Idris yahuza

Idris yahuza

Share

Photos from Idris yahuza's post 09/04/2026

Kamar yadda nayi alƙawari,
Wannan shine Babban asibitin da yake Kula da alummar garuruwa guda biyar (5)
• Gidandallah
•Kaziyeta
•Zubarau
•maƙerayi da kuma
•tsurutawa
Duk a mazaɓar Auyo Karamar hukumar Auyo. Wannan asibitin yaɗauki tsawon Shekaru a haka Amma abin mamaki Har awun Mata masu juna biyu akeyi a wannan asibitin sakamakon ƙarin ma aikaciyar jinya mace damuka Samu (nursing) ta wannan Fannin Munci gaba.
Haka zalika tun Sama da shekara Goma (10) Akeda buƙatar canzawa wannan asibitin matsugunni sakamakon cigaba da akasamu na ƙaruwar jama'a dakuma Gine gine Hakan tasa asibitin yashiga Lungu.
mafi yawancin mutane Sai sunyi tambaya Idan sunzo asibitin.
Muna ƙira ga alummarmu da muyi iyakar ƙokarinmu don ganin munkawo sauyi ga rayuwar alummarmu.
Hakan kuwa bazai samuba Saimun ajiye komai munsa alummarmu agaba.
Muna ƙira da Babbar Murya ga shugabannin mu dasuyi abinda yadace ga alummarmu.
Magana ta zahiri matsugunni muke buƙatar canzawa wannan asibitin Mai ɗumbin tarihi.
© Idris yahuza

08/04/2026

Insha Allahu gobe zanyi rubutu akan asibitin da yaƙunashi waɗannan garuruwa Kamar haka!
1, Zubarau
2, gidandallah
3, Kaziyeta
4, Maƙerayi
5, Tsurutawa

Photos from Idris yahuza's post 08/04/2026

Kamar yadda nayi alƙawari jiya wannan sune azuzuwan makarantar gidandallah primary school wacce taɗau tsawon shekaru ahaka ba'a gyara ba Kuma ba niyyar gyara.
Tsawon Shekara goma Inna koyarwa fisabilillahi a wannan makarantar tun alokacin tsohon gwamna Alh Sule lamiɗo har izuwa ƙarshen Mulkin Alh Abubakar badaru nayi iyakar ƙokarina ganin angyra wannan makarantar. Lokacin Inna Maga takardar maliman sakai na Karamar hukumar Auyo (Secretary) alokacin munyi nasarar samun ƙarin block ɗaya Mai ɗauke da azuzuwa guda uku awannan makarantar azamanin tsohon gwamna Alh abubakar badaru Amma abin takaici shine tunda akayi wannan block Mai dauke da azuzuwa guda uku Har s**a Mutu ba'a sakamusu kujera Ko guda ɗayaba.
Ai'na matsalar take alokacin Muna zama da ƙungiyar SBMC ta makarantar Kuma ana samun cigaba sosai alokacin Domin Duk ajinda yake wannan makarantar kullum akatashi Daga darasi za'a kulle kowanne Aji zuwa yamma maliman islmiyya subuɗe suyi nasu karatun Duk Hakan yanada nasaba da SBMC dakuma wancan shugaban makarantar.
Alokacin Alh Jibrin yayi Iya bakin ƙokarinsa na ganin anyi gyara a wannan makarantar Domin yaturo anɗauki Hoton makarantar nan yakai Karo uku awannan lokacin Amma abin baiyi tasiriba.
Don haka innaso insanar daku bawanda Zai nemamana mafita saidai muɗin damukaja jiki gefe.
Matasanmu mufarka muajiye aƙidar siyasa munemawa kanmu mafita.
Mu wayar da Kan manyanmu da matanmu da Duk Wani Wanda mukega Zai bamu gudun mawa.
@ Idris yahuza

07/04/2026

Babu wata alaka tsakaninmu da wannan masu magagin faduwar don naga yaron da s**a saka yayi ta zagin manyan Jigawa da yi musu shagube tsawon shekara uku ya saka hoton Jagoranmu da fusataccen mai gidansu yana cewa ga yadda lissafin yake.

A fadawa mai takurarriya hula cewar ya rubuta handover dinsa ya ajiye kurum. Wa'adinsa zai cika a 2027 da yardar ubangiji.

Photos from Idris yahuza's post 07/04/2026

(((Dakai nake Dan media)))
Kasancewarka dan Media kada ka kaɗaita da siyasa kayi ƙoƙari ka daga muryarka inda kaga ana zalunci da take haƙƙin alumma da kuma nema musu mafita a rayuwa ta hanyar data dace bisa doka da lumana.
Duk abinda zakayi kayi bincike ka gano gaskiya kafin ka yaɗa don kada ka ɗaga hankalin alumma.
Alumma suna fama da rashin wuta,ko ruwa, ko matsalar tsaro a kauyenku,karamar hukumarku ko yankinku ka ɗaga murya don jawo hankalin hukuma da wadda abin ya shafa don a ɗauki matakai.
Ka taimaki alumma ta hanyar dakake taimakon siyasarka. Kaɗan Daga cikin aikin jagoranmu Dr Sula Lamiɗo

07/04/2026

Duk wanda ya buɗe ƙofar karɓar gyara a lamuransa na rayuwa, gobensa za ta yi kyau, jibinsa kuwa za ta fi gobensa kyau.
karɓar gyara ba ƙasƙanci bane mataki ne zuwa ga nasara.

06/04/2026

Sule lamiɗon dai

06/04/2026

Ka tashi ka nemi kuɗi har sai ka fara zuwa baƙunta ana cewa,

Shigo da takalminka ciki, kai fa baƙo ne na musamman, 😄
to ka sani ka fara samun kuɗi 😂

06/04/2026

Memories for get together

Photos from Idris yahuza's post 22/03/2026

Idris yahuza
Hassan yahuza
Abdullahi yahuza
Nayi muku barka da sallah

11/08/2024

Website