Mufty Bakery

Mufty Bakery

Share

Photos from Mufty Bakery's post 04/12/2025

Africa Muna Da Ingantattun Abinci. 🌮🍵☕

01/11/2025

Big shout-out to my newest top fans! Ummu Husna MB, Ummasalama Abdullahi, Hauwa Adado

Photos from Mufty Bakery's post 11/09/2025

Assalamu Alaikum.
Kamar Yanda Na Alkarwanta Ranar Asabar Zan Zo Da Cikakken Wannan Recipe. Sannan Kuma Ina Son Kowa Yayi Mention Mutum Biyu Kadai Daga Cikin Friends (Abokai) Dinsa A 'Kasan Comments Na Wannan Rubutun. Domin Hakan Zai Sa Masu Amfanar Abubuwan Da Mu Ke Kawowa A Wannan Gida Na Mufty Bakery Su Kara Yawaita.
WHEAT BISCUIT RECIPE.

1- Wheat Flour - 1 Cup ( 150g)
2- Sugar - 1/2 Cup (100g)
3- Butter - 2 Tsb
4- Salt - Kadan
5- Mai Na Soyawa (Wadacce)
YANDA ZA A HADA (METHODS).
MATAKI NA - 1
A cikin Mazubi mai fadi haka, za a zuba Wheat Flour, Sugar, Salt (Gishiri), sai kuma Butter. To daga nan sai a juya su a tare na yanda za su hade su zama abu guda. ( Kamar dai yanda ake yin Pastry Powder).
MATAKI NA - 2
Za a zuba ruwa kadan a cikin wannan hadin. Sannan sai a yi Kneading dinsa har zuwa lokacin da aka ga ya zama dough mai laushi.
MATAKI NA - 3
Za a sanya Dough din a cikin wani Mazubin haka, sannan sai a rufe a kuma barshi har na tsahon mintuna kamar sha biyar (15).
MATAKI NA - 4
Bayan mintuna Sha Biyar din nan, sai a fito dashi daga cikin Mazubin da aka sanya, sannan sai a dora shi akan Table, sannan akan Table din a tabbatar an yayyafa Flour a kai, sannan sai a dauko Rolling Pin (Rolling Stick) sai a murza yayi fadi. Sannan sai a dauko Cookise Cutter a yayyanka da shi iya Size din da ake muradin ya fito.
MATAKI NA - 5
Idan an kammala yin hakan, to Cookies ya hadu, sai kuma Soyawa ya rage kawai. Za a dora Mai a kan Wuta bayan an zuba a cikin Kaskon Suya, sannan Wutar da zamto ba a hura ta tayi yawa sosai ba. Idan Mai din yayi zafi za a Soya Bescuit din a cikin Mai din a tsahon Muntuna Biyar, ko Takwas (5-8). Ko ma dai zuwa lokacin da aka fahimta da Biscuit din ya sauya launi zuwa Brown Clour haka. To sai a tsame daga cikin Mai a kuma barshi ya tsane.

Za A Iya Ci Da, Shayi, Lemo, Yoghourt, Ruwa, A Hakansa Ma Yana Da Dadi Sosai. Da Dai Sauransu. Mufty Bakery Na Ku Ne
http://www.muftybakery.com.ng/
DAGA SHAFIN MUFTY BAKERY.🎂🍝🍮🍯🍦

Want your business to be the top-listed Bakery in Ikeja G. R.a?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address

Ikeja G. R.a