KABO MEDIA WATCH

KABO MEDIA WATCH

Share

Photos from KABO MEDIA WATCH's post 26/04/2026

Yadda Bikin saukar Alqurani na Makarantar WOFAN Islamiyya ya kasance a Jiya Asabar 25th ga watan Aprilu, 2026.

Makarantar WOFAN Islamiyya ta yaye dalibai Maza da mata 32 wadanda s**a sauke alkur'ani.

A kokarin Haj. Dr. Salamatu Garba na samar da kyakyawan yanayi na tarbiyyar yara manyan gobe da kuma ilmi mai albarka a wannan Karon ma Wofan Islamiyya ta yaye Dalibai 32.

Iyayen yara Sunyi matukar nuna godiyarsu da Farinciki ganin yayansu sun sauke alkur'ani Mai girma.
Kuma sun Mika godiyarsu ga Haj. Salamatu Garba da Malaman WOFAN ISLAMIYYA.

Haj. Salamatu tayi addu'ar fatan Alkhairi ga dalibai da iyaye tare tayasu farin ciki Mara masaltuwa da wannan gagarumin cigaba wajen samarwa yayanmu ilimin boko da na addini dan Samar da rayuwa mai inganci Wanda zamu yi Alfahari dasu da kasarmu mai Albarka baki daya.

A karshe ta yiwa daukacin Alummar da s**a halarci wannan gagarimin bikin sauka fatan Alheri da fatan kowa ya koma gida lafiya.

20/04/2026

Allah ya gafartawa Saddiku Mai Walda da Dahiru alkali.
Allah ya bawa ahalinsu hakurin rabuwa dasu. Allah ka gafarta Mana.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Kano