Arewa View Point

Arewa View Point

Share

11/06/2026

Jira ya kare , a yau da misalin karfe 8:00 za bude gasar kofin duniya tsakanin Mexico da South Africa, a wani wasa mai kayatarwa.
Mun shirya tsaf domin kawo dukkan wani labari tare da sakamakon wasan ni, fara daga wasannin rukuni har zuwa wasan karshe , tare da wasu kayatattun labarai
AREWA VIEW POINT

10/06/2026

UP NIGERIAN

A yau ne da misalin karfe 20:45 na dare za a buga wasan sada zumunci tsakinin Portugal da super Eagle 🦅.

A Haduwar karshe daii Portugal ta doke Eagle daci 4-0 a November 2022
a wasan da Ronaldo bai bugava sbd rauni.

Muna yiwa babbar Kungiyar mu ta kasa Nigerian wato super Eagles fatan nasara

AREWA VIEW POINT

10/06/2026

LABARI NA MUSAMMAN: Jorge Mendes ya bayyana cewa Vitinha da João Neves ba za su koma Real Madrid ba.
Kamar yadda aka ruwaito a ƙarshen mako, João Neves da Vitinha za su ci gaba da zama a Paris Saint-Germain (PSG), kuma ba za su koma Real Madrid ba.

PSG zata sake yin yin kurin lashe kofin karo na uku a jere , kamar yadda Madrid tayi daga 2016- 2018

AREWA VIEW POINT

08/06/2026

An nada José Mourinho a matsayin sabon kocin Real Madrid.
🇩🇪 Toni Rüdiger ya sabunta kwantiraginsa har zuwa watan Yuni na shekarar 2027.
🇫🇷 An cimma yarjejeniya da Ibrahima Konaté wadda za ta ɗaure shi da ƙungiyar har zuwa watan Yuni na shekarar 2030.

AREWA VIEW POINT
🇳🇱 Denzel Dumfries zai koma ƙungiyar kan kuɗin canja wuri na Yuro miliyan 20 (€20m).
Ana sa ran ƙarin manyan sanarwa nan ba da jimawa ba.

06/06/2026

MANEMA LABARAI

6 ga Yuni, 2026

HUKUMAR NOA RESHEN JIHAR KANO TA ZIYARCI FAFAR YAƊA LABARAI TA AREWA VIEW POINT DON WAYAR DA KAI KAN CUTAR EBOLA

A wani bangare na ƙoƙarin da take yi na wayar da kan jama'a game da cutar Ebola (EVD), Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Reshen Jihar Kano, ta yi amfani da shirin kafar yaɗa labarai ta yanar gizo mai suna Arewa View Points domin isar da saƙonnin kariya da faɗakarwa ga al'umma.

Shirin, wanda Babangida Musa Baba ya gabatar, ya samu halartar Hajiya Hauwa Adamu Garba, Shugabar Sashen Sadarwa da Yaɗa Labarai ta NOA Kano, tare da Hajiya Hafsat Kabiru Yaradu'a. Mahalartan sun yi cikakken bayani kan muhimmancin wayar da kai da ɗaukar matakan kariya domin kare lafiyar al'umma daga barazanar cutar Ebola.

Sun bayyana cewa duk da cewa a halin yanzu babu wani rahoto da ya tabbatar da bullar cutar Ebola a Najeriya, akwai buƙatar jama'a su kasance cikin shiri tare da bin shawarwari da matakan kariya da hukumomin lafiya s**a gindaya.

Jami'an sun jaddada muhimmancin wanke hannu akai-akai da ruwa da sabulu, kiyaye tsafta, gujewa hulɗa da ruwan jikin wanda ake zargin ya kamu da cutar, da kuma gaggauta kai rahoton duk wani mutum da ke nuna alamomin cutar ga hukumomin lafiya da abin ya shafa.

Har ila yau, shirin ya zama wata dama ta kawar da jita-jita da bayanan ƙarya da ke yawo game da cutar Ebola, tare da ƙarfafa jama'a su dogara da sahihan bayanai daga hukumomin gwamnati da cibiyoyin lafiya masu inganci.

Hukumar NOA Reshen Jihar Kano ta sake tabbatar da aniyarta na ci gaba da haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa jama'a sun samu ingantattun bayanai da za su taimaka wajen kare lafiyarsu da kuma dakile yaɗuwar cututtuka masu saurin yaɗuwa.

Kabiru Bala

Jami'in Hulɗa da Jama'a (PRO)Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA)Reshen Jihar Kano

06/06/2026

Tsohon Kakakin Rundunar Sojin Nigeria Kenan Manjo Janar Rabe Abubakar Mai Ritaya da Mai Dakin Sa a Hannun Yan’Bindiga

Wane Fata Kuke dashi a gare Su?

04/06/2026

AREWA VIEW POINT

FARFESA MAINASARA YAKUBU KURFI YA ZAMA SABON DEAN NA FACULTY OF COMMUNICATION A JAMI’AR BAYERO KANO

Daga Wakilinmu

An zaɓi Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi a matsayin sabon Dean na Faculty of Communication a Bayero University Kano, bayan kammala zaɓen da aka gudanar domin cike wannan muhimmin muƙami na shugabanci a tsangayar.

Zaɓen Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi ya samu karɓuwa daga malamai, ɗalibai da masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa, waɗanda s**a bayyana zaɓensa a matsayin wata alama ta amincewa da ƙwarewarsa, gogewarsa da kuma gudunmawar da ya dade yana bayarwa a fannin koyarwa da bincike.

