Ibrahimfky

Ibrahimfky

Share

09/04/2026

MU’AMALA TSAKANIN LIBRA (MIZAN7) DA LIBRA (MIZAM7)
(ba aure kaɗai ba, har abota, kasuwanci da dukkan hulɗar rayuwa)
ASALI DA HALITTA
LIBRA
Burujin iska ne.
Mai son daidaito, adalci, ladabi da kyakkyawar mu’amala.
Yana son zaman lafiya, tattaunawa da yarjejeniya.
Ba ya son rikici ko tsaurin magana.
Yana yawan tunani kafin yanke hukunci.
Idan Libra ya haɗu da Libra
Kamar madubi ne da ya kalli kansa.
Halaye iri ɗaya, buri iri ɗaya, da rauni iri ɗaya.
YANAYIN MU’AMALA
SOYAYYA
Akwai soyayya mai laushi da kyau.
Dukansu suna son kulawa, ladabi da farin ciki.
Rayuwa na iya zama mai daɗi, cike da nishaɗi da kyakkyawar mu’amala.
Matsala
Dukansu ba sa son rikici.
Saboda haka suna iya ɓoye matsala maimakon su magance ta.
Dukansu suna jinkirin yanke hukunci.
Wannan na iya jawo tsaiko a rayuwa.
IDAN SUKAI AURE
Aure mai kyau a zahiri.
Gida mai tsafta, salo da zaman lafiya.
Amma a ciki
Idan babu wanda zai ɗauki nauyin yanke hukunci, rayuwa za ta tsaya.
Idan an ɓoye matsala, za ta girma a hankali.
Sirrin nasara
Gaskiya a fili
Yanke hukunci ba tare da tsoro ba
Karɓar cewa rikici wani lokaci dole ne
A ABOTA
Abota mai ƙarfi sosai.
Suna fahimtar juna cikin sauƙi.
Suna iya zama abokai na gaskiya na dogon lokaci.
A KASUWANCI DA AIKI
Haɗin na da kyau a hulɗar jama’a, shari’a, kasuwanci da ciniki.
Dukansu suna iya yin yarjejeniya da mutane.
Amma matsala
Rashin wanda zai yanke hukunci cikin gaggawa
Ko tsoron ɗaukar haɗari
DARASI NA RAYUWA
Kowa yana koyon yanke hukunci da tsayawa a kai.
Kuma koyon fuskantar matsala maimakon guje mata.

GASKIYA A HIKIMA
Wannan haɗin mai kyau ne amma mai rauni a cikin yanke hukunci.
Yana da zaman lafiya, amma yana buƙatar ƙarfin zuciya.
Idan an gyara wannan, zai zama haɗin mai daɗi sosai.

AƘARSHE
Taurari alamu ne kawai na halaye da yanayi.
Ba su da ikon tilasta soyayya ko rabuwa.
Allah Shi kaɗai ne Mai iko da zukata da kaddara.
Abin da Ya so ne kaɗai yake tabbata.
Wallahu ta’ala a’alam.

Ibrahim fky al falaky ✍️ 07033105536

08/04/2026

MU’AMALA TSAKANIN SAGITTARIUS (QAUSU9) DA PISCES (HUTU12)

(ba aure kaɗai ba, har abota, kasuwanci da dukkan hulɗar rayuwa)

ASALI DA HALITTA
SAGITTARIUS
Burujin wuta ne.
Mai son gaskiya, ‘yanci, tafiya, ilimi da faɗin ra’ayi a fili.
Yana da kuzari, hangen nesa da son gano sabbin abubuwa.
Yana son rayuwa mai faɗi ba tare da takura ba.

PISCES
Burujin ruwa ne.
Mai tausayi, ruhaniya, jin ƙai, mafarki da zurfin zuciya.
Yana rayuwa da ji da tunanin ciki.
Yana da sauƙin shafar yanayi da mutane.

WUTA DA RUWA
Wuta tana iya dumama ruwa.
Ruwa kuma yana iya kashe wuta.
Haɗin na iya zama mai daɗi ko mai rikitarwa gwargwadon yadda aka tafiyar da shi.

YANAYIN MU’AMALA
SOYAYYA
Akwai jan hankali na ruhaniya da zuciya.
Pisces yana jan Sagittarius da tausayi da zurfin ji.
Sagittarius yana jan Pisces da kuzari da gaskiya.
Matsala
Sagittarius yana magana kai tsaye ba tare da la’akari da ji ba.
Pisces yana saurin jin rauni.
Sagittarius yana son ‘yanci.
Pisces yana son kusanci da kulawa.
Wannan na iya haifar da soyayya mai taushi amma mai sauƙin karyewa.

IDAN SUKAI AURE
Aure mai buƙatar haƙuri sosai.
Sagittarius yana son tafiya da ‘yanci.
Pisces yana son zama kusa da kulawa.
Idan Sagittarius ya yi nisa da yawa, Pisces zai ji an bar shi.
Idan Pisces ya jingina sosai, Sagittarius zai ji an takura shi.
Zaman aure zai yiwu ne idan
Sagittarius ya ƙara tausayi da taushi.
Pisces ya ƙara ƙarfi da tsayawa kan kansa.

A ABOTA
Abota na iya zama mai kyau.
Sagittarius yana kawo nishaɗi da kuzari.
Pisces yana kawo tausayi da fahimta.
Amma rashin daidaiton halaye na iya rage kusanci.

