Hausa.com
02/04/2026
Da ɗumi-ɗumi: ADC ta nemi a kori shugaban INEC, ta zargi shirin kafa ƙasa mai jam’iyya ɗaya
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta buƙaci a gaggauta sallamar shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), tana mai zargin cewa ana ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ADC ta bayyana cewa matakan da INEC ke ɗauka a baya-bayan nan na nuna alamun shirin murƙushe dimokuraɗiyya tare da rage damar sauran jam’iyyu a harkokin siyasa.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa wannan lamari na iya jefa ƙasar cikin babban rikicin siyasa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba. Saboda haka, ta nemi gwamnati da hukumomin da s**a dace su shiga tsakani domin kare tsarin dimokuraɗiyya.
ADC ta jaddada cewa dole ne a tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin zaɓe domin guje wa rikice-rikice da kuma tabbatar da wakilcin al’umma yadda ya kamata.
Tambaya a yanzu ita ce: Shin za a saurari wannan ƙira, ko kuwa rikicin siyasa zai ƙara tsananta a ƙasar?
29/07/2025
Dubban Ƴan Najeriya Sun Ci Alwahin Tabbatar Da Ganin Tinubu Ya Zarce A Zaɓen 2027, Cewar Dogonbauchi
A wani yanayi da ke nuni da yadda dubun-dubatar ƴan Najeriya s**a gamsu da kamun ludayin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu cikin shekaru biyu, yanzu haka dubban ƴan Najeriya sun ci alwahin yin duk mai iyuwa wajen ganin shugaban ƙasa Tinubu ya zarce a babban zaɓen shekarar 2027, in ji kwamishiniya a hukumar ƙidaya ta ƙasa reshen Jihar Kaduna, Hajiya Sa'adatu Garba Saa Dogonbauchi.
Dogonbauchi, wacce ɗaya ce daga cikin manyan jiga-jigan ƴan siyasa a Jihar Kaduna, ta bayyana haka ne ta cikin wata tattaunawarta da Dokin Ƙarfe TV, "Idan aka yi la'akari da ƙwazon shugaban ƙasa Tinubu a shekaru biyu za a ga cewa ya iya shawo kan matsaloli masu sarƙaƙiya sosai. Misali, a da man fetur yana wahalar samu kuma da tsada, amma yanzu duk da cewa da tsadar amma ya wadata, ba a shan wahala wajen nema da samunsa". Inji ta.
Ta ci gaba da cewa, "Sannan kuma, abinci ya wadata ana kuma samunsa a farashi mai sauƙi. Haka zalika takardun kuɗaɗe na Nera yanzu ba sa wahala saɓanin da inda ake shan wahala wajen samun (Cash)". In ji ta.
Haka kuma, shugaban ƙasa Tinubu ya samu nasarar hallaka manyan ƴan ta'adda da dama a gwamnatinsa. Ƴan ta'adda irin su:
1.Kachallah Ɗanbaleri
2. Kachallah Dogo Kwaddi
3. Lawalli Dodo
4. Kachallah Naguru
5. Kachallah Ɗanbabirki
6. Kachallah Hana-Zuwa
7. Kachallah Adamu
8. Halilu Sububu
9. Baleri Fukai
10. Modi Modi
11. Kachalla Mai Shayi
12. Kachalla Tsoho Lulu
13. Kachalla Makore
14. Bulak
15. Kachalla Tukur Sharme. Ire-iren waɗannan nasarori da shugaban ƙasa ke samar wa ƙasa, su ne s**a ba wa dubban ƴan Najeriya ƙaimi da ɗaura ɗamarar ganin ya zarce a zaɓen 2027". Cewar Dogonbauchi.
Me zaku ce?
28/07/2025
MSF Nigeria Suna recruitment👇👇
Credit; Talk with Hauwau Dahiru
06/03/2025
Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta yi tir da abin da ta kira cin zarafi da tauye hakkin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi, tare da bukatar a gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin.
06/03/2025
Jam’iyyar APC Ta Yi Watsi Da A.A. Zaura Da Inuwa Waya, Cewar Garba Kankarofi
Matashin ɗan siyasa a Jihar Kano, Garba Ubale Kankarofi ya koka da yadda jam’iyyar APC ta yi watsi da manyan jiga-jigan ƴan siyasa a Jihar Kano waɗanda s**a ba da gagarumar gudunmawa cikin harkokin jam’iyyar ta fannoni daban-daban.
