MW Hausa
21/06/2026
Janye korafi da neman afuwa bisa ga kuskuren da na yi
- Ibrahim Usman Yaro
13/06/2026
Ta tabbata babu Tsaro
Major janar Rabe Abubakar mai ritaya ya mutu a hannun 'yan bindiga. Kwamishinan tsaron jihar Dr Nasuru Ma'azu Damnusa ne ya tabbaar da mutuwar amma ba su kai ga dauko gawar ba.
Rahotin DW hausa
10/06/2026
LABARI DA DUMI-DUMI: Dan Takarar NDC Ya Kai Jam'iyyarsa Kara Wajen Hukumar EFCC Kan Zargin Damfarar Naira Miliyan 20.
Wani dan takarar majalisar dattawa (Sanata) da ke fushi a jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ya shigar da korafi gaban Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annuti (EFCC), inda yake zargin mambobin kwamitin tantance 'yan takarar sanata na jam'iyyar da laifukan zamba, damfara, da hadakar baki don tafka laifi da ya shafi Naira miliyan 20.
Ofishin Shugaban Hukumar EFCC ne ya karbi takardar korafin a babban sakatariyar hukumar da ke Abuja a ranar Talata.
Wannan lamari ya faru ne biyo bayan wasu zarge-zarge da jarumin fina-finai kuma dan siyasa, Kenneth Okonkwo ya yi kwanan nan. Shi dai Okonkwo yana tsaka da takaddama da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, bayan ya yi zargin cewa shugabannin jam'iyyar sun kafa wani tsari na karbar kudaden dole a hannun masu neman takara.
Bisa ga hujjojin da wani shafi na tona asiri mai suna Pidomnigeria ya fallasa a dandalin X (wanda aka sani da Twitter da), dan takarar da farko ya sayi fom din nuna sha'awar tsayawa takara na hukumar jam'iyyar akan kudi Naira miliyan 3, inda ya bi dukkan ka'idojin da shugabannin jam'iyyar s**a gindaya.
Sai dai, bayan isarsa Abuja don gudanar da tantancewar dole, an zargi kwamitin da tilasta wa dan takarar sanya hannu kan wata takardar rantsuwa ta doka, inda ya yi alkawarin amincewa da duk wani hukunci da kwamitin zai yanke, sannan kuma ya janye hakinnsa na kai jam'iyyar NDC gaban kotu don neman hakki.
Ya ce: “Da isarsa Abuja, s**a ba shi wani fom ya sanya hannu cewa zai amince da duk abin da kwamitin tantancewar ya yi, kuma ba zai kai NDC kotu ba. Ya yi mamaki, amma duk da haka ya sanya hannun. Ya zata za su tantance shi ne bisa la'akari da aikinsa na kwarewa, gogewarsa ta siyasa, tasirinsa ga mutanen karkara, ayyukansa na baya, da takardun shaidar karatu da ya mallaka, da sauran su.
“Amma abin mamaki, sai s**a fara tambayarsa game da bayanan asusun bankinsa (bank statement), adadin gidaje da kadarorin da ya mallaka, motoci da zuba jari, da kuma karfinsa na kudi.
“S**a shaida masa cewa lallai sai ya nuna bajinta da karfin kudi idan har da gaske yake yana son zama sanata. S**a rubuta masa bayanan asusun banki na FCMB, s**a ce ya biya tsabar kudi Naira miliyan 20,000,000 a ciki. Ya biya kudin, kuma tun daga ranar NDC ta rufe masa kofofinta har zuwa yau.
“Yanzu haka yana neman jam'iyyar da ta mayar masa da kudinsa Naira miliyan 20,000,000, kuma ya shigar da korafi a kansu wajen hukumar EFCC.”
Rahoranni sun bayyana cewa kwamitin ya tsananta wa dan takarar da tambayoyi game da asusun bankinsa, gidajen da ya mallaka, motocinsa, da sauran guraren da ya zuba jari, duk a karkashin sunan tantance karfinsa na kudi na tsayawa takara.
Bayan tantance karfinsa na kudi, an zargi kwamitin da ba wa dan takarar lambar asusun banki na First City Monument Bank (FCMB) ba tare da ba shi rasit ba, inda s**a umarce shi da ya tura Naira miliyan 20 cikin gaggawa domin ya tabbatar da samun gurbin takarar. Dan takarar ya cika wannan umarni, amma bayan nan sai shugabannin NDC s**a yanke dukkan wata alaka ta gudanarwa da shi.
Okonkwo ya bayyana irin wadannan zarge-zarge a kwanan nan. Kafin nan, Okonkwo ya taba raba wasu bayanan sirri na cikin gida daga wajen wani dan takarar Majalisar Wakilai, Obunike Ohaegbu, wanda shi ma ya yi zargin cewa jam'iyyar ta yi amfani da wasu kungiyoyin daidaita alamura na jiha (parallel state caucus structures) wajen neman Naira miliyan 10 daga hannun masu neman takarar Majalisar Wakilai da kuma Naira miliyan 20 daga hannun masu neman takarar Sanata, kafin a tattara jerin sunayen 'yan takarar a asirce a Otal din Johnwood da ke Abuja.
01/06/2026
Taruka guda Uku da basu da amfani a yanzu.
Daga shafin
Hassan Nasir Musa Gwammaja
Taron Old Boys
Taron Family
Taron Cigaban Unguwa.
Taron Old Boys tarone da akeyi aga yanda rayuwa tayi da wasu bayan rayuwar makaranta, a dora masu shadda me kyalli a hightable haka za'a tashi ba agenda sai wata shekarar a turo maka account kasa kudin taro.
Taron Family shima kusan tafiya daye suke dana makaranta banbancin kawai shi sai annuna an Isa dakai amma Yayan masu kudin family sune taurari a wajen karshe kafin a tashi babansu za'aita godewa a mic.
Taron unguwa kuwa idan kaga an Kira taro wani ne ya zama dan iska tuburan sunga zai bata musu Y'ay'a amma bazaka tabajin an taru domin a biyawa yara kudin Jamb, Waec ko Neco ba, duk taron masu kudin wnanan unguwa baza kaji sunce zasu dauki masu hankalin layinsu kasuwa ko makaranta ko masu degree su dauke su aiki ba, haka za'ai taron ai ta tsinewa yaron da s**a lalace karshe idan megidan ya mutu kaji ana ai dama Alhaji wane ne ya siyi gidan.
Jama'a yanzu fa muna karni na 21 Wanda zai taimake ka bazai wahalar dakai ba shiyasa akayi Opay da Moniepoint dan haka a daina doraku a igiyar zato da taron iska da wofi.
~Hassan Nasir Musa Gwammaja
31/05/2026
Gwamnoni sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta duba yanayin kara albashi ya kai 100,000 a matsayin mafi karancin Albashi ga ma'aikata. Saboda rage radadin matsin tattalin arziki.
28/05/2026
Ana ta cecekuce:
Waye zai iya rike Amana
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano