AHMAD MEDIA

AHMAD MEDIA

Share

12/01/2026

Real Madrid ta kori Alanso bayan Rashin Nasara da s**ayi a hannun bacalona jiya 🤔🤔🤔

11/01/2026

Bacalona ta zura Kwallo 3 yayin da madari take 2

karshen wasa..

31/12/2025

Da ɗumi-ɗumi: Peter Obi ya fice daga LP, ya koma jam’iyyar ADC.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Labour Party (LP) tare da komawa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Peter Obi ya bayyana hakan ne yayin wani taron siyasa, inda ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na sabon tsari da hangen nesa na ceto da gyara siyasar Najeriya, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

A cewar Obi, ya ɗauki wannan shawara ne bayan dogon nazari, yana mai jaddada cewa burinsa shi ne gina adalci, shugabanci nagari da tsarin siyasa mai amfani ga talakawan ƙasa.

Ƙetarewar Obi ta haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar nan, inda magoya bayansa ke kallon matakin a matsayin sabon babi na gwagwarmayar siyasa, yayin da wasu ke jiran ganin tasirin hakan a cikin jam’iyyun adawa.

Masu sharhi na siyasa na ganin wannan sauyi na iya girƙiza tsarin jam’iyyun Najeriya, tare da sake jefa haske kan yadda za a tunkari zaɓen 2027.

30/12/2025

Allah ya mu dace 👌👌🤫

30/12/2025

Bam ya tashi a babban asibitin Kebbi

Rundunar ‘yansanda a jihar Kebbi ta tabbatar da afkuwar fashewar bam da sanyin safiyar Talata a babban asibitin Bagudo, da ke karamar hukumar Bagudo ta jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya fitar a Birnin Kebbi.

Usman ya ce: “Muna son tabbatar wa mazauna yankin cewa an shawo kan al’amuran tsaro gaba ɗaya bayan wata babbar kara ta fashewa da ta auku a babban asibitin Bagudo da sanyin safiyar Talata, 30 ga Disamba.

“Ƙungiyar tsaro ta haɗin gwiwa wadda ta ƙunshi ‘yansanda, sojoji da ‘yan sa-kai ta kulle tare da tabbatar da tsaron yankin cikin gaggawa. Ƙwararrun jami’an EOD-CBRN suna wurin suna gudanar da cikakken bincike.

“Muna farin cikin sanar da cewa babu wanda ya rasa ransa. Duk da cewa wani gini a bangaren ma’aikata ya lalace, mazauna wajen sun riga sun fice lafiya.

“Kwamishinan ‘yansanda na jihar ya ƙara tura jami’an tsaro na musamman domin tabbatar da zaman lafiya da doka.”

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano Outlying?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kano Outlying
700001