Gombawa
Dan takarar dan majalisa a jihar Gombe Hon Mubarak Musa Dantori, tare da dubunnan magoya bayansa, sun fice daga jam'iyyar ADC zuwa jam'iyyar PDP domin marawa Professor Isa Ali Pantami baya a zaben 2027.
A yau Jumma'a daya daga cikin shahararrun matasa 'yan siyasa masu taimakon al'umma a jihar Gombe Hon Mubarak Musa Dantori kuma dan takarar dan majalisar jiha na Gombe ta kudu karkashin jam’iyyar ADC ya sanar da ficewarshi tare da dubunnan magoya bayansa daga jam'iyyar ADC zuwa jam'iyyar PDP.
Hon Mubarak Musa Dantori yace sun fice daga jam'iyyar ADC ne zuwa jam'iyyar PDP domin marawa tafiyar Pantamiyya baya karkashin jagorancin Professor Isa Ali Pantami domin samar da ingantaccen shugabanci a jihar Gombe.
Hon. Dantori ya bayyana cewa ayyukan Alkhairan da Professor Isa Ali Pantami ya shimfida a jihar Gombe da samawa daruruwan matasa ayyukan yi a jihar Gombe yana daga cikin abubuwan da s**a ja hankalinshi na shiga tafiyar Pantamiyya domin shima ya bada tashi gudummawa na ciyar da al'ummar jihar Gombe gaba.
05/06/2026
Hukumar Tsare-tsare da Ci Gaban Birane ta Jihar Gombe (GOSUPDA) ta bai wa daidaikun mutane, ƙungiyoyi da jam’iyyun siyasa da s**a kafa allunan talla, fosta da tutoci a manyan tituna da wuraren jama’a a cikin Babban Birnin Gombe wa’adin cire su kafin ko zuwa ranar 15 ga watan Yunin 2026.
Shugaban Gudanarwa na GOSUPDA, Alhaji Bappayo Samanja Maudo, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya ce hukumar ta lura da yadda ake ci gaba da sanya allunan talla da fosta ba tare da bin ƙa’idojin da s**a dace ba a sassa daban-daban na birnin Gombe.
Ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka sun saɓa wa dokokin tsare-tsaren birane na jihar, tare da kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na tabbatar da tsafta, tsari da kyawun muhalli a faɗin babban birnin jihar.
Alhaji Bappayo ya jaddada cewa hukumar ba za ta ci gaba da lamuntar duk wani aiki da ya saɓa wa dokokin ci gaban birane ba, yana mai gargadin cewa za a ɗauki matakin doka kan duk wanda ya ƙi bin wannan umarni bayan wa’adin da aka sanya.
Haka kuma, ya gargadi masu motocin haya da na kashin kansu da masu babura da su guji wanke ababen hawansu a kan tituna da sauran wuraren jama’a, yana mai cewa hakan na lalata hanyoyi, toshe magudanan ruwa da kuma ƙara gurbata muhalli.
Shugaban na GOSUPDA ya kuma yi kira ga masu gini, masu yin bulo da ’yan kwangila da su daina haɗa siminti, yashi da sauran kayan gini a kan hanyoyi da wuraren da jama’a ke bi, yana mai cewa hakan na haddasa lalacewar tituna tare da jefa masu amfani da hanya cikin wahala.
Ya ƙara da cewa dole ne dukkan ayyukan gine-gine su kasance cikin tsarin da aka amince da shi tare da bin ƙa’idojin muhalli domin tabbatar da tsaro da kuma ci gaban birane cikin tsari.
A ƙarshe, Alhaji Bappayo Samanja Maudo ya yi kira ga mazauna jihar Gombe da su mara wa hukumar baya wajen tabbatar da tsafta da kyawun birnin, yana mai cewa ci gaban birane nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa.
Majiyar Rahoto: Hukumar Tsare-tsare da Ci Gaban Birane ta Jihar Gombe (GOSUPDA).
05/06/2026
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa duk wani zaɓen fidda gwani da jam’iyyun siyasa s**a gudanar bayan wa’adin ranar 30 ga watan Mayu, 2026, ba zai kasance cikin tsarin jadawalin da hukumar ta amince da shi ba.
Hakan na zuwa ne bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke wasu sassa na jadawalin zaɓukan fidda gwani da INEC ta fitar domin shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027, inda kotun ta ce hukumar ba ta da ikon takaita wa’adin da Dokar Zaɓe ta tanada ga jam’iyyun siyasa.
03/06/2026
Yadda Ruwa da Iska S**a Lalata Gidaje a Wuro Dole, Karamar Hukumar Akko ta Jihar Gombe
Mazauna garin Wuro Dole da ke Ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe sun shiga cikin damuwa bayan wata guguwa mai ƙarfi tare da ruwan sama ta yi barna mai yawa a yankin.
Lamarin ya faru ne lokacin da iska mai ƙarfi da ruwan sama s**a mamaye garin, lamarin da ya janyo rushewar wasu gidaje tare da lalata rufufin wasu da dama. Haka kuma, an samu asarar dukiyoyi da kayayyakin amfanin gida sakamakon wannan ibtila'i.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa barnar ta shafi iyalai da dama, inda wasu s**a rasa matsugunansu tare da shiga halin ƙunci. Sun yi kira ga gwamnati da ƙungiyoyin agaji da masu hannu da shuni da su kawo musu ɗauki domin rage radadin halin da suke ciki.
Al'ummar yankin na ci gaba da ƙididdige asarar da aka yi, tare da fatan samun taimakon gaggawa daga hukumomin da abin ya shafa.
Allah Ya kiyaye gaba, Ya kuma bai wa waɗanda abin ya shafa ikon jure wannan jarabawa. Ameen.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Gombe
741212