View Point Hausa

View Point Hausa

Share

08/05/2026

LABARI DA DUMI-DUMI

An samu wani sabon bayani mai tayar da hankali daga bakin wani tsohon SSA na tsohon Gwamnan Jihar Zamfa Bello Matawalle, inda ya bayyana yadda ake zargin wani jami’in dan sanda da hannu a kisan Dadiyata.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon hadimin ya yi wannan bayani ne yayin wata tattaunawa, inda ya ce akwai bayanai da suke nuna yadda lamarin ya faru da kuma mutanen da ake zargi da hannu a ciki. Wannan batu ya sake jawo ce-ce-ku-ce da martani daga jama’a musamman a kafafen sada zumunta, yayin da mutane ke kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Al’umma da dama sun bayyana damuwarsu kan yadda batun bacewar Dadiyata ya dade yana jan hankali ba tare da samun cikakken bayani daga hukumomi ba. Wasu kuma na ganin wannan sabon zargi zai iya bude wata kafa ta sake bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan wannan sabon zargi ba.

Website