Real Abba Ibrahim
Wa
zaka Zaɓa
A
Shugabancin ƙasa
a Nigeria.
15/04/2026
Kamfanin MTN Nigeria ya sanar da wani sabon sauyi da ya shafi masu amfani da layinsa a fadin ƙasar, inda ya dakatar da damar karɓar bashi (airtime ko data) ga yawancin kwastomominsa.
Wannan mataki ya zo ne a wani yunƙuri na sake fasalin tsarin bayar da bashi, bayan kamfanin ya lura da ƙaruwa a yawan bashin da ba a biya ba, wanda ke janyo asara mai yawa ga kamfanin. A cewar wasu bayanai daga ciki, an ce MTN na kokarin tabbatar da cewa tsarin nasa ya kasance mai ɗorewa da kuma rage matsalolin da ke tattare da rashin biyan bashi a kan lokaci.
Masu amfani da layin MTN da dama sun bayyana damuwarsu kan wannan mataki, musamman waɗanda s**a saba dogaro da tsarin bashi domin ci gaba da sadarwa a lokacin da ba su da kuɗi a hannu. Wasu sun bayyana cewa wannan zai iya jefa su cikin matsala, musamman a lokutan gaggawa.
Sai dai wasu masana harkar sadarwa sun ce wannan mataki na iya zama na ɗan lokaci ne kawai, domin bai kamata kamfani ya daina wata muhimmiyar sabis da ke taimaka wa kwastomomi gaba ɗaya ba. Sun ƙara da cewa ana iya sake dawo da tsarin da wasu ƙa’idoji masu tsauri domin rage hasara.
A halin yanzu, MTN bai fitar da cikakken bayani kan ko wannan mataki na dindindin ba ne ko kuma na wucin gadi, amma ana sa ran za a samu ƙarin haske daga kamfanin nan gaba kaɗan.
Shawara ga masu amfani:
Idan kana amfani da MTN, yana da kyau ka riƙa tabbatar da cewa kana da isasshen kati ko data domin kauce wa tangarda, musamman idan kana yawan amfani da tsarin bashi a baya.
13/04/2026
Choose the correct answer👇
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Kano
HAKAJ