Labaran Kasar Mu

Labaran Kasar Mu

Share

29/04/2026

“Bayan kammala bautar kasa (NYSC), na shiga harkar siyasa kuma aka zaɓe ni a matsayin Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo. Da fiye da shekaru 36 na gogewa a hidimar jama’a, babu wani abu a siyasa da zan ji tsoro a kansa.”

Labaran Kasar Mu Bashiru Umar Yareema Real Bangis Yarimawa

22/04/2026

BABANGIDA BANGIS: JAGORAN ADC YARIMAWA
​Babangida Bangis babban jigo ne kuma jagora a cikin tafiyar jam’iyyar ADC a yankin Yarimawa. Matsayinsa na jagora ya ginu ne a kan jajircewa da kuma kokarin hada kan jama'a domin cimma burin siyasa da ci gaban al'umma.
​A matsayinsa na Jagoran ADC, babban burinsa ya hada da:
​Hada Kan Al'umma: Karfafa gwiwar matasa da manya na Yarimawa wajen gane manufofin jam'iyyar ADC.
​Wakilci na Gari: Kasancewa murya ga talakawa da kuma tabbatar da cewa muradun yankinsa sun isa matakin da ya dace a siyasance.
​Siyasar Ci Gaba: Tabbatar da cewa taken jam'iyyar na "Domin Dukkan 'Yan Najeriya" ya fito fili ta hanyar ayyukan raya kasa da kyautata rayuwar jama'ar Yarimawa.
​Babangida Bangis ya shahara wajen sanin ya kamata da kuma kokarin ganin an tafi da kowa a cikin harkar siyasar Yarimawa , wanda hakan ya ba shi damar zama babban jagora abin koyi

28/10/2025

Gwamnatin Najeriya ta sanar da wani sabon haraji kan tikitin jirgi ga fansinjojin dake son tafiya zuwa ƙetare, inda daga ranar 1 ga watan Disamba duk wanda zai yi tafiya zuwa ƙasar waje sai ya biya harajin Dala 11.5.

Harajin wanda ake kira APIS, zai ƙara adadin harajin tsaro zuwa Dala 31.50 kan duk tikitin jirgi guda ɗaya da mutum zai siya, kuma ana tsammanin za’a tarawa hukumar kula da sufurin jiragen saman Najeriya aƙalla Dala miliyan 46 a duk shekara ta hanyar karbar wannan haraji.

A gefe guda kuma, matakin wanda aka tsara za’a shafe shekaru 20 ana aiki da shi, zai ƙara tsadar kuɗaɗen fita waje ga ‘yan asalin Najeriya.

08/08/2025

“YADDA ƳAN SANDA S**A K**A NI, BA TARE DA SANIN CEWAR NINE KWAMISHINAN ƳAN SANDA BA” – MD ABUBAKAR

“A lokacin da nake Kwamishinan Ƴan Sanda a jihar Lagos, bana wasa da aiki — musamman ranar Asabar. Ko da yake ayyuka na suna farawa ne daga karfe 10 na safe, wannan rana na tashi tun 6 na safe don in kai ziyara ba tare da sanarwa ba.

Na hau motata Jeep na nufi ofis, amma sai na yanke shawarar yin ‘yin ziyarar ba-zata’ ga wasu 'yan sanda a kan hanya – domin in ga irin yadda suke gudanar da aikinsu.

A wani shingen bincike “checkpoint” dake t**in Herbert Macaulay, wasu matasan 'yan sanda s**a tsaida ni. Wani karamin dan sanda (constable) ya kalle ni yace:

> "Kai saurayi, ina zaka ne da motar mahaifinka?"

Ya bukaci takardun motar da shaidar lasisin tuƙi. Na ce masa sunana Mohammed. Yace dole sai na nuna ID card. Na ce masa, to ya fara nuna mini nasa. Bai da ID card, don haka sai ya kira sergeant dinsu.

Shi ma sergeant din ya bukaci ID card dina, na ce masa ya nuna mini nasa kafin nawa. Ganin bana jin tsoro ko nuna daraja, sai s**a ce mu tafi ofishin ‘yan sanda na Yaba (Panti) domin “gano ko ni wanene”.

Muna isa station – babu parking sai a wajen DPO. Na ajiye motata a can, constable din ya fusata yace: “Wannan wajen parking din DPO ne fa!” Ko uffan ban ce masa ba.

Bayan mun shiga ciki, sai s**a kaini wurin wani ASP (Assistant Superintendent of Police) wanda ke sanye da gajeren wando 'shorts'!. Yace na shigo, na ki, nace masa ba zai yiwu ya tuhumeni cikin kayan gida ba. Yayi fushi ya jawo ni ciki da ƙarfi – nima ina jan shi. Da ya duba fuskata da kyau sai ya fara zare ido…

A gefe guda, wani tsoho da ke ofishin ya leƙa ofishin DPO don duba hoton shugabannin rundunar Ƴan sanda dake jikin bango. Da ya tabbatar cewa ni ne, sai kawai ya tsallake taga ya gudu!

Sergeant da ya kawo ni ya kasa gane me ke faruwa, har sai da wani Ɗan sanda ya matso kusa da kunnensa, ya ce masa: “Kai, CP ne wannan fa!”.

Cikin firgici, ASP ɗin da ke sanye da shorts ma ya bi taga ya gudu!

Bayan haka, Area Commander ya kirani ya tambaya me ya faru. Aka gaya masa cewa an tsare DPO, ASP, da sauran ‘yan sanda da s**a shiga lamarin – suna jiran umarni na.

Abin da ya fi tada min hankali ba wai kamun da s**a yi min ba ne – a’a, amma irin yadda s**a nuna rashin tarbiyya, rashin horo, da rashin kwarewa a aiki.

Yaya dan sanda zai tsaya a t**i ba tare da ID ba, yana tsare jama’a? Yaya ASP zai zauna da kaya irin na gida yana sarrafa aiki? Wannan ya kara tabbatar min da cewa shugabanci ba sai ka zauna ofis ba – dole ka fita ka duba, ka gani da idonka, ka tabbatar da gaskiya da adalci a kowanne mataki.

Fassara: AB Damare

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Lagos Island
Kano
73