Saifullahi Muazu Muhammad
15/05/2025
Haruffan da suke cikin LEG, suna dai acikin GLE. Fafutukar ka da addu'ar ka ce zata taimaka maka wajen kaiwa ga inda kake so da kuma wacce kake so ka hau.
-Rubutun bashi da alaƙa da hotunan. Kawai na saka ne don ganin abinda yake trend a Arewa kenan a yau.
08/05/2025
Labari
Tsarin jam'iyya ɗaya a Nijeriya ba zai haifar da ɗa mai ido ba, in ji Jonathan
Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce ƙoƙarin komawa tsarin jam'iyya ɗayata hanyar “ƙarfa-ƙarfar ar siyasa” zai jefa ƙasar cikin rikici.
TheCable ta rawaito cewa Jonathan ya yi wannan furuci ne a jiya Laraba a wajen bikin tunawa da kuma gabatar da jawabin girmamawa ga marigayi Edwin Clark, fitaccen shugaba daga yankin Ijaw.
An gudanar da taron ne a Abuja, inda manyan ’yan siyasa s**a halarta.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce batun mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya yana tayar da kura a kafafen sada zumunta.
Jonathan ya ce ko da yake wasu ƙasashe sun rungumi tsarin jam’iyya ɗaya, an tsara hakan ne da kyau domin cimma wasu manufofin ƙasa.
Ya ce idan Najeriya na da niyyar rungumar tsarin jam’iyya ɗaya, sai an tsara shi yadda ya kamata ta hannun masana da kuma bayyana manufofin sa.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Kano