Dan umar

Dan umar

Share

15/05/2026

mwkake tunanai

07/05/2026

IDAN HAR KANA SON ZAMA WANI A WANNAN ZAMANIN, DOLE NE KA KOKA ZAMA MUGU A IDON WASU MUTANEN.

Mafi yawancin matasa suna asarar makomarsu ne don suna so kowa ya yabe su ya ce su mutanen kirki ne. Gaskiya mai ɗaci ita ce: Ba zaka taɓa gina daular kanka ba har sai ka koyi dabarar yi wa mutane "A'A" a kan waɗannan abubuwan:

1.
Zama Mugu Wajen Ba da Bashi: Idan ka ce ba zaka bayar da bashin jarinka ga ƴan'uwa da abokan arziki ba, zasu ce kai mugu ne, ka canza tun da ka sami 'yan canji. Rungumi wannan zagin, Idan ka bayar s**a cinye jarinka har ka karye, su ɗin ne zasu ce maka "Baka iya lissafi ba".

2.
Zama Mugu Wajen Zaman Majalisa: Idan ka daina zama a majalisar tsegumi don ka fuskanci neman halas ɗinka a ɓoye, zasu ce kayi girman kai. Jure wannan kaɗaicin, Majalisar da bata sa ka lissafin yadda zaka gina duniyarka da lahirarka ba, guba ce ga rayuwarka.

Mutumin kirki a wurin mutanen da basu da lissafin gobe, shi ne wanda zai wargaza rayuwarsa don ya faranta musu rai a yau. Rufe idonka ka fuskanci sana'arka da ibadarka.

UMAR ALIYU DAHIRU ✍️

07/05/2026

Guguwar “Pantamiyya” ta taso yanzu ne zaku gane tasirin gwagwarmayar masu ilimi a siyasa.
Pantami

06/05/2026

Ku Adana Katinku Domin Zabar Sheik Pantami A Ranar Zaben Fidda Gwani, Sakon Abba Sani Pantami Ga Gombawa

Mun samu labarin wasu bata gari sun fara bi lungu da sako na jihar Gombe suna karbar katin mutane na jam'iyyar APC da sunan maigidanmu Professor Isa Ali Pantami, alhali karya ne, maha'inta ne da suke son cutar al'umma.

Muna kira ga dukkannin al'ummar jihar Gombe birni da karkara da kada su yadda su bawa wani katin jam'iyyarsu, su adana katinsu har zuwa ranar zaben Primaries su fito su zabi Professor Isa Ali Pantami domin cigaban al'ummar jihar Gombe.

Duk wanda yaga wannan sanarwar don Allah ya sanarwa da 'yan uwa da iyaye da suke gida da sauran abokanan arziki.

06/05/2026

Sakone gareku
Abokai

06/05/2026

A tsakiyar kasuwa mai cike da hayaniya, kowa na neman abin duniya…
amma ni na tsaya ne da wani buri daban.
Na ajiye ayaba a gabana, amma ba ita nake sayarwa ba.
Ina tsaye ne ina karanta Al-Qur’ani, ina gayyatar mutane zuwa ga gaskiya.
Wasu sun wuce…
Wasu sun tsaya suna kallo…
Wasu kuma sun saurara… ❤️
A gefena akwai karamin keke 🚲 — alamar tafiyata a rayuwa.
Ba tafiyar arziki kadai ba… amma tafiyar neman ilimi da yada alheri.
👉 Ba dole sai kana babban matsayi ba kafin ka zama mai tasiri.
👉 Duk inda kake, zaka iya zama haske ga wani.
Yau kai me kake “talla”? Duniya ko Lahira? 🤔
📌 Hashtags:

✍️Dan umar

26/04/2026

Five fashion designe

03/04/2026

Teloring design

27/02/2026

Comebacks

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Gombe