Sir Wisdom II

Sir Wisdom II

Share

17/06/2026

MU NUTSU MU DUBA WAƊANNAN:

Duk kyawun surarka ko surarki, kana tuna cewa birrai 🦥🐒🦍ma suna burge masu zuwa zoo kallon su. Don haka ka daina tinƙaho

👌 Komai ƙarfin ka da girman jikinka bazaka kai kanka kabari ba, sai dai wasu su kaika.
Ka daina jiji da kai ɗan'uwa.

👌 Komai tsawonka ba zaka hango gobe ba. Don haka kayi haƙuri.

👌 Komai hasken fatarki, Koda yaushe zaki buƙaci haske idan kika shiga duhu don haka ki kiyaye.

👌Komai kuɗin ka da yawan motocinka, koda yaushe da kafarka zaka shiga ɗakin kwananka, domin haka ka zamto mai nutsuwa da daina ji dakai

Mu ɗauki rayuwa da sauƙi, rayuwa ba tada tabbass gajera ce.

KO MUN TAƁA LURA DA WANNAN:

🤔 MASJID 🕌 yana ɗauke da harufa 6 hakannan CHOCHI ⛪ shima

🤔 Kalmar QUR'AN yana ɗauke da harufa 5 hakannan shima BIBLE yana ɗauke da harufa 5.

🤔 Kalmar RAYUWA tana ɗauke da harufa 6 hakannan itama MUTUWA

🤔 Kalmar ƘIYAYYA tana ɗauke da harufa 7 hakannan itama SOYAYYA tana ɗauke da harufa 7.

🤔 Kalmar MAƘIYA na ɗauke da harufa 6 hakannan kalmar MASOYA tana ɗauke da harufa 6.

🤔 kalmar NASARA tana ɗauke da harufa 6 hakannan kalmar FAƊUWA itama harufanta 6.

Idan ka ɗauka cewa alarm ɗinka shine yake tashin ka daga bacci, gwada sanya alarm ⏰ ɗin a gefen gawa kaga ko zata tashi.

Don haka ikon Allah ne kawai ke tayar da kai daga bacci.

Ɗan'uwa ka yarda da Allah sannan ka yadda da ikon Allah wanda duk ya yarda da Allah wallahi bazai taɓe ba.

Ya Allah Ka gafatar mana ka daura mu bisa hanya data dace.

Allah Ya sa mu wanye lafiya.
Sir Wisdom II ...🖊️

14/06/2026

Fiye da gawarwakin mutane 650 ne a halin yanzu aka ajiye su cikin nitrogen mai sanyi, an daskarar dasu, tare da fatan cewa nan gaba fasaha zata iya farfaɗo dasu wata rana.

Kamfanonin cryonics sun adana kusan mutum 600 zuwa 700 haka, kuma sama da mutane 5,000 sun rigaya sunyi rajistar a ajiye su bayan mutuwarsu. 🤣

Haka kuma daruruwan dabbobi (musamman karnuka da kuliyoyi) an yi musu rajista

Ajiye cikakken jiki gaba ɗaya yawanci ana kashe kusan dala $200,000.

Wannan shine irin babban fatan da ya dogara da fasahar da yanzu ba ta ma wanzu ba sai nan gaba kuma watakila bazata wanzu ba.

Amma ga waɗanda s**a yi wannan zabin suna ganin hakan ya cancanci gwaji.

Mu kam sai dai muce: can gasu gada..🏃

Sir Wisdom II

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Kano