Darma Tv
30/12/2025
YANZU-YANZU: Kotu ta tura Malami da matarsa da Ɗansa gidan gyaran hali na Kuje, bisa zargin Almundahanar Naira Biliyan 8.7
Darma Tv
13/12/2025
Dubban magoya bayan Messi sun yi fushi ne bayan biyan kuɗin Indiya rupee 12,000 domin ganin ɗan wasan amma ba su samu dama ba saboda yawan mutanen da ke tsare da shi, sannan ya bar wurin da wuri.
Messi ya je Indiya ne domin ƙaddamar da mutum-mutuminsa da aka gina a ƙasar.
Darma TV
Daga bbc
05/12/2025
Antoni Janar na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen k**a masu goyo a babur
Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude (SAN), ya gana da Kwamishinan ’Yansanda na Jihar Kano a ranar Juma’a domin tattauna wa kan koke-koken jama’a kan kamun masu babura da ake yi a fadin jihar.
Taron ya mayar da hankali ne kan duba yadda ake aiwatar da Dokar hana Achaba ta 2013, tare da jaddada cewa dole a tabbatar da cewa duk wani aikin tsaro yana gudana cikin bin doka ba tare da tauye hakkin direbobin babura da ba na Achaba ba.
Mai taimaka wa kwamishinan shari’a kan harkokin yada labarai, Abubakar Tijjani Ibrahim, ya ce tattaunawar ta yi nufin karfafa hadin kai tsakanin Ma’aikatar Shari’a da Rundunar ’Yansanda domin tabbatar da sahihin aiwatar da doka cikin gaskiya da adalci.
Ya kara da cewa za a fitar da cikakkun bayanai kan sak**akon ganawar a nan gaba.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
70010