Unity Media

Unity Media

Share

05/06/2026

Allah ya yi wa Malam Sadik Pharmacy Gombe rasuwa, bayan fama da jinya da ya yi.

Al'ummar Musulmi, musamman daga Arewacin Najeriya, sun shiga alhini bayan samun labarin rasuwar marigayin, wanda ya kasance matashin malamin addinin Musulunci, tare da kwarewa a fannin magungunan Musulunci da kuma bayar da shawarwari kan gyaran zamantakewar iyali.

Ubangiji, Allah Ya gafarta mi shi.

04/06/2026

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo, ta cafke wani mutum mai shekaru 38, Nsikak Kingsley, bisa zargin dukan mahaifinsa har lahira a yankin Oda da ke karamar hukumar Akure ta kudu a jihar.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abayomi Jimoh ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne bayan wata gardama tsakanin wanda ake zargin da mahaifinsa, Adone Peter mai shekaru 65, wacce ta rikiɗe zuwa fada.

Binciken farko ya nuna cewa a ranar 28 ga watan Mayun 2026, Kingsley ya kai wa mahaifinsa hari tare da yi masa munanan raunuka, musamman a kai.

Daga bisani an garzaya da wanda abin ya shafa asibiti domin samun kulawar likitoci. Sai dai duk da kokarin ceto rayuwarsa da ma’aikatan lafiya s**a yi, likita ya tabbatar da mutuwar tsohon yayin da ake masa magani.

04/06/2026

CIKIYA! CIKIYA! CIKIYA! CIKIYA! CIKIYA!

Ana cikiyar wannan baiwar Allah mai suna FATIMA IBRAHIM wacce ake kira da UMMI, wacce ta ɓata tun kwanaki 2 da s**a gabata.

Fatima dai ƴar kimanin shekaru 10 ce, sannan ta fita ne daga gidan su dake Anguwan Rogo bayan jeji a nan Jos sanye da doguwar rigar less mai launin “golden”.

Mai ɗan matsakaicin tsayi da jiki ce.

Idan Allah Ya sa wani ya ganta ko ya ji labarin inda FATIMA ta ke, a dubi girman Allah a tuntuɓi wannan lambar: 07015898279.

A taya mu da tura wannan saƙo har ko da Allah zai sa saƙon ya isa inda Fatima ta ke.

Mun gode.

CIKIN SHEKARU BIYU: ƊALIBAI DA MALAMAI SAMA DA 600 AKA SACE DUK DA SHIRIN TSARON MAKARANTU NA NAIRA BILIYAN 145 04/06/2026

Aƙalla ɗalibai da malamai 603 ne aka yi garkuwa da su a hare-hare bakwai da aka kai wa makarantu a jihohi daban-daban na Najeriya tsakanin watan Maris na shekarar 2024 zuwa Mayun 2026.

CIKIN SHEKARU BIYU: ƊALIBAI DA MALAMAI SAMA DA 600 AKA SACE DUK DA SHIRIN TSARON MAKARANTU NA NAIRA BILIYAN 145 Rahotanni sun nuna cewa aƙalla ɗalibai da malamai 603 ne aka yi garkuwa da su a hare-hare bakwai da aka kai wa makarantu a jihohi daban-daban na Najeriya tsakanin watan Maris na shekarar 2024 zuwa Mayun 2026. Wannan na zuwa ne duk da aiwatar da shirin “Safe Schools Initiative” na gwamnatin tar...

Want your business to be the top-listed Media Company in Jos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


No 62, Zinaria Hill Layout Jos, Plateau State
Jos