Labari Da Gaskiya

Labari Da Gaskiya

Share

Photos from Labari Da Gaskiya's post 21/04/2026

Da Dumi Dumi: Mutane Sun Kauracewa Taron Gan Ganin Zaɓen Shugabannin Jam Iyyar ADC Ɓangaren Hon Nafi'u Bala A Garin Abuja A Wannan Safiya.

21/04/2026

Gwamnati Ta Bude Shafin Tallafin Karatu Na PTDF Ga Daliban Injiniya

Hukumar Bunƙasa Fasahar Man Fetur (PTDF) ta sanar da buɗe shafin neman tallafin karatu na shekarar 2025/2026 ga ɗaliban da ke karatun aikin injiniya da sauran fannoni masu alaƙa da harkar man fetur a jami’o’in Najeriya.

Hukumar ta buɗe shafin ne a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2026, inda aka tsara rufe karɓar rejista a ranar Juma’a, 29 ga watan Mayu, 2026.

Wannan tallafi ya shafi ɗaliban da ke matakin digiri na farko (Undergraduate) da kuma masu neman digiri na biyu da na uku (Postgraduate). Manufar shirin ita ce ƙarfafa kishin gida da samar da kwararru a fannin fasaha don rage dogaro da masana daga ƙasashen waje.

Masu sha’awa za su iya rejista ta shafin: https://scholarship.ptdf.gov.ng

Hukumar PTDF ta fitar da matakai guda goma da ya k**ata masu nema su bi:
1. Buɗe Akawun: Ziyarci shafin tallafin, sannan ka samar da akawun ta hanyar shigar da bayananka. Za a turo maka sako ta imel don tabbatarwa.
2. Shiga Shafin (Login): Yi amfani da imel da kalmar sirri (password) don shiga shafin akawun dinka.
3. Tabbatar da Lambar NIN: Wajibi ne mai nema ya tabbatar da lambar sa ta shaidar ɗan ƙasa (NIN). Hukumar ta yi kashedin cewa idan aka samu matsala wajen tantancewa, kada a riƙa maimaitawa akai-akai don gudun asarar kuɗi; k**ata ya yi a tuntuɓi sashen taimako.
4. Yarda da Sharuɗɗa: Dole ne ka karanta sannan ka amince da sharuɗɗan shirin kafin ka ci gaba.
5. Cike Fom: Shigar da dukkan bayanan da ake buƙata cikin kwarewa da gaskiya.
6. Zaɓar Karatu da Jami’a: Zaɓi jami’o’i da darusan da kake son karantawa (na farko, na biyu, da na uku). Masu neman digiri na biyu da na uku za su loda takardar bayyana manufar karatu (Statement of Purpose) ko shawarar bincike (Research Proposal).
7. Ɗora Takardu: Ana buƙatar takardar shaidar karatu, takardar haihuwa, da ta ɗan ƙasa da jiha. Dole takardun su kasance cikin tsarin PDF kuma girmansu bai fi 300KB ba.
8. Ƙarin Takardu: Za ka iya loda takardun kasancewa dan daya daga ƙungiyoyin kwararru idan kana da su.
9. Duba Bayanan da aka shigar: Tabbatar ka duba dukkan bayanan da ka shigar don gyara kura-kurai kafin ka tura.
10. Tura bayanai: Da zaran ka tura, ba za ka iya sake gyara komai ba. Don haka, a tabbatar komai ya kammala kafin dannawa a tura.

Wannan tallafi na cikin gida (In-country scholarship) ya bambanta da wanda ake fita ƙasashen waje don yi. Tallafin yana rufe kuɗin makaranta, kuɗin alawus na wata-wata, da kuma samar da kayan karatu ga ɗaliban da s**a yi nasara bisa cancanta.

Hukumar ta jaddada cewa wannan yunkuri wani ɓangare ne na dabarun gwamnatin tarayya na haɓaka jarin bil-adama a fannin mak**ashi na ƙasa.

20/04/2026

Ma’aikatar Kuɗi Ta Karyata Zargin Ɓoye Kuɗaɗen Shiga Na Kasa

Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta mayar da martani kan wasu rahotannin kafafen yada labarai da suke ikirarin cewa ana karkatar da kuɗaɗen shigar ƙasa ko kuma ana yin “ɓoyayyen kashe-kashe.”

Wadannan rahotanni sun biyo bayan fassarar da aka yi wa sabon rahoton Bankin Duniya (World Bank) kan tattalin arzikin Najeriya.

Ma’aikatar ta bayyana cewa wadannan rahotanni ba gaskiya ba ne, kuma sun samo asali ne daga rashin fahimtar yadda tsarin kasafin kuɗi da rabon kuɗi yake aiki.

Ina Kuɗaɗen FAAC Suke Tafiya?