"A cikin jam'iyyar APC ta Kano, sunayen Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura (A.A. Zaura) da Malam Inuwa Ibrahim Waya sun daɗe suna da tasiri. Sai dai abubuwan da s**a faru a baya-bayan nan sun mayar da su gefe, duk da gudunmawar da s**a bayar wajen ci gaban jam’iyyar". Ya ce.
Garba ya ci gaba da cewa "Zaura ya tsaya takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a zaɓen 2023 ƙarkashin APC, kuma an san shi da ayyukan alheri da hidimar jama’a. Lokacin zaɓen, ya bayar da tallafin kuɗi da na kayan aiki ga jam’iyyar. Amma duk da haka, APC matakin Jiha da na ƙasa ta yi watsi da shi. Wannan hali har ya jawo hankalin Peter Obi na jam’iyyar Labour Party, wanda ya yi yunƙurin jan Zaura zuwa tawagarsa. Wannan ya tayar da tambayoyi kan yadda APC ke kula da masu biyayya gare ta. Duk da gudunmawar Zaura, an bar shi a gefe, abin da ke nuna cewa wasu lokuta, biyayya da hidima ba sa taka rawar gani idan ana maganar yanke shawarar siyasa". In ji shi.
Kankarofi ya kuma ƙara da cewa: "Haka zalika, Malam Inuwa Ibrahim Waya, wanda ya nemi takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin APC, shi ma ya gamu da irin wannan ƙaddara. Waya, wanda ya fito daga kamfanin NNPC, ya nuna sha’awarsa ta yin takarar gwamna a 2022 da 2023.
Sai dai gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zaɓi mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin dan takarar gwamna na APC. Wannan matakin ya mayar da Waya gefe. Duk da cewa bai yi bore ba, ya bayar da gudunmawa ga kamfen ɗin APC ta hanyar ba da ofishin yaƙin neman zabensa, wani ɗakin taro mai ɗaukar mutum 10,000, da kuma tallafin Naira miliyan 50 ga tawagar kamfen ɗin Gawuna-Garo". Ya ce.
Ya kuma ƙara da cewa "Tun bayan zaɓen 2023, Waya ya daina fitowa fili a harkokin siyasa. Ba a cika jin shigarsa a kafafen sada zumunta ko shirye-shiryen rediyo kamar da ba, abin da ke nuna yiwuwar ya janye ko yana jin takaici da watsi da aka yi da shi". In ji shi.
Ubale ya kuma ƙara da cewa "Halin da Zaura da Waya s**a tsinci kansu a ciki yana nuna matsalar da ke cikin APC. Duk da irin gudunmawar da s**a bayar, jam’iyyar ta watsar da su. Wannan yana tayar da tambayoyi kan kimar biyayya da kuma yadda APC ke kula da waɗanda s**a ba da gudunmawa ga nasararta. Makomar Zaura da Waya na nan cikin duhu". Cewar Garba Ubale Kankarofi Daga Kano.
06/03/2025
AN DAKATAR DA SANATA NATASHA WATANNI 6 KUMA ZA KATSE MATA ALBASHI
Majalisar Dattijai ta dakatar da Sanata Natasha mai wakiltar Jihar Kogi ta tsakiya daga halartar majalisar na tsawon watanni 6.
Haka ma zaa katse mata ALBASHI na tsawon watanni 6, zan Kuma a janye mata hadimai, kuma zata rubuta takardar bayar da hakuri a gaban majalisar.
Wannan ya biyo bayan yin watsi da korafe-korafen da Sanata Natasha ta shigar a gaban majalisar kan zargin Shugaban majalisar Dattijai Godswill Akpabio, cewar yana bibiyar ta.
Wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahotan bincike da kwamitin da'a da aka kafa karkashin Sanata Sanata Neda Imasuen, bayan daya kafa hujja da doka mai lamba 40 na kudin tsarin mulkin majalisar.
06/03/2025
WATA SABUWA: China Ta Gargadi Amurka Cewa A Shirye Take Ta Yi "Kowane Nau'i" Na Yaki Bayan Bugun Ƙirjin Kasuwancin Shugaba Donald Trump Na Karuwa Jadawalin Kuɗin Fito
HAUSA.COM
21/10/2024
Babban Daraktan Kamfanin Sadarwa na Najeriya, Sule Abdulaziz, ya bayyana cewa Najeriya ke samar da wutar lantarki na sa’o’i 24 ga kasashen Togo da Benin, Kuma Suna biya
21/10/2024
Gwamnatin Jihar Kaduna ta rushe gidan wata dattijiya dake Kaduna da aka kàshè mata yara 5 a Zariya cikin shekarar 2015 Almajiran Sheikh Zakzaky Hajiya Jummai Ahmad Karofi.