A KASUWANCI DA AIKI
Haɗin ba shi da ƙarfi sosai.
Sagittarius yana aiki da hangen nesa da sauri.
Pisces yana aiki da ji da yanayi.
Idan babu tsari, aiki zai lalace.
DARASI NA RAYUWA
Sagittarius yana koyon tausayi da la’akari da ji.
Pisces yana koyon tsayawa da ƙarfi da kare kansa.
GASKIYA A HIKIMA
Wannan haɗin matsakaici ne.
Ba sharri tsantsa ba, amma ba mai sauƙi ba.
Yana buƙatar fahimta da haƙuri mai yawa.
A ƘARSHE
Taurari alamu ne kawai na halaye da yanayi.
Ba su da ikon tilasta soyayya, aure ko rabuwa.
Allah Shi kaɗai ne Mai iko da zukata da kaddara.
Abin da Ya so ne kaɗai yake tabbata.
Wallahu ta’ala a’alam.
ibrahim fky al falaky ✍️ 07033105536

29/01/2026

IRAN

bari mu taba nazari a bayyane cikin wannan al'amarin amma a mahangar Ilimin taurari Astrology.

Bisa ga tafiyar taurari adaidan lokacin ta tambayar tazo min arai sannan na sata a hai'ar (chat).

Iran ce Acsedent a wannar hai'a
burujin mizan shike wakiltar Iran tauraron venus ce rula.
dabi'ar burujin mizan wato Iran shine
son daidaito, neman adalci, yanci, sulhu, son haɗin kan raunana, kin zalunci, faɗa dashi, juriya, wannan sune dabi'un mizan Iran kenan.

America itace burujin himlu murikh shine rula
ɗabi'ar burujin himlu son jagoranci kota halin ƙaka, son fifiko, nuna isa, izza, jiji dakai, neman cikici, tada hankali, gaggawa, faɗa, kasada, sonkai, fin ƙarfi.

Iran venus tana gidan dalwu gidan 5 da Degrees 13 venu tana huznu a gidan aquarius tana fuskantar damuwa da ƙunci wannan ke bayyana halin da Iran ce ciki yanzu na matsin lamba daga waje takunkumai.

sannan dakarun soji na Iran sune burujin hutu jupiter gasu a surɗan 10 house Gidan government suna riju'i amma gidan sharafinsu ne wannan ke nuna cewa suna da matukar ƙarfi amma asirrance tareda sadaukarwa da ƙaƙƙarfan haɗin kai da government na qasar amma suna fuskantar kalubale da jinkirin tafiyar al'amura.

Iran government itane burujin surdan tausayi, jinƙai, taimakon na kasa, tsaron gida, kishin ƙasa, sirri,
ƙamar shine wakilin ta kuma gashi a jauza'a da 0 Degree kuma ƙamar yana farhi a jauza'a sannan yayi tislisi mai shiga da venus wannan yana nuna ƙarfin government a fili sosai sosai .

Sannan cikin ƙasar Iran ne burujin jadyu
tsari, bin doka da Oder, tattali, shiri don gaba, dabara, jinkiri mai ƙunci, nasara bayan juriya da gwaji.
wannan sune dabi'un capricorn cikin ƙasar Iran kenan. zuhal shine rula na jadyu gashi can a burujin hutu dindan dakaru da sojojin kasar, wannan ke nuna kusan kowani mutum a ƙasar jinsa yake tamkar soja zai iya bada kaomai nasa wajen ganin cewa kasar takai ga nasara koda bayan ransa 💪 kuma yana kusan irin juriya da jarumtar su da dakewa,
amma zaman Neptune a gurin shine damuwa ta ruɗani da daga kayar baya daga wassu munafukai, misalin zanga-zanga da America tai amfani da bata gari kenan amma babu nasara.

America Mars tana gidan dalwu suna buruji daya da venus Iran amma babu alamar haduwa da iran domin America Mars tanada Degrees 3 venus Iran tana 13 Degrees kuma venus tafi sauri fiye da mars America
wannan ke nuna Iran bata burin yin yaki amma
tana da cikakken ƙarfin kare kanta fiye da kima💪. sannan America tazo Gidan 11 domin neman temakon daga abokan hulɗarta
wato amma mars tana fuskantar ƙaskanci da walakanci a gidan dalwu kuma wai taimako tazo nema😂 amma ta biyo Iran ne har gidan 5 na Iran ɗin kuma zuhal shine rula muna fuaka kenan tana Neman taimakon zuhal ne amma baizai ba shima ta kansa yake.

government na Amurka jadyu zuhal a 12
government tana cikin rudani da kulewar kai amma.
soldiers na America Virgo Mercury a daluwu
suna da karfi a gurin amma musallasi suke ba yabo ba fallasa domin ba muhallin su bane amma basa da muradin son a gwabza kawai bin umurni ne.

cikin ƙasar America surɗan moon a gemini
al ummar ƙasa basa goyon bayan wannan yaki domin babu aspeat na buƙatuwa da hakan agurin ƙamar zuwa mars.

a taƙaice dai a Wannan yanayi ba lallai ne a gwabza wannan ƙazamin yaki tsakanin musulumci da kafirci ba.
yaƙin zaifi karkata ga yaƙin cacar baka
idan ma za'a gwabza ɗin to abin bazai tsauri ba kuma muminai sune zasui rinjaye da nasara da ƙarfin Allah
wallahu ta'ala a'alam.

A ƙarshe muna fatan Allah ya kasance tare da jamhuriyar Musulunci ta Iran
ya rushe America da magoya bayan ta na zahiri da na ɓoye albarkacin manzon Allah (saww) da iyalan gidansa (as)
🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲
ibrahim fky al-falaky ✍️ 07033105536

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Gombe

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00