Ma’aikatar ta fayyace cewa kudaden da ake cirewa daga asusun tarayya (FAAC) ba ɓataccen kuɗi ba ne. Ana amfani da su ne wajen kashe-kashen da doka ta amince da su da s**a haɗa da; Zuba Jari da Tanadi Don samar da gobe mai kyau; Harkar Tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya; Kuɗin da ake bai wa hukumomin tara haraji; Turawa ma’aikatu da rassa (MDAs) kuɗaɗen da ya k**ata a mayar musu.

Ma’aikatar ta jaddada cewa tura wa jihohi da sauran matakan gwamnati kuɗaɗe ba wai sace su ba ne; harka ce ta tsarin mulki da ya wajaba a biya.

Sanarwar ta zargi wasu masu sharhi da amfani da tsoffin bayanai yayin da s**a yi kunnen uwar shegu da sabbin gyare-gyaren da gwamnati ta fito da su a farkon shekarar 2026.

"Dokar da Shugaban Ƙasa ya sanya wa hannu kwanan nan don kare kuɗaɗen man fetur za ta ƙara gaskiya a harkar kuɗi, kuma ana sa ran za ta ƙara kudaden da ake rabawa da kimanin kashi 0.4% na arzikin kasa (GDP) a kowace shekara."

Ma’aikatar ta bayyana cewa babban sakon rahoton Bankin Duniya shi ne cewa Najeriya na kan hanya madaidaiciya. Ga wasu daga cikin nasarorin:
1. Haɓakar Tattalin Arziki: Bangarori daban-daban na bunkasa.
2. Saukar Farashin Kaya: Ko da yake har yanzu akwai tsada, matakan da ake dauka sun fara rage radadin hauhawar farashi.
3. Rage Basuss**a: A karon farko cikin shekaru goma, bashin da ake bin Najeriya idan aka kwatanta da arzikin ƙasa ya ragu.

Gwamnatin Tarayya ta ce tana nan kan bakarta na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkar kuɗi. Ta bukaci manema labarai da jama’a da su rika tantance bayanai kafin yadawa don gudun janyo rudani a kasa.

Photos from Labari Da Gaskiya's post 20/04/2026

A RANAR 18/4/2026❤️❤️❤️

Shugaban Wannan Kafa Mai Suna Dr Abdullahi Dahiru Yasamu Karuwa Na Aure Tareda Matarsa Halima Shafi'u Baby"

Sakon Godiya Ga Mahalarta Wannan Biki, Dafatan Kowa Yaje Gidansa Lafiya, Allah Muke Roko Yabasu Zaman Lafiya Da Karuwar Arziki"

Daukan Hoto~ Hafsat Yusuf Jibia.

19/04/2026

NELFUND Ta Biya Wa Daliba 6,385 na Jami’ar Lafiya Kudin Makaranta Miliyan 795

Hukumar bayar da lamuni ga dalibai ta kasa (NELFUND), ta fitar da kudi har naira miliyan dari bakwai da casa’in da biyar da dubu dari bakwai da ashirin da tara da dari biyar (₦795,729,500) domin biyan kudin karatun dalibai dubu shida da dari uku da tamanin da biyar (6,385) na Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafiya (FULafia), Jihar Nasarawa.

Hakan na ƙunshe cikin wata wasikar godiya da jami’ar ta aika wa hukumar ta NELFUND mai dauke da sa hannun Shugaban Jami’ar (Vice Chancellor), Farfesa Mohammed Isa Kida.

A cikin wasikar, jami’ar ta nuna cewa an turo kudaden ne kashi uku tsakanin watan Fabrairu da Maris na wannan shekara k**ar haka:

A ranar 16 ga Fabrairu, 2026, ta biya wa dalibai 4,563 Naira 565,249,500; sai ranar 24 ga Fabrairu, 2026 da aka biya wa ɗalibai 636 Naira 82,189,000; sai kuma 3 ga Maris, 2026 da aka biyawa ɗalibai 1,186 Naira 148,291,000. Jimillar adadin ɗaliban ya k**a 6,385 wanda aka biya musu Naira 795,729,500.

Farfesa Isa Kida ya bayyana jin dadinsa da kuma yabawa hukumar kan yadda take gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da rikon amana. Ya ce wannan tallafi babban abin farin ciki ne ga daliban jami'ar, domin zai share musu hawaye tare da basu damar ci gaba da karatunsu ba tare da fargabar kudin makaranta ba.

"Tasirin da NELFUND ke yi a rayuwar dalibanmu ba abin da za a iya kwatantawa ba ne. Mun gode kwarai da gaske kan sadaukarwarku wajen bunkasa ilimi a Najeriya," in ji shi.

Wannan tallafi na zuwa ne a karkashin shirin "Renewed Hope" na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin tabbatar da cewa babu dalibin da ya rasa damar yin karatu saboda rashin hali.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

No 7 Ado Gwaram Rigasa Kaduna
Kaduna