21/10/2024
Sanata Kwankwaso Jagoranmu ya Gina Rayuwar Bil'adama da ba zamu iya biyan sa ba -Gwamna Abba
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya karrama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) a zaben 2023, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso a bikin cikarsa shekaru 68 da haihuwa.
A sakon taya murna ga shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Gwamna Yusuf ya yaba da ingancin shugabancin Kwankwaso da kuma tasirin siyasar da ta shafe tsawon lokaci da numfashin kasar nan.
Sanarwa daga Sanusi Ahmad Bature Dawakin-Tofa, mai magana da yawun gwamnan ya bayyana Sen. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin babba kuma jagora wanda ya gina miliyoyin shugabanni a duk wani aiki na dan Adam.
A cewar Gwamnan ga Kwankwaso "A cikin shekaru 38 na san ku kuma na yi aiki tare da ku. Na ɗauki darussa masu mahimmanci na rayuwa da gogewa. Lallai kai alama ce ta gaskiya, sadaukarwa da hidima ga mutane.
Hikimar ku ta siyasa ta yi tasiri ga al'umma, ta zaburar da shugabanni masu nagarta, kuma sun ba da gudummawa sosai ga bil'adama. Lalle ne kai mai karfi ne da ba za a iya tantama a siyasar Najeriya ba, kuma ka kware a siyasar Arewa."
“A cikin tafiya ta hidima ga bil’adama, kun rike mukamai da s**a hada da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Gwamnan Jihar Kano, Ministan Tsaro, Wakilin Musamman a Darfur da Somaliya, Sanata Tarayyar da Dan takarar Shugabancin kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023.
"A madadin kai na, dangi, gwamnati na al'ummar jihar Kano, ina yi muku fatan karin shekaru masu hidimtawa bil'adama a Najeriya fiye da haka". Sanarwar ta karanta.
21/10/2024
Gwamna Abba K. Yusuf ya halarci shirin Jami'ar Skyline CSR domin murnar cika shekaru 68 da haihuwar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
21/10/2024
Da dumi'dumi: Gwamnatin Tarayya ta Bai wa Daliban Najeriya Lamunin Naira Biliyan 11bn.
Asusun bayar da lamunin ilimi a Najeriya NELFUND ya sanar da cewa zuwa yanzu, ya raba rancen kimanin Naira biliyan 11 ga dalibai domin tallafa wa ilimi a kasar.
Shugaban hukumar, Akintunde Sawyerr ne ya bayyana haka yayin wata hira da Gidan Talabijin na Arise inda yake bayyana kudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na ganin an sami sauki a harkar Ilmi
Sawyerr ya jaddada cewa ba za a bukaci wadanda s**a ci gajiyar lamunin su biya bashin ba har sai bayan sun kammala bautar kasa da shekaru biyu ko kuma sun sami aikin yi.
Sannan tsarin biyan lamunin a cewarsa, zai biyo ta hanyar zare wani kaso da bai taka kara ya karya ba daga albashin mai dauke da bashin a kowane wata cikin ƙayyadadden lokaci
Sawyerr ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne da nufin sassauta jin nauyi akan masu dauke da bashin da ba su riga sun sami aikin da zai biya musu bashin ba
Idan ba a manta ba, Gwamnatin Shugaba Tinubu ta kirkiro shirin bayar da lamunin Ilmi ga ɗaliban da s**a cancanta, wanda zai ba su damar neman ilimi mafi girma ba tare da sun shiga matsalar neman kuɗi ba.
Baya ga daliban Ilmi NELFUND ta sake jaddada aniyar ta ta tallafa wa fannin ilimin kirkira ga matasan Najeriya, da kuma samar masu da ayyukan yi.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Kaduna
24
Opening Hours
| Monday | 09:00 - 17:00 |
| Tuesday | 09:00 - 17:00 |
| Wednesday | 09:00 - 17:00 |
| Thursday | 09:00 - 17:00 |
| Friday | 09:00 - 17:00 |
| Saturday | 09:00 - 17:00 |
| Sunday | 09:00 - 17:00 |