Sani Shuaibu Suleman
ADDU'A IDAN MAI AZUMI ZAI BUDA BAKI
ذهب الظمأ، وابتلت العروق، وثبت الأجر إن شاء الله.
Ma'ana: Kishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah Ya So.
Abdullahi bn Amr bn al-As ya ce Manzo Allah, Tsira da amincin Allah Su tabbata a gare Shi, ya ce: "Mai Azumi yana da addu'a da Ba a mayar da ita Idan ya Zo Bude baki”. Abdullahi bn Amr ya Kasance Idan ya zo Bude Baki Sai ya ce;
اللهم إني أسأللك برحمتك التي و سعت كل شي ء إن تغفر لي
Ma'ana: Ya Allah! Ina Rokon ka Saboda Rahamarka da ta yalwaci komai, ka gafarta mini.
© Sani Shuaibu Suleman
HANA GABA DA KAURACEWA JUNA
Daga Abu Huraira RA ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: ana bude kofofin Aljannah duk ranar litinin da ranar alhamis, sai a yafe wa duk bawan da ba ya yin shirka da Allah , amma banda mutumin da yake gaba da dan uwansa, sai a ce: Ku kyale wadannan har sai sun yi Sulhu; Ku kyale wadannan har sai sun yi Sulhu; Ku kyale wadannan har sai sun yi Sulhu.
Muslim ne ya ruwaito.
KWADAITARWA KAN YIN SANA'A
Daga Abu Huraira ya ce: Na Ji Manzon Allah yana cewa: dayanku ya fita da safe ya yi itace ya dauko shi a gadan bayansa (da niyyar yin Sana'a) ya yi sadaka da shi ya wadatu daga rokon mutane, ya fi alheri a gare shi kan ya roki wani, shi kuma ko ya ba shi , ko ya hana shi. wannan kuwa saboda hannun da yake sama ( mai kyauta) ya fi hannun da yake kasa (mai kar6a). kuma ka fara (wajen ciyarwa) da iyalinka.
Bukhari da Muslim s**a ruwaito shi.
Click here to claim your Sponsored Listing.