AAC Zamfara STATE Chapter
CONDOLENCE MESSAGE TO THE EMIRATE COUNCIL AND THE GOOD PEOPLE OF GUSAU AND ZAMFARA STATE
The African Action Congress (AAC), Zamfara State Chapter, extends its deepest condolences to the Gusau Emirate Council, the entire people of Gusau, and Zamfara State at large, over the passing of our revered father, His Royal Highness Alhaji Ibrahim Bello, OFR, the Emir of Gusau.
His Royal Highness was a father to all, whose reign brought stability, guidance, and a deep sense of pride to the people of Gusau and beyond. His contributions to traditional leadership and community development will never be forgotten.
We pray that Almighty Allah (SWT) grants him Aljannatul Firdaus, and gives his family, the Emirate Council, and the good people of Zamfara the strength and patience to bear this great loss.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Signed:
African Action Congress (AAC)
Zamfara State Chapter
06/06/2025
23/01/2025
*Zuwa ga Matasa Masu Kishin Kasa da jahar zamfara*
Daga: Shugaban Jam’iyyar African Action Congress (AAC), Jihar Zamfara
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.
Bayan gaisuwa da fatan alheri, ina rubuto wannan wasika ce domin jan hankalin ku, matasa, masu jini a jika da kuma kishin al'umma, akan muhimmancin shiga jam'iyyar African Action Congress (AAC) domin ceto al'umma daga kangin bautar da suke ciki.
A matsayinku na matasa, kuna da karfi, hangen nesa, da ilimin da zai iya kawo sauyi a harkokin shugabanci da cigaban kasa. Amma wannan ba zai yiwu ba sai mun hada kai domin tsaida nagartattun mutane da za su shugabance mu ta hanyar gaskiya da adalci.
Jam'iyyar African Action Congress (AAC) tana da tsari mai karfi da manufofi na kawo sauyi mai dorewa ga al'umma, ta hanyar tabbatar da shugabanci nagari wanda zai yaki zalunci, cin hanci, da rashawa. Don haka, muna bukatar matasa irinku da za su ba da gudummawa wajen cika wannan manufa mai kyau.
Dalilan da ya sa ya kamata ku shiga Jam’iyyar AAC:
1. Kawo Sauyi na Gaskiya: Jam'iyyar AAC ta kuduri aniyar kawo sauyi wanda zai cire talakawa daga kangin wahala ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa.
2. Muhimmancin Hadin Kai: Hadin kan matasa yana da muhimmanci wajen tabbatar da samun shugabanni nagari da kuma tabbatar da cewa muradun al'umma sun zama babban abin da ake yi.
3. Shugabanci na Gaskiya da Adalci: AAC tana nan daram akan tsari mai gaskiya da shugabanci na alheri wanda ba ya karkata ga son zuciya.
Me Za Ku Yi?
Ku shiga cikin wannan tafiya mai albarka ta hanyar zama membobi na jam'iyyar AAC.
Ku yi amfani da ilimi da hikimar ku wajen wayar da kan al'umma akan muhimmancin kawo sauyi mai dorewa.
Ku tabbatar da cewa matasa sun hada kai domin tsaida shugabanni nagari da za su kawo mana cigaba.
A Karshe,
Muna rokon Allah ya ba mu damar hada kai domin ceto al'umma daga wahalhalun da suke ciki. Wannan dama ce ta musamman gare ku, matasa, domin ku zama jagororin sauyi da al’umma za su yi alfahari da su. Ku tuna cewa lokaci yana tafiya, kuma wannan lokaci ya zo domin mu tashi tsaye mu canza halin da muke ciki.
Nagode da kulawarku, kuma muna jiran ku cikin tafiyar AAC.
Da girmamawa,
daga.
Shugaban Jam’iyyar AAC,
Jihar Zamfara
21/01/2025
SAKON GAISUWA DA JINJINA GA JAMI'AN TSARON SOJA DA CPG NA JAHAR ZAMFARA
Da farko muna mika godiya da jinjina ta musamman ga jami’an tsaro na jihar Zamfara bisa nasarar da s**a samu a yankin Shinkafi wajen kawo karshen matsalolin tsaro da s**a addabi yankin. Ayyukanku na nuna kwarewa, jajircewa, da kishin kasa, wanda ya zama abin alfahari ga dukkan ‘yan kasa. Allah ya kara basira da daukaka a aikinku.
Hakazalika, muna mika godiya ga Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal Dare, da Karamin Minista, Dr. Bello Matawalle, bisa jajircewarsu da kwazon da s**a nuna wajen tabbatar da tsaro a jihar. Kokarinsu ya zama haske ga al’ummar jihar, wanda ke tabbatar da cewa idan aka hada kai, matsalolin tsaro za su zama tarihi.
Jam’iyyar African Action Congress (AAC) tana taya ku murna da wannan ci gaba, tare da nuna farin cikinmu da goyon bayan da kuka bayar wajen ganin an kawo karshen matsalar tsaro a jihar Zamfara. AAC na kuma kira ga daukacin al’umma, musamman mazauna karkara, da su hada kai da gwamnati da jami’an tsaro don tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar.
A karshe, muna kira ga masu ruwa da tsaki da su cire siyasa daga harkokin tsaro, domin matsalar tsaron jihar Zamfara ta zama abu da ke bukatar hadin kan kowa da kowa ba tare da nuna bambanci ba. Yakamata a mayar da hankali kan tsare rayuka da dukiyoyin al’umma fiye da komai.
Allah ya ci gaba da kare jihar Zamfara da daukacin Najeriya.
Nagode.
Click here to claim your Sponsored Listing.