Shuwarin Development Association-SHUDA
28/03/2026
DOMIN SANAR DA AL'UMMAR GARI!
A cikin 'yan watannin da s**a gabata, bayan samun sahihan bayanai game da zargin niyyar raba filin lambun Shuwarin na dab da Gidan Tsika (kadarar alumma ta ƙarshe da ta rage a cikin garin Shuwarin) ga wasu mutane, wannan Ƙungiya ta dauki matakin gaggawa ta hanyar tuntuɓar duk masu ruwa da tsaki. Daga baya, Ƙungiyar ta nemi ganawa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Kiyawa domin gabatar da damuwarta da kuma tattauna al'amarin cikin manufar ƙubutar da wannan wuri da ya rage a cikin kewayen garin.
Shugaban Ƙaramar Hukuma a wancan lokacin ya tabbatar mana da cewa shi da kansa bai amince da wannan shirin ba, kuma cewa wannan ƙoƙari na wasu mutane ne masu son rai da neman amfanar da kansu kadai. Har ila yau, ya tabbatar wa Ƙungiyar da cewa zai jajirce wajen farfaɗo da lambun, wanda ya haɗa da gina shinge a kewaye shi, shuka ƙarin itatuwan da suke da amfani wajen tattalin arziki, samar da borehole don bayin ruwa, da kuma ɗaukar ma’aikatan wucin gadi don kula da lambun a kowace rana.
Abin takaici, a cikin 'yan kwanakin da s**a gabata, mun lura da ja da baya daga wannan alkawari. Sahihan bayanai sun nuna cewa an sake farfado da yunkurin yanka lambun kuma yanzu ana ƙoƙarin aiwatar da shi, wanda wani wakilin Ƙaramar Hukumar ke jagoranta. Wannan yunkurin ya kasance abin bakin ciki da takaice, duba da la’akari da alkawarin da akayi na farfado da shi amfanin dukkanin alummar garin Shuwarin da ma ita kanta karamar hukumar. Ƙungiyar SHUDA, shugabanninta, da sauran masu muradin alkairi ga Shuwarin sun kasance kan rashin amincewa da wannan yunkurin.
Wannan sanarwa an fitar da ita ne don sanar da alumma halin da ake ciki tare da kuma jan hankalin duk wani mai ruwa da tsaki.
Muhammad Sunusi Hussain
Sakatare
SANARWA SANARWA,
KIYAWA LGA.
Gobe Juma'a 13-11-2025, za'a tantance mata masu sha'awar shiga Shirin Foundation Year Program (FYP).
Ma'ana Karatun JINYA da Kuma UNGOZOMA na Jihar Jigawa, karamar Hukuma KIYAWA.
Da Misalin 9:00am. Insha Allah.
A cikin sakateriyar mulki dake karamar Hukuma ta Kiyawa.
WAJIBABBUN ABUBUWAN DA AKE BUKATA SUNE:-
- SSCE daga 7-9 credit a bangaran kimiya (SCIENCE), Wanda ya hada da English, Maths, Physics, Chemistry, da Kuma Biology.
-Takardar shedar karamar Hukuma (INDIGINE).
-Takardar shedar katin Dan kasa (NIN).
-Original copy da Kuma Photocopy na takardun.
Allah ya bada sa'a.
Domin karin bayani a tuntubi.
Mushaffau Aliyu
Coordinator Danmodi Student care Kiyawa local Government.
08132112961.
07/09/2025
SHUDA OFFICIAL!
Wakilan SHUDA sun gana da Shugaban Karamar Hukumar Kiyawa.
Wakilan sun tattauna batun Samar da Batiran Solar da aka sace a asibitin Shuwarin inda maigirma Shugaban Karamar Hukuma Hon. Abdulhamid yayi alkawarin Samar da Batiran a cikin kankanin lokaci duba da tasirin da Solar ke dashi wajen gudanar da aiyukan asibitin.
Tun da farko Wakilan karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kiyawa Hon. Adamu Muhammad Adamu sun mika wa Shugaban Karamar Hukumar takarda Mai dauke da kira ga Shugaban Karamar Hukumar da ya sahale tare da bada gudunmowa wajen farfado da Lambun Gwamnati (Orchard) da yake Unguwar Gidan Tsika.
Shugaban ya Nuna Jin Dadin sa da wannan yunkurin tare da yin alkawarin turo kwamiti daga Karamar Hukuma Dan yin aiki tare da kungiya Dan rayar da wannan Lambu.
Muna adduar Allah Ya tabbatar mana da wadannan aiyukan tare da sauran ayyukan alheri da muke nema ga Al'ummar mu da Garinmu.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the organization
Website
Address
Jigawa