KAWO TV PLUS
21/01/2025
Ƙungiyar masu amfani da wayar tarho a Najeriya ta yi barazanar shigar da ƙara kan ƙarin farashin kuɗin kiran waya
-
-
-
Wata ƙungiya da ke wakiltar masu amfani da wayar tarho a Najeriya ta yi barazanar maka gwamnatin ƙasar a kotu bayan da hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da ƙarin kuɗin kiran waya da kashi 50 cikin 100 daga ewatan Fabrairun wannan shekarar.
Shafin yaɗa labarai na Daily Post ta rawaito cewa shugaban ƙungiyar Adeolu Ogunbanjo ya ce ƙarin kuɗin ya yi yawa, saboda ƴan Najeriya na kokawa da tsadar man fetur da kuma farashin kayan masarufi. “Yayin da na fahimci kalubalen da ake fuskanta a fannin sadarwa, mun amince da ƙarin kuɗin da bai wuce kashi 5% zuwa 10% ba, idan hakan bai wadatar ba, ya kamata kamfanonin sadarwa su nufi kawsuwar musayar hannun jari damin tara kuɗaɗe'' In ji Ogunbanjo.
“Ƙarin Kashi 50% ya yi yawa, muna cewa ba mu yarda ba, ba abin yarda ba ne, duk abin da ya wuce kashi 10%, za mu kai ƙara kotu.
Amincewa da ƙarin kuɗin kiran wayar dai na zuwa ne shekaru 12 bayan da hukumar NCC ta amince da farashin a shekarar 2013.
17/01/2025
Al'ummar sunce a ruguje musu makarantar secondary ta basa so,
Ku biyomu gobe domin kallon cikikken rahoton
KAWO TV PLUS
18/11/2024
Ya kamata a kori shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC Farfesa Mahmood Yakubu sannan a yi wa dokokin zabe garanbawul
- Tsohon shugaba Cif Olusegun Obasanjo
KAWO TV PLUS
Click here to claim your Sponsored Listing.