abin da zai faranta masa rai.
الثَّامِنَةَ عَشْرَةَ: الْخَوْفُ مِنَ الاتِّكَالِ عَلَى سَعَةِ رَحْمَةِ اللهِ.
Na sha takwas: Tsoron dogara kacokan akan faɗin rahamar Allah ba tare da yin aiki ba.
التَّاسِعَةَ عَشْرَةَ: قَوْلُ الْمَسْؤُوْلِ عَمَّا لَا يَعْلَمُ: (اللهُ وَرَسُوْلُهُ أَعْلَمُ).
Na sha tara: Wanda aka tambaya abin da bai sani ba ya ce: "Allah da Manzonsa ne mafi sani."
الْعِشْرُوْنَ: جَوَازُ تَخْصِيْصِ بَعْضِ النَّاسِ بِالْعِلْمِ دُوْنَ بَعْضٍ.
Na ashirin: Halaccin keɓance wasu mutane da wani ilimi ba tare da wasu ba.
الْحَادِيَةُ وَالْعِشْرُوْنَ: تَوَاضُعُهُ ﷺ لِرُكُوْبِ الْحِمَارِ مَعَ الإِرْدَافِ عَلَيْهِ.
Ashirin da ɗaya: Sauƙin kan Annabi SAW na hawa jaki da kuma ɗaukar wani a bayansa.
الثَّانِيَةُ وَالْعِشْرُوْنَ: جَوَازُ الإِرْدَافِ عَلَى الدَّابَّةِ.
Ashirin da biyu: Halaccin yin goyo (mutum biyu) a kan dabba.
الثَّالِثَةُ وَالْعِشْرُوْنَ: فَضِيْلَةُ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ.
Ashirin da uku: Falala da darajar Mu'azu ɗan Jabal.
الرَّابِعَةُ وَالْعِشْرُوْنَ: عِظَمُ شَأْنِ هٰذِهِ الْمَسْأَلَةِ.
Ashirin da huɗu: Girman muhimmancin wannan mas'alar ta (Kadaita Allah).
والله أعلم.
Allah ne mafi Sani 🙏
Jawahirul ma,ani
Toh kunji dae se kusan Dawa zaku Hada kan
Up Sunnah ⭐
Family Issue
Allah ya shiryar daku Baki daya 😊
Allah ya jaddada Rahamar sa Gareka 🙏
Yan Bidi,a Dillalan sharri
Allah ya ganar daku 🤔
21/09/2025
14/09/2025
Ya Allah 🙏🙏🙏
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
700101