AMR Hausa

AMR Hausa

Share

18/05/2026

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane da kuma ƴan ta’adda suna aikata hakan ne saboda neman kuɗaɗen da za su kare kansu daga matsin lambar gwamnati.

Gumi ya yi wannan furuci ne yayin da yake magana kan matsalar tsaro da ta addabi wasu sassan Najeriya, inda ya ce matsin da gwamnati ke lallaba musu yana sa su neman hanyoyin samun kuɗi domin ci gaba da rayuwa da kare kansu.

Sai dai kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ƴan Najeriya, inda wasu ke ganin kamar yana ƙoƙarin kare ayyukan ƴan bindiga da masu tada ƙayar baya, yayin da wasu kuma s**a ce yana ƙoƙarin bayyana tushen matsalar ne domin a samo mafita mai ɗorewa.

18/05/2026

Jam’iyyar PDP za ta tantance tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a ranar Talata a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya na jam’iyyar domin zaɓen 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa ɓangaren PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ne ya sanar da hakan, inda s**a ce Jonathan ne kaɗai ya nuna sha’awar neman tikitin takarar shugaban ƙasa a cikin tsarin tantancewar da ake yi yanzu.

Haka kuma, ana zargin wasu ƙungiyoyin magoya baya sun fara haɗa kuɗaɗe domin sayen fom ɗin takara ga Jonathan, lamarin da ya ƙara janyo ce-ce-ku-ce kan yiwuwar komawarsa siyasa bayan barinsa mulki a shekarar 2015.

Sai dai har yanzu Jonathan bai fito fili ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba.

17/05/2026

Ɗan Majalisar Jigawa Mafi Daɗewa a Kujera Ya Rasa Tikitin APC Bayan Shekaru 16

Wani babban sauyi na siyasa na ci gaba da bayyana a Jihar Jigawa bayan da ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Miga/Kaugama, Hon. Sa’idu Yusuf Miga, ya rasa tikitin tsayawa takara a jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027.

Hon. Miga, wanda ya shafe shekaru 16 yana wakiltar mazabarsa a Majalisar Tarayya, ya kasance ɗaya daga cikin ƴan majalisar da s**a fi daɗewa a kujerarsu a jihar ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Rashin samun tikitin nasa na zuwa ne yayin da ake ganin ana samun manyan sauye-sauye da sauyin fuska a siyasar jihar kafin babban zaɓen 2027.

16/05/2026

YANZU-YANZU: Yusuf Buhari Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani Na Kujerar Majalisar Tarayya Ta Sandamu, Daura Da Mai’adua

Yusuf Buhari, ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Sandamu, Daura da Mai’adua.

A sakamakon zaɓen, Yusuf Buhari ya samu ƙuri’u 5,849, inda ya kayar da abokin takararsa Hon. Auwal Lawal Daura, wanda ya samu ƙuri’u 21 rak.

Nasarar tasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓukan 2027 a jihar Katsina.
Daga Mutawakkil Gambo Doko

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address

Zawachiki
Kano
110001