Masu taya shi murna sun bayyana cewa sabon Dean ɗin ya yi fice wajen inganta harkokin ilimi da sadarwa, tare da nuna ƙwarewa a ayyukan gudanarwa da jagoranci a matakai daban-daban.

Ana sa ran sabon shugaban tsangayar zai ci gaba da kawo sababbin tsare-tsare da za su taimaka wajen bunƙasa Faculty of Communication, tare da ƙara ɗaukaka sunan Jami’ar Bayero Kano a matakin ƙasa da ƙasa.

Arewa View Point na taya Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi murnar wannan nasara tare da yi masa fatan alheri da nasara a sabon nauyin da aka ɗora masa.

AREWA VIEW POINT
“Muryar Al’umma, Madubin Gaskiya.”

04/06/2026

GIDAUNIYYAR ALH. YAHAYA LAWAN FOUNDATION NA CI GABA DA BAI WA DALIBAI SCHOLARSHIP A KANO

Daga Wakilinmu

Gidauniyyar Alhaji Yahaya Lawan Foundation na ci gaba da gudanar da shirinta na tallafa wa harkar ilimi ta hanyar bai wa ɗalibai marayu da marasa galihu tallafin karatu (Scholarship) domin sauƙaƙa musu nauyin karatu a manyan makarantu.

Sakataren Gidauniyyar, Alhaji Anas Mukhtar, ya bayyana cewa gidauniyyar na ba da tallafin karatu ga ɗalibai sama da mutum ɗari a duk shekara, inda ta mayar da hankali wajen tallafa wa marayu da ɗaliban da ke fuskantar ƙalubalen kuɗaɗen karatu a Jihar Kano da Arewacin Najeriya baki ɗaya.

A cewarsa, a wannan shekarar ma gidauniyyar ta ci gaba da rabon tallafin karatu ga ɗaliban da s**a cancanta, a wani shiri da ke gudana a Tsangayar Sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano (BUK), ƙarƙashin jagorancin sakataren gidauniyyar, Alhaji Anas Mukhtar.

Wakilan Arewa View Point da s**a ziyarci wurin rabon tallafin sun shaida yadda ɗalibai daga jami’o’i da kwalejoji daban-daban s**a taru domin karɓar tallafin, tare da nuna farin ciki da godiya ga gidauniyyar bisa wannan gagarumin tallafi da take bayarwa.

Masu anfani da tallafin sun bayyana cewa wannan shiri zai taimaka musu matuƙa wajen ci gaba da karatunsu ba tare da fuskantar matsalolin kuɗaɗen makaranta ba.

An yabawa Alhaji Yahaya Lawan Foundation kan irin gudunmawar da take bayarwa wajen bunƙasa ilimi da taimaka wa marasa ƙarfi, inda masu ruwa da tsaki s**a buƙaci sauran masu hannu da shuni da ƙungiyoyi masu zaman kansu su yi koyi da irin wannan aiki na alheri domin tallafa wa matasa da makomar ilimi a Arewa.

AREWA VIEW POINT
“Muryar Al’umma, Madubin Gaskiya.”

04/06/2026

AREWA VIEW POINT

Fitaccen Ɗan Kasuwar Man Fetur na Kano, Alhaji Audu Manager, Ya Rasu Yana da Shekaru 68

Al’ummar Jihar Kano da ma Arewacin Najeriya sun shiga jimami bayan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma hamshaƙin mai zuba jari a harkokin man fetur, Alhaji Audu Manager, wanda ya rasu yana da shekaru 68 a duniya.

Marigayin Audu Manager ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan kasuwa a Kano, inda ya shahara wajen gudanar da harkokin kasuwancin man fetur da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki da walwalar al’umma.

A tsawon rayuwarsa, ya taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa da dama tare da tallafawa al’umma a fannoni daban-daban. Hakan ya sanya ya kasance mutum mai farin jini da kima a tsakanin abokan hulɗarsa da al’ummar da ke kewaye da shi.

Labarin rasuwarsa ya haifar da alhini da jimami a tsakanin ‘yan uwa, abokai, abokan kasuwanci da daukacin waɗanda s**a amfana da ayyukan alherinsa. Mutane da dama sun fara bayyana alhininsu tare da yi masa addu’ar samun rahama daga Allah Maɗaukakin Sarki.

Marigayin ya bar tarihi mai kyau a fagen kasuwanci da ayyukan alheri, wanda za a ci gaba da tunawa da shi har tsawon lokaci.

Arewa View Point na miƙa ta’aziyya ga iyalansa, abokan arziki da daukacin al’ummar Kano bisa wannan babban rashi.

Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Amin.

— Arewa View Point

01/06/2026

FIFA ta sanar da wasu manyan sauye-sauye ga dokokin gasar Kofin Duniya domin inganta ladabtarwa da rage yaudara a wasa.

• Masu tsaron gida ba za su ƙara samun damar amfani da dabarun ɓata lokaci ba.

• Za a hana 'yan wasa kusantar yankin masu horarwa (technical area) yayin da aka dakatar da wasa.

• VAR za ta samu ƙarin iko wajen duba laifukan kai hari da s**a faru kafin bugun tazara (set-piece).

• Rufe baki da hannu yayin faɗa ko sa-in-sa a filin wasa zai iya jawo jan kati.

Ana sa ran za a gudanar da gasar Kofin Duniya ƙarƙashin wasu daga cikin mafi tsauraran dokokin ƙwallon ƙafa da aka taɓa gani.

AREWA VIEW POINT

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Kano
